Canada da Hong Kong sun bi sahun London wajen bankwana da Sarauniya

Yayin da dubban al’umma ke ci gaba da shafe tsawon dare a layi domin kaiwa ga inda aka ajiye akawatin da ke dauke da gawar Sarauniya Elizabeth don bankwana da ita a dakin taro na Majalisar Dokokin Birtaniya wato West Minister Hall,
can a wasu kasashen ma ana gudanar da matakai ne na gudanar da taruka na musamman domin martaba Sarauniyar wadda ta cika kwana na bakwai da rasuwa.
Can a Canada a yau 'yan majalisar dokokin kasar za su koma kafin ainahin ranar da aka shirya komawar zaman majalisar a Ottawa domin zama na musamman na tunawa tare da bankwana da Sarauniyar.
A Hong Kong ma jama’a na bin layi tsawon sa’o’i domin bankwana da Elizabeth ta biyu a wani taro da ake gani kusan mafi girma a wajen Birtaniya na girmama ta.
Yayin da a birnin London dubban jama’a ke kan layin da suka sahfe dare domin yin bankwana da Sarauniyar, inda hukumomi suka dauki matakan tsaro ba kan rufin gine-gine ba ba ramukan karkashin tituna ba duk domin tabbatar da tsaro a wannan taro.
Taron da ke zaman daya daga cikin mafiya girma da tarihi a Birtaniya domin bankwana da Sarauniyarm kazalika Canada da alummar Homg Kong suma suna cikin yanayi na kama da abin da ke gudana a birnin London.
'Yan majalisar dokokin na Canada na komawa domin zaman na musamman na tunawa da martaba Sarauniyar wadda ita ma a lokacin rayuwarta ta dauki kasar ta nahiyar Amurka ta Arewa.
Sarauniya Elizabeth ta ziyarci Canada fiye da duk wata kasa ta kungiyar kasashe renon Ingila, inda ta kai ziyara sau 22 a lokacin rayuwarta.
Kamar yadda za a yi jana’izar sarauniyar a ranar Litinin, kasar ta Canada ita ma tana cikin makoki na kwana goma, inda za a kammala makokin da biki na kasa ranar Litinin din a can.
Sarauniya Elizabeth ta kasance shugabar kasar ta Canada kusan tsawon rabin kasancewarta.
Tsoffin firaministoci da shugabannin kasar na da da na yanzu na cikin alhinin rashinta tare da tunawa da ita, a matsayin sarauniyar da ta kaunaci kasar tasu sosai.
‘Yan majalisar dokokin kasar sun katse hutun da suke yi domin su koma su martaba da yin bankwana da ita a wannan lokaci a Ottawa.
Marigayiya sarauniyar ta kasance babbar kwamandar sojojin kasar da kuma shugaba ta nadi ga ‘yan sandan kan doki na kasar ta Canada.
Wakilan dukkanin wadannan rundunoni biyu za su kasance a London a yayin gudanar da jana’izarta.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, PA Media
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp