Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta sauya taken ƙasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar da ta dawo da amfani da tsohon taken ƙasar mai suna "Nigeria: We Hail Thee".
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a yau, wanda tuni aka yi amfani da shi lokacin da Tinubu ya yi wa taron majalisar na haɗin gwiwa jawabi a yau Laraba.
Shi ne karon farko da majalisar ta rera taken tun bayan daina amfani da shi shekara 46 da suka wuce.
Shugaba Tinubu ya ce taken na nuna bambancin al'adu, da kuma wakiltar kowane ɓangare tare da zimmar taka rawa wajen ƙulla 'yan'uwantaka.
Yayin bikin cikarsa shekara ɗaya a kan mulki da kuma murnar cika shekara 25 da komawa mulkin dimokuraɗiyya, shugaban ya taya 'yan ƙasa murna kuma ya nemi 'yan majalisa "su ci gaba da aiki tare don gina ƙasar da na gaba za su yi alfahari da ita".
Dokar Taken Ƙasa ta 2024, wadda za ta bai wa ƴan Najeriya damar komawa amfani da tsohon taken ƙasar.
A lokacin zaman da majalisar ta gudanar, wanda shugaban na Najeriya ya halarta, ƴan majalisar sun rera taken.
Dokar ta tanadi cewa ma’aikatar yaɗa labaru ta Najeriya za ta “tsara yadda za a riƙa rera taken na Najeriya, kuma za su naɗi sabon taken wanda za a riƙa kunnawa.
Za a wallafa sabon taken Najeriyar da aka naɗa a shafukan intanet na gwamnati kuma zai kasance cikin abubuwan da za a rika koyar da ɗalibai a makarantu.
A shekarar 1960 ne Najeriya ta amince da fara amfani da tsaken Najeriya lokacin da ta samu ƴancin kai, sai dai daga baya a n daina amfani da shi a shekarar 1978, lokacin mulkin shugaban mulkin soji Olusegun Obasanjo.
Taken Najeriya da za a riƙa rerawa
Nigeria, we hail thee,
Our own dear native land,
Though tribe and tongue may differ,
In brotherhood, we stand,
Nigerians all, and proud to serve
Our sovereign Motherland.
Our flag shall be a symbol
That truth and justice reign,
In peace or battle honour’d,
And this we count as gain,
To hand on to our children
A banner without stain.
O God of all creation,
Grant this our one request,
Help us to build a nation
Where no man is oppressed,
And so with peace and plenty
Nigeria may be blessed.