Mutum miliyan goma sun yi rijista da dandalin Threads kishiyar Twitter

Threads

Asalin hoton, OTHERS

Mutum miliyan goma ne suka yi rijista don amfani da sabuwar manhajar Thread a cikin sa'a bakwai da ƙaddamar da ita, in ji shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg.

Ya bayyana dandalin da cewa kishiya ce "da za ta yi zaman mutunci" da Twitter, wadda hamshaƙin mai arziƙin nan Elon Musk ya saya a watan Oktoba.

Ƙwararru sun ce dandalin Threads zai iya jan hankalin masu amfani da Twitter waɗanda ba sa farin ciki da sauye-sauyen da aka kawo wa manhajar a baya-bayan nan.

Threads na bai wa mai amfani da ita, damar wallafa haruffa sama da 500, kuma tana da siffofi irin na Tuwita.

Tun farko, Mista Zuckerberg ya ce gudanar da dandalin "mai sauƙin kai ga masu amfani... zai kasance muhimmin lamari wajen samun nasarar manhajar".

Sai dai Mista Elon Musk ya mayar da martanin cewa: "Tabbas ya fi sauƙi, wasu baƙin ido su far maka a Tuwita, da mutum ya ɓuge da ƙaryar samun farin ciki daga Instagram na ɓoye."

Katafaren kamfanin Meta wanda ya mallaki shafin Facebook da Instagram ne, ya ƙaddamar da manhajar sada zumunta da muhawarar, mai suna Threads, da galibi ake kallo a matsayin kishiya ga Twitter.

Ba ma ga ƙwararrun da ke kallon ƙaddamar da sabuwar manhajar ta Threads a matsayin kishiya ga Twitter mallakar Elon Musk ba, Mark Zuckerberg da kansa ya furta cewa Threads wanda ya ƙunshi abubuwa kusan irin na Twitter zai iya yi wa Tuwita fintinkau.

Duk da yake, zuwa yanzu ba a ƙaddamar da sabuwar manhajar sada zumunta da muhawarar a yankin Tarayyar Turai ba, amma Mista Zuckerberg ya ce a cikin sa’a hudu da kaddamar da shi har ya samu masu amfani da shi sama da miliyan biyar.

Ya ƙara da cewa zai ɗauki lokaci kafin sabon dandalin ya buwaya, amma dai mai yiwuwa ne Threads ya samu yawan mutane sama da miliyan dubu ɗaya.

A cewar Zuckerberg, Twitter ya samu wannan damar, sai dai bai yi amfani da ita ba. Amma ya ce su suna fatan za su yi.

Sai dai abokan gogayya sun yi suka a kan yawan bayanan masu amfani da ita da manhajar za ta riƙa tattarawa.

A ciki akwai batun lafiya da na kuɗi da kuma bayanan mai shiga shafin , in ji rumbun Apple Store.

A yanzu dai ana iya sauke wannan manhaja ta sabon shafin na sada zumunta da muhawara na Threads, a sama da kasashe 100, ciki har da Birtaniya, amma ban da kasashen Tarayyar Turai.

Kamfanin Meta da ya mallaki wannan sabuwar manhaja ya ce, a yanzu zubin farko ce, wanda hakan ke nufin akwai karin wasu abubuwa da ya shirya sanya wa manhajar domin kara jan hankalin jama’a

Kasancewar shafin nada alaka da Instagram wanda ke da tarin mabiya, wannan zai sa ya samu saukin daukar hankalin tarin miliyoyin mabiya da ke kan Instagram, wadanda tuni wasui ma har sun damfara da sauke shi.