Ko gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa za su iya samar da lantarkin bai ɗaya?

Asalin hoton, BBC/ COLLAGE
Gwamnatocin jihohin Kano da Katsina da Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya na wani yunƙurin samar da wata haɗaka ta samar da wutar da isassishiyar lantarkin da jihohin uku ke buƙata.
A ƙarshen makon nan ne gwamnonin jihohin uku - Abba Kabir Yusuf da Umar Dikko Radda da Umar Namadi suka tattauna da kamfanin wuta na KEDCO da Future Energies Africa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar makamashi a ƙasar Morocco.
Gwamnonin sun ce suna son fito da haryar yin haɗaka a fannin wutar lantarki a yankin musamman abin da ya shafi amfani da makamashin rana da iska ƙari a kan wadda suke samu daga babban layin ƙasa.
Ba dai a ƙarƙare yarjejeniyar ba kawo yanzu amma ana ganin yiwuwar al'amarin bisa la'akari da halartar gwamnonin zuwa wurin taron da kansu ba wakilci ba.
Abu 6 da gwamnonin ke son cimma

Asalin hoton, Katsina Govern House
Kwamishinan ma'aikatar lantarki ta jihar Kano, Dakta Gaddafi Sani Shehu wanda ya halarci taron ya ce jihohin sun ƙulla alaƙar ne dangane da abubuwa kamar haka:
- Jihohin uku bisa haɗin gwiwar kamfanin rarraba wuta na KEDCO sun fahimci dole ne a samar da kuɗaɗe domin tallafa wa kamfanin.
- Fito da dokokin da suka bai wa jihohi da ɗaiɗaiku damar kafa kamfanonin wutar lantarki kamar yadda sabuwar dokar lantarki ta Najeriya ta tanada.
- Wayar da kan al'ummomin jihohin uku kan rawar da ya kamata su taka dangane da haɓakar wutar lantarki a yankin.
- KEDCO na buƙatar kuɗade a matakin farko kamar naira biliyan 50, inda jihohin za su bayar da rabi shi kuma kamfanin na KEDCO ya samar da rabi.
- Jihohin na son ganin kowacce jiha ta samu aƙalla wutar lantarki mai yawan megawatts 200 kowacce ƙari a kan ƙasa da megawatts 100 da kowacce jihar ke samu a yanzu haka. A yanzu haka jihohin uku na samun megawatts 300 daga babban layin wutar Najeriya.
- Gwamnonin jihohin na son samar da wutar ga yankin ta hanyar alkilta albarkatun rana da iska da kuma ruwa.
'Abu ne mai kyau amma ba dole ne a yi haɗaka ba'
Injiniya Sani Bala Tsanyawa wanda masanin wutar lantarki ne sannan kuma ɗanmajalisar wakilai da ke wakiltar jihar Kano a majalisar wakilan Najeriya, ya ce wannan al'amari ne mai kyau.
" Idan ka duba da ma a duk Najeriya babu wani yanki da Allah ya yi wa albarka da makamashi maras gurɓata muhalli kamar iska da rana da ruwa. Ko a duniya ƙasashen da suke yin irin wannan abu za ka ga suna da yanayi irin na arewacin Najeriya."
Sai dai kuma Injiniya ya ce ba lallai sai jihohin uku sun haɗu ba kasancewar dokar ƙasa ta bai wa kowacce jiha ta kafa wutarta sannan ma ta kafa hukumar da ke saka idanu kan kamfanin.
"Ita harkar nan ba sai jihohi uku sun haɗu ba. Misali jihohin Kudu sun yi nisa wajen kafa hukumomin da ke ƙa'idance samar da sayar da wutar lantarki. Kowacce jiha bisa dokar wutar lantarki da aka gyara ta 2022 tana da damar yin waɗannan abubuwa," in ji Injiniya Sani Bala Tsanyawa.
Shawara 10 ga gwamnoni
Injiniya Sani Bala ya ƙara da cewa Sai dai kuma ya ce idan har dole ne sai jihohin sun haɗu ta dole a yi la'akari da wasu shawarwari domin cin moriyar tsarin.
- Kowacce jihar ta samu filin da za ta rinƙa yin farantan wuta na hasken rana da kuma rumbun wutar.
- Ɗora wutar kowacce jiha a kan babban layi wato grid domin sayarwa.
- Dole ne a tabbatar da idan an sayar da wutar ana ajiye kuɗin domin gyare-gyare na yau da kullum.
- Dole ne a saka idanu kan kayan wutar a kowacce jiha domin gudun maimata irin abin da ya faru da cibiyar wuta mai amfani da iska da gwamnatin tarayya ta fara a Katsina.
- Tabbatar da tsaro a wuraren da za a kafa tashoshin wutar domin gudun masu ɓarnata kayayyakin kamar abin da ya faru a Katsina.
- Tabbatar da gaskiya da riƙon amana kasancewar za a yi amfani da kuɗaɗen al'umma.
- Dangane kuma da amfani da ruwa to sai an tabbatar da cewa an fitar da hanyoyin da idan aka saki ruwan ba zai ɓarna ba musamman ga manoma.
- Yin cikakken nazari kan yadda al'amarin zai bayar da fa'ida maimakon.
- Ita kanta KEDCO sai an saka mata ido bisa la'akari da abin da ya faru da ita a farko lokacin da aka kafa ta inda basussuka suka yi mata katutu.










