Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a hukunta waɗanda suka yi wa matan ƙauye fyaɗe bayan shekara 30
- Marubuci, Geeta Pandey da Pramila Krishnan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Delhi da Chennai
Babbar kotun jihar Tamil Nadu da ke Indiya ta tabbatar da hukuncin da aka yanke shekara 30 da suka wuce, inda aka samu ɗaruruwan jami’an gwamnati da laifin aikata miyagun laifuka, ciki har da yin fyaɗe ga wasu mata 18.
Jami’an gwamnatin da aka samu da laifin sun haɗa da ƴan sanda da masu aiki a ɓangaren kula da gandun daji da kuma na tattara haraji.
Jamai’an sun far wa wasu ƴan ƙauye a watan Yunin 1992, bisa zargin su da taimaka wa wani mai fasa-ƙwaurin itacen turare, mai suna Veerappan.
Jami’an sun ci zarafin maza sannan suka yi wa mata fyaɗe, sun farfasa musu gidaje da halaka dabbobi da suka mallaka.
An yi wa al’amarin laƙabi da ‘Shari’ar Vachathi’, wato sunan ƙauyen da aikata waɗannan laifuka.
Dukkanin jami’ai 269 da aka zarga sun musanta aikata laifukan, sai dai a shekara 2011 wata kotu ta kama su da laifi a ƙarƙashin wata doka.
An kuma samu mutum 17 daga cikin su da laifin aikata fyaɗe.
Yayin da 54 daga cikin waɗanda ake zargin suka mutu a tsawon lokacin da ake shari’ar, an yanke wa sauran 215 hukuncin ɗauri da suka kama daga shekara ɗaya zuwa 10.
Sai dai mutanen sun ɗauka ƙara a babbar kotun Madras da ke birnin Chennai a arewacin ƙasar.
Lauyar waɗanda aka ci zarafin ta shaida wa BBC cewa an bayar da belin dukkanin waɗanda aka samu da laifin.
Ta ce “Baya ga mutum 17 da aka kama da laifin fyaɗe, kusan dukkanin sauran ba su yi zaman kurkuku ba ko kaɗan.”
A ranar Juma’a mai shari’a P Velmurugan ya umarci gwamnatin jihar ta biya kowace daga cikin waɗanda aka ci zarafi diyyar kuɗin rupee miliyan ɗaya, wato dalar Amurka 12,034 da kuma aikin yi.
Hukuncin kotun ya kuma yi kira da a ɗauki mataƙi mai tsauri a kan shugaban ma’aikatan yankin na wancan lokacin, da babban malamin daji da kuma shugaban ƴan sandan yankin.
A watan Maris, mai shari’a Velmurugan ya kai ziyara a ƙauyen na Vachathi, wanda ke kusa da tuddan Sitheri a gundumar Dharmapuri.
Me ya faru a ƙauyen Vachathi?
A shekarun 1990, jami’an tsaro sun mamaye dazuka da ƙauyukan yankin suna neman wani da ake kira Veerappan, wanda shi ne ɗan bindigar da ya fi kowane rashin imani a Inidiya a wancan lokacin, wanda ake zargi da kashe mutane sama da 100.
Haka nan an zarge shi garkuwa da mutane, da fasa-ƙwauri da kuma kisan namun daji babu izini.
(Ƴan sanda sun samu nasarar kashe shi a shekarar 2004)
Jami’an tsaro sun riƙa kai samame a ƙauyen Vachathi, suna zargin mazauna ƙauyen da taimaka wa ɗan fasa-ƙwaurin, da kuma cewar suna da hannu a fasa-ƙwaurin itacen turare.
Da safiyar ranar 20 ga watan Yunin 1992 an fafata tsakanin mazauna ƙauyen da jami’an kula da gandun daji a lokacin irin wannan samame.
Lamarin ya sanya an raunata wani malamin daji.
Takardun bayanan kotu sun nuna cewa bayan sa’o’i kaɗan tawagar malaman daji 155 da jami’an ƴan sanda 108 da kuma jami’an tattara haraji shida sun dirar wa ƙauyen.
