Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Me ya sa kika azabtar da ni?': Wata ƴar aikin gida da take neman a yi mata adalci
“Ku agaza mun, wacce ta dauke ni aiki tana azabtar da ni.” Meriance Kabu ta rubuta.” Kullum sai an yi mun jina-jina a agaje ni!
Daganan sai ta kanannade takardar ta jeho ta, ta tsakanin karafunan kyauren da aka garkame gidan, wanda yake wajen Kuala Lampur inda take aiki a matsayin `yar aikin gida.
Wata mata da ta zo wucewa ta tsinci takardar a kasa. Tana karanta takardar ta maza ta kai wa wani jami`in `yan sanda mai murabus da shi ma yake zaune a wadannan gidaje. “In da ta ci gaba da zama a wajen, tabbas da ta mutu.,” ya bayyana daga bisani.
A wannan rana, 20 ga watan Disamba na shekarar 2014, `yan sandan Maleshiya suka je suka buga kyauren kofar inda Mariance take.
Wajen da ta kasa fita a watanni takwas. “Ji nake kamar ina faduwa” ta bayyana a lokacin da take tuna lokacin da ta ga jami`an.
“Suka ce, `Kada ki ji tsoro, ga mu mun kawo miki agaji`. A wannan lokaci na sake jin karfi ya zo mun. Na ji ashe zan iya sake numfasawa. Jami`an `yansandan suka kira ni kusa da su, na fada musu gaskiya.”
Wannan labari yana kunshe da bayani dalla-dalla da wasu daga cikin masu karanta shi, za su iya kasancewa cikin damuwa.
Shekara 9 ke nan, har yanzu Meriance tana neman a mata adalci. Lamarin nata wanda za a iya cewa ya zama na daban, yana nuna hadarin da `yan zuwa neman aiki ko aikatau a wasu wurare masu nisa, da babu bayaninsu a rubuce suke ciki da kuma yadda adalci yake musu wahalar samu har ma da wadanda suka rayu har suke iya ba da labarinsu.
A shekarar 2015, `yan sanda sun tuhumi wacce ta dauki Mariance aikin gida, Ong Su Ping Serene, da laifin haddasa mata tsananin rauni, da kokarin aikata kisan kai, da safarar bil`Adama da saba wa dokokin shige da fice.
Ta ce sam atabau ita ba ta aikata laifuffukan da ake tuhumarta ta aikata ba. Meriance ta ba da shaida a kotu, kafin a karshe ta koma gida cikin iyalanta.
Bayan shekara biyu ta samu labari ta hannun ofishin jakadanci na Indonesiya cewa masu tuhumar matar, sun janye tuhume-tuhumen saboda rashin wadatacciyar shaidar ta aikata.
“Wacce ta dauketa aikin gidan aka kyale ta, ina adalci a nan?” Jakadan kasar a Maleshiya, Harmono (`yan maleshiya da dama suna amfani da suna guda daya tilo) da ya gana da Meriance a watan Oktoba yake shaida mata.
Ofishin Jakadancin ya daukar mata lauya kuma yana ta kamun kafar a ci gaba da yi wa wacce ta dauki Meriance aikin gida shari`a.
“Ina dalilin jinkirin? Shekaru biyar ba su isa a ce an yanke hukunci ba? Idan ba mun ci gaba da tambaya ba, za a mance da batun, musamman da yake tuni Meriance ta riga ta dawo gida.
An rasa gane me ya sa kalilan daga cikin cin zarafi ne a karshe ake yin hukunci a Maleshiya amma masu gangami suke nuni da wata al`ada da take daukar `yan aikin gida, da yawancinsu `yan kasar Indonesiya ne, a matsayin marasa matsayi da ba za su iya samun kariya iri daya da ta `yan Maleshiya ba.
Ma`aikatar harkokin wajen Maleshiya ta sanar da BBC cewa “za su tabbatar da an yi adalci kamar yadda doka ta tanadar”
A 2018 wata kotun Indoneshiya ta daure wasu mutum biyu saboda safarar Meriance.
