Me ya sa ake taka-tsantsan a tattaunawar Iran da Amurka?

Asalin hoton, Getty Images
Iran da Amurka sun fara wata sabuwar tattaunawa a ƙasar Oman a daidai lokacin da takun-saƙar siyasa da na soji ke ƙara ƙamari a tsakaninsu, bayan hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran na wani ɗan lokaci.
Wannan dai ita ce tattaunawa ta farko kai-tsaye tun bayan yaƙin da aka kira "yaƙin kwanaki 12", wanda ya ɓarke bayan harin da Isra'ila ta kai wa Iran tare da sanya fargabar ɓarkewar wani gagarumin yaƙi a yankin.
Tattaunawar dai na gudana ne a daidai lokacin da ake takun saƙa tsakanin ɓangarorin biyu.
Iran dai ta dage cewa a shirye ta ke ta sasanta, amma bisa sharuɗɗanta, yayin da Amurka ta yi gargaɗin cewa har yanzu ana ci gaba da nazarin ɗaukar matakin soji idan tattaunawar ta ci tura.
Kalaman sun ƙara nuna rashin tabbas kan ko diflomasiyya za ta iya hana ɓarkewar rikici.
Tsawon shekaru da dama, dangantakar da ke tsakanin Iran da Amurka na ƙara tsami, sakamakon rashin yarda da takunkuman tattalin arziki da barazanar ɗaukara matakan soji.
Masu sharhi dai na ganin tattaunawar ta Oman a matsayin wani yunƙuri na hana al'amura rikiɗewa zuwa yaƙin da zai wargaza yankin.
Amma ga wanda bai san siyasar duniya ba, babbar tambayar da zai yi ita ce, mene ne ainihin abubuwan da za a tattanuna a wannan ganawar, me ya sa ta ke da muhimmanci, kuma me zai iya faruwa bayan an kammala?
Maƙasudin tattaunawar, da abin da ya sa ake taka tsan-tsan a kai?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babban abin da aka sanya a gaba a tattaunawar dai shi ne shirin nukiliyar Iran.
Tehran ta ce shiri ne na amfani fararen hula, kamar samar da makamashi, amma Amurka da ƙawayenta na fargabar cewa Iran za ta iya amfani da ita wajen ƙera makaman ƙare dangi.
Amurka dai na son Iran ta dakatar ko rage yawan tace sinadarin Uranium, ta kuma amince da masu bincike na ƙasa da ƙasa da za su tabbatar da ingancin aikin, sannan ta koma kan tsauraran sharuɗɗan yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015.
A nata ɓangaren Iran na son a ɗage takunkumin karya tattalin arziki da Amurka ta ƙaƙaba mata, tana mai cewa ya shafi tattalin arzikinta da kuma rayuwar ƴan ƙasarta.
Babban musababbin tashin hankali shi ne shirin makami mai linzami na Iran.
Amurka ta dage cewa dole ne a tattauna batun saboda makamai masu linzami na iya ɗaukar manyan bama-bamai.
Iran dai ta musanta hakan, tana mai cewa shirinta na samar da makamai masu linzami wani ɓangare ne na tsaron ƙasarta kuma abu ne da za ta lamunci sanya ma ta baki a ciki ba.
Rikicin dai na ƙara ta'azzara ne saboda barazanar ɗaukar matakan sojoji. Shugaba Donald Trump ya sha yin gargaɗin cewa Amurka za ta iya yin amfani da ƙarfin soji idan tattaunawar ta ci tura, yayin da Iran ta ce za ta mayar da martani kan duk wani harin da aka kai, ciki har da matakan da za su kawo cikas ga jigilar mai a kasuwar duniya ta mashigin Hormuz.
Me ya sa Iran ta buƙaci a yi ganawar a Oman?

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Iran dai ta na ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen ƙasar Abbas Araqchi, wani gogaggen jami'in diflomasiyya da ya halarci tattaunawar nukiliyar da ta gabata.
Ɓangaren Amurka kuma yana ƙarƙashin jagorancin wakilin shugaba Trump na musamman a yankin gabas ta tsakiya, Steve Wittkopf, wanda kuma ke da hannu a tattauna wasu muhimman batutuwan diflomasiyya.
Tun da farko dai an shirya gudanar da tattaunawar a Turkiyya, amma Iran ta buƙaci a mayar da ita Oman.
Oman ta kwashe shekaru da dama tana kasancewa mai shiga tsakani a batutuwan da ke tsakanin Tehran da Washington, musamman kan batutuwan da suka shafi nukiliya.
Ga Iran, Oman wuri ne mai aminci ta fuskar diflomasiyya, mai tarihin ɗaukar nauyin tattaunawa ba tare da matsin lamba na siyasa ba.
Tehran ta kuma buƙaci tattaunawar ta kasance ta ɓangarorin biyu kaɗai, ba tare da haɗawa da wasu ƙasashen yankin ba.
Iran dai ta damu matuƙa cewa shigar da ƙarin ƙasashe tattaunawar zai sa ajandar ta faɗaɗa ta haɗa da batutuwan da suka shafi makamai masu linzami da kuma tasirinta a yankin, lamarin da take adawa da shi.
Me zai faru bayan tattaunawar?

Asalin hoton, Getty Images
Yawancin masana ba sa tsammanin wannan tattaunawar za ta haifar da sakamako nan take.
Maimakon haka, ana ganin ta a matsayin yunƙuri na rage tashin hankali da kuma hana ɓarkewar rikici.
Ga Iran, manufar ita ce ta motsa hannun agogo baya, rage barazanar soji, dakuma kare abin da take gani hakkinta ne na ƙare kai.
Ga Amurka, ita ce ta yi ƙoƙarin hana Iran cimma ƙarfin nukiliyar soja ba tare da shiga wani sabon yaƙi a Gabas ta Tsakiya ba.
Duk da haka, haɗarin ya kasance, idan tattaunawar ta ci tura, za a iya ɗaukar matakan soji, wanda zai shafi tsaron yankin da tattalin arzikin duniya ta hanyar tashin farashin mai.
A halin yanzu, tattaunawar Oman ta kasance wani shinge maras kauri da aka gitta tsakanin diflomasiyya da rikici, wani yunƙuri ne na ƙarshe na tattaunawa kafin yiwuwar ɗaukar tsauraran matakai.