A lokacin da suka isa, sun iske yawanci mata da ƙananan yara da kuma tsofaffi a cikin gidaje, kasancewa akasarin maza majiya ƙarfi sun tsere domin ɓuya a tsaunukan da ke kusa da ƙauyen, wurin da suka ci gaba da ɓuya har tsawon watanni.
Jami’an da suka kai samamen sun aikata ta’asa, suka riƙa dukan maza da mata babu tausayi, sun farfasa gidaje, suka halaka dabbobi kuma suka kwashe tsawon lokaci suna yi wa mata 18 fyaɗe.
Sama da mata 100 da yara ne aka kama aka ɗaure, wasu aka kai su gidan yari na tsawon watanni bisa zarge-zarge na bogi.
Bayan shekara 20, babbar kotu ta yi watsi da ƙararrakin inda ta ce “an shigar da su ne da mummunar manufa”.
Wata jaridar ƙasar Indiya mai suna ‘The Hindu’ ta bayyana harin da aka kai a ƙauyen a matsayin misalin “irin abin da mugayen jami’an tsaro da jami’an gwamnati marasa imani za su iya aikatawa a kan talaka da marasa ƙarfi”
Fyaɗe mai muni
Wata ƙatuwar bishiya da a ke tsakiyar ƙauyen ita ce shida a kan cin zarafin da aka aikata.
A kwanakin nan lokacin wata tattaunawa da BBC, Mazauna ƙauyen sun ce an tursasa maza da mata da yara su taru a ƙarƙashin bishiyar, inda aka riƙa yi musu dukan kawo wuƙa.
Daga nan kuma aka ware wasu mata da ƴan mata 18 aka kai su bakin wani tafki da ke kusa, inda aka riƙa yi musu fyaɗe.
Wata daga cikin waɗanda aka yi wa fyaɗe, wadda a wancan lokacin take da shekara 13, ta ce ta riƙa roƙon jami’an na gwamnati kan su ji tausayin ta su sake kasancewar ita yarinya ce ƴar makaranta, to amma sun yi kunnen uwar-shegu da roƙon nata.
Ta ce “sun yi mana fyaɗe, sun doke mu, haka za ka ji mutane na kururuwa a kowane ɓangare na ƙauyen.”
Ta ƙara da cewa “bayan sun gama yi mana fyaɗe, an ɗauke mu zuwa ofishin ƴan sanda, inda suka jiye mu, suka hana mu barci a tsawon daren.
An kulle mu a bayan kanta, ni da ƴar’uwata da kawunmu da mamata da kuma innarmu.”
Sa’ilin da suka koma gida bayan kwashe makwanni a ɗaure, sun iske wawwatsar musu da hatsinsu, an fasa rumbunansu, an ƙona musu kayan sawansu, yayin da suka ga ƙasusuwan dabbobi a cikin rijiyoyi.
Yadda aka bi musu hakki
Mazauna ƙauyen sun daɗe suna faɗi-tashin ganin an yi musu adalci, kuma sun riƙa cin karo da matsaloli da turjiya a yunƙurin nasu na bin haƙƙinsu.
A farko hukumomi sun musanta aikata ba daidai ba.
Ƴan sanda sun ƙi kai koke a madadinsu kuma kotuna sun ƙi sauraron su, inda suke cewa babu yadda za a yi ƴan sanda da jami’an gwamnati su yi musu fyaɗe.
Sai dai bayan hanƙoro da ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyar ‘Communist Party of India suka riƙa yi, an miƙa batun ga Cibiyar binciken manyan laifuka ta ƙasar Indiya (CBI).
A rahoton da ta bayar bayan yin bincike, CBI ta ce ƴan sanda da jami’an gwamnati sun dirar wa ƙauyen, suka murƙushe maza da mata da yara da rushe bukkokin al’umma.
An iya ƙwatar wa al’ummar Vachathi hakkinsu ne kawai saboda nacewar da matan da aka yi wa fyaɗe suka yi da kuma goyon bayan da suka samu daga masu hanƙoro.