Alkalin ya yanke hukuncin cewa an tura ta yin aiki a Maleshiya “a matsayin mai taimaka wa Ong Su Ping Serene aikin aikin gida, wacce ta azabtar da ita, ta mata raunuka ba dan kadan ba” da ya kai ga kwantar da ita a asibiti.
An yi bayanin irin bakar wahalar da Meriance ta sha a lokacin yanke hukuncin, da ya ce wacce ta dauketa aikin tai ta dukanta, ta karya mata karan hanci, a wani lokacin take azabtar da ita da wani karfe da take sawa a wuta, da fincis, da batin, da filaya.
Shekara takwas ke nan har yanzun akwai miki da tabon azabatar da ita da aka yi a jikinta.
Akwai wani tabo mai zurfi a lebenta na sama, an cire mata hakora hudu aka nakasa mata kunne daya. Mijinta Karvius ya ce da aka ceto ta, kasa gane ta ya yi: “Na yi matukar kaduwa da suka nuna mun hotunan Meri a asibiti.”
A bara, Maleshiya da Indonesiya sun sa hannu a kan wata yarjejeniya ta kyautata jin dadin `yan kasar Indonesiya `yan aikin gida da ke kasar. A yanzun haka Indonesiya tana kamun kafa a ci gaba da shari`ar wacce ta dauki Meriance aiki.
Ma`aikata da ba a san adadinsu ba irinta, suna cikin wani mawuyacin hali saboda an kwace fasfonsu, suna zaune da wadanda suka dauke su aiki a kasashen waje, sun zama babu wata takamemiyar hanyar neman agaji.
`Yar Majalisar Dokoki ta Maleshiya Hanna Yeoh da take so ta ga an kawo karshen abin da ta kwatanta da al`adar gum a kasar a game da cin zarafin `yan aikin gida, ta ce “akwai bukatar kowa da kowa ya kara sanin hakkin da ya hau kansa”
Ma`aikatar aikin kwadago ta Maleshiya ta ce akwai `yan kasar Indonesiya `yan aikin gida su fiye da 63,000 da suke kasar, amma wannan ba su hada da ma`aikatan da babu wani ajiyayyen bayani a game da su ba.
Su wadannan ba a san adadinsu ba. Ofishin jakadanci na Indonesiya ya ce ofishin ya samu rahotanni na cin zarafi guda kusan 500 a shekaru biyar da suka gabata.
Jakada Hermomo ya ce wannan adadi ma, dan kadan ne da aka iya ji, saboda yawancin cin zarafin, musamman ga ma`aikatan da babu bayanansu a rubuce, ba a sani.
“Ban san ranar kawo karshen wannan lamari ba. Abin da muka sani shi ne, a kullum ana samun karin wadanda ake azabtar da su, da kin biyansu hakkokinsu na aiki da sauran laifuka. “
Ofishin ba zai iya cewa ga yawan hukunci da aka yi a kai ba. Sai dai akwai wasu hukunce-hukunce manya da aka yi. A 2008 an yanke wa wata mata `yar kasar Maleshiya daurin shekara 18 a gidan yari saboda azabtar da `yar aikinta ta gida `yar kasar Indonesiya.
Bayan shekara 6 an yanke wa wasu ma`aurata hukuncin kisa saboda kashe `yar aikinsu ta gida `yar kasar Indonesiya.
`Zan yi yaki hakan har bayan raina`
“Zan yi gwagwarmayar neman adalci har karshen raina” Meriance take furtawa. “Ina so in iya tambayar tsohuwar wacce ta dauke ni aiki, `Me ya sa kika azabtar da ni?”
Tana da shekara 32 a lokacin da ta yanke shawarar neman aiki a kasashen waje domin “ya zama `ya`ya sun daina kukan abinci”.
Rayuwar ta yi zafi a kauyensu da ke Yammacin Timor/West Timor, inda babu wutar lantarki ko ruwan sha mai kyau. Kuma albashin mijinta, aiki yake yin a yini a biya shi, da ba ya isarsu ciyar da su, su shida.
