Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wa ya kamata a yi wa allurar riga-kafin cutar kansar bakin mahaifa?
Bincike ya nuna cewa allurar riga-kafin HPV za ta iya rage yawan masu kamuwa da cutar daji ta bakin mahaifa da kusan kashi 90 cikin ɗari.
Cutar daji ta bakin mahaifa ita ce ta huɗu a cikin cutukan daji da mata suka fi kamuwa da su a duniya, inda take hallaka sama da mata 300,000 a duk shekara.
Ta yaya allurar riga-kafin HPV za ta iya hana kamuwa da cutar daji?
Allurar riga-kafin HPV tana hana kamauwa da nau'in cutukan HPV har guda tara.
Sun haɗa da cutuka biyu waɗanda kusan suke haddasa dukkanin cutukan kansar bakin mahaifa, da waɗanda suke janyo kansar dubura da wasu cutukan daji na gaba da kai da kuma kansar wuya.
Bincike ya nuna cewa allurar riga-kafin za ta iya kare kamuwa da cutukan HPV tsawon aƙalla shekara 10, kodayake ƙwararru ma na ganin zai iya wuce hakan.
Nazari ya nuna cewa allurar na rage yawan masu kamuwa da kansar mahaifa da kusan kashi 90 cikin ɗari.
Wa za a iya yi wa riga-kafin na HPV?
Allurar riga-kafin ta HPV ta fi aiki sosai idan aka yi wa 'yan mata da maza matasa kafin su kamu da kwayoyin cutar ta HPV.
Dalilin hakan kuwa shi ne allurar riga-kafin za ta iya kare kamuwa da ƙwayar cuta ne amma ba za ta iya raba jikin mutum da ƙwayar cutar ba idan har ya kamu.
Ƙwayoyin cutar suna da yawa saboda haka dole ne a yi wa yara ƙanana riga-kafin tun kafin su balaga.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce za a iya yin riga-kafin sau daya ko biyu. Hukumar ta ce mutanen da garkuwar jikinsu ta ragu za su iya karɓar riga-kafin sau biyu ko sau uku.
Mece ce HPV?
HPV (short for human papillomavirus) suna ne na wasu ƙwayoyin cuta na bairus (virus) da ke da yawa kusan a ko'ina.
Akwai nau'in ƙwayoyin cuta na bairus na HPV, sama da 100 kuma yawanci ba a ganin wata alama ta kamuwa da cutar, kodayake wasu na iya sanya wa mutum ɗan kumburi a fata. Za a iya ganin wannan a hannu ko ƙafa ko gaba ko kuma a cikin bakin mutum.
Yawancin mutane ba sa ma sanin sun kamu kuma jikinsu na yaƙar cutar ba tare da yin wani magani ba.
Idan cutar ta yi tsanani takan iya haddasa babban kunburi da ka iya zama cutar daji.
Wa yake kamuwa da HPV kuma ta jima'i ake kamuwa?
Abu ne mai sauƙi kamuwa da ita kasancewar ƙwayoyin cuta ne da ke saurin yaɗuwa kuma ana yaɗa su ta hanyar haɗuwar fata ko jiki.
Kusan kashi 80 cikin ɗari na mutane na cikin haɗarin kamuwa da HPV zuwa shekara ta 25.
Yawanci mutane na kamuwa cikin wata 18 zuwa shekara biyu.
Galibi cuta ce da ake kamuwa da ita ta hanyar jima'i amma kuma ba a kamuwa da ita ta hanyar maniyyi, kamar yadda ake kamuwa da cutar sanyi (gonorrhoea).
To amma kuma yawanci ana kamuwa da ita sakamakon tattaɓa jiki a lokacin soyayya ko jima'i.
Yaya girman aikin riga-kafin na HPV yake a faɗin duniya?
Kusan kashi 90 cikin ɗari na mutuwa sakamakon cutar kansar bakin mahaifa na faruwa ne a ƙasashe matalauta da kuma masu matsakaicin samu kamar yadda hukumar lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar.
A waɗannan ƙasashe yawanci ba a gano cutar kansar bakin mahaifa ba har sai ta yi tsanani ta fito da alamu.
A baya hukumar lafiya ta ce ta ƙuduri aniyar kawar da cutar zuwa ƙarni na gaba ta hanyar cimma kashi 90 cikin ɗari na riga-kafin na HPV zuwa shekara ta 2030.
Ƙasashe 140 a yanzu sun ɓullo da allurar riga-kafin, in ji WHO.
Yawanci mata sun fi kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa a ƙasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara, inda ake da kashi 24 cikin ɗari, sai mai bin baya, Latin Amurka sai kuma yankin Karebiyan wanda yake da kashi 16 cikin ɗari.
Daga nan sai kuma Gabashin Turai mai kashi 14 cikin ɗari, sai yankin kudu maso gabashin Asiya mai kashi 14 cikin ɗari in ji WHO.
Rashin cikakken aikin bincike ko duba alamun cutar a jikin mutane da ƙarancin hanyoyin samun magani da kuma jinkirin yin riga-kafin, dukkaninsu suna haifar da matsalar.
Rwanda na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka ɓullo da yi wa mutane allurar riga-kafin.
A shekara ta 2011 ta ƙaddamar da wani shiri na yi wa yara mata riga-kafin tun da wuri ta kuma ɓullo da shirin yi wa mata gwajin alamun cutar ta sankarar bakin mahaifa.
A shekarar farko ta yi nasarar yi wa mata tara cikin 10 allurar, wannan ya sa ƙwararru suke ganin hakan abin koyi ne ga sauran ƙasashe.
Duk da cewa allurar riga-kafin na matuƙar rage haɗarin kamuwa da kansar bakin mahaifa, to amma ba wai tana hana kamuwa da dukkanin cutukan da ƙwayar cutar HPV ke yaɗawa ba.
Saboda haka abu ne mai kyau da muhimmanci mata su riƙa zuwa ana yi musu gwajin cutar ta kansar bakin mahaifa idan sun kai shekara 25 da haihuwa.