Ta samu aiki a Maleshiya da mafarkin gina wa iyalanta gida.
Da ta isa Kuala Lumpur a watan Afrilu na shekarar 2014, wanda ya kai ta, ya karbe mata fasfo ya mika wa wacce ta dauketa aiki. Masu daukar aiki a Indonesiya sun riga sun karbe mata wayarta.
Amma Meriance tana sa ran rayuwa mai kyau. Aikinta shi ne “kula da kaka” mahaifiyar Serene da ta dauketa aiki, wacce a lokacin tana da shekara 93.
Mako uku da soma aikinta, ta ce ta soma cin duka.
Wata rana da yamma Serene tana so ta dafa kifi, amma ta tarar babu kifin a cikin firji saboda Meriance ta yi kuskuren sa shi a firiza. Mariance ta ce kawai sai ta ji an kwada mata daskararren kifi. Jinni ya soma fita mata ta ka.
Ta ce bayan wannan, a kullum sai an buge ta.
Ta ce ba a taba bari ta fita daga wannan gida ba. Kofar gida a garkame take a kowanne lokaci, kuma ba ta da dan mabudi a hannunta. Mutane hudu da suke makwabtaka da su a dai wannan gida, ba su da masaniyar tana wannan gida, har sai ranar da `yan sanda suka isa gidan.
“Ni ganta ne kawai ranar a daren da aka ceto ta,” daya daga cikinsu ta bayyana.
Meriance ta ce akan tsagaita dukanta da azabtar da ita ne, a lokacin da wacce ta dauketa aiki ta gaji da gana mata azaba. Daga nan sai ta umarci Meriance ta goge jininta da ya zuba a kasa da jikin bango.
Ta ce akwai wasu lokutan da take tunanin kashe kanta, amma idan ta tuna `ya`yanta hudu da ta baro a gida, sai ta ci gaba da jurewa.
“Har ila yau nakan yi tunanin ramawa, sai dai da na rama da na mutu” kamar yadda ta bayyana.
Sannan wata rana – a karshen 2014- ta tsaya ta kalli kanta a madubi sai ta ji wani sauyi: “Ba zan ci gaba da daukar wannan ba. Na yi fushi, ba wai da wacce ta dauke ni aiki ba. Ina fushi ne da ni kaina. Ya kamata in kokarta fita.”
A lokacin ne ta rubuta wasikar da za ta kwace ta.
BBC ta yi yunkuri fiye da shurin masaki don kai wa ga wacce ta dauketa aikiOng Su Ping Serene don jin ta bakinta a game da zargin da ake mata, amma ta ki cewa uffan.
Meriance ta ce gwagwarmayar da take yi ta neman a mata adalci, har ila yau tana yi ne a madadin saura kamar ta, - da wadanda ba su iya kai labara ba.
Jakada Hermono da ke bin wani cin zarafin na `yar aikin gida da ya ce “azabtarwar ta saba wa hankali” ga horo da yunwa. Da aka cetota, nauyin bai wuce kilogiram 30 ba.
A yanzun haka ana nan ana yi wa wacce ta daukrta aiki shari`a. Sai dai akwai wasu kamar Adelina Sau `yar shekara 20 da ba a ceto ta a kan kari ba. An ce wacce ta dauketa aiki ta hana ta abinci tare da azabtar da ita, da suka yi sanadiyyar mutuwarta.
An tuhumi wacce ta dauketa aiki da laifin kisa sai dai a shekarar 2019 bangaren masu tuhuma ya janye tuhume-tuhumen. An yi watsi da bukatar da aka gabatar shekarar da ta gabata, ta a sake tado da shari`ar.
Adelina ta fito ne daga gunduma daya da Meriance a West Timor.
Meriance ta ce ta hadu da mahaifiyar Adelina a kauyensu, ta sanar da ita, “Duk da diyarki ta rasu, muryarta tana nan a tattare da ni. “