Ko yarjejeniya tsakanin Turkiyya da Ƙurdawa za ta iya kawo ƙarshen PKK?

A Kurdish woman holds a portrait of jailed PKK leader Abdullah Ocalan during a rally

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A baya dai Turkiyya ta yi tattaunawar zaman lafiya da shugaban PKK Ocalan, amma abin ya ci tura, kuma batun Ƙurdawa na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiyar Turkiyya.
    • Marubuci, Selin Girit and Merve Kara-Kaska
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Turkish
  • Lokacin karatu: Minti 8

Abin mamaki ne ga duk wanda ke bibiyar siyasar Turkiyya lokacin da shugaban babbar jam'iyyar kishin ƙasa ta kasar ya yi kira ga shugaban ƙungiyar ƴan ta'addar Ƙurdawa na PKK da ke ɗaure a gidan yari domin a sasanta.

Devlet Bahceli, shugaban jam'iyyar Nationalist Movement Party (MHP) kuma babban aminin shugaba Recep Tayyip Erdogan a gwamnatin Ƙasar, a wani mataki na ba-zata ya sanar da cewa za a iya barin shugaban PKK Abdullah Ocalan ya yi jawabi ga majalisar dokokin Turkiyya bisa sharaɗin wargaza ƙungiyar.

"Idan aka cire wariyar da shugaban ƴan ta'adda ke fuskanta, to ya zo ya yi jawabi," in ji Bahceli. "Bari ya yi iƙirarin cewa an kawo ƙarshen ta'addanci gaba ɗaya kuma an wargaza ƙungiyar."

Kuma ya yi nuni da cewa hakan na iya kai wa ga sakin Ocalan.

Devlet Bahceli ya kasance yana adawa da duk wani rangwame ga Kurdawan Turkiyya kuma ya taba jefa igiya a wani gangamin neman a maido da hukuncin kisa domin a ƙashe shugaban ƙungiyar ta PKK.

Matakin ba zato ba tsammani da ya ɗauka ya haifar da ce-ce-ku-ce kan cewa ana ci gaba da ƙoƙarin da ake yi a bayan fage na cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen PKK.

Mece ce PKK kuma wane ne Ocalan?

PKK (Jami'yyar Ma'aikatan Kurdistan) ƙungiya ce ta masu fafutuka da aka kafa a shekara ta 1978, kuma ta kaddamar da iƙirarin aƙidar aware a kudu maso gabashin Turkiyya shekaru shida bayan haka.

The PKK's second in command Murat Karayilan (2nd Left) walks surrounded by an escort at a PKK base in the Qandil mountains, in northern Iraq

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Turkiyya da Amurka da ƙungiyar EU sun ayyana PKK a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda

Yaƙin da take yi ya hada da hare-haren ƙunar baƙin wake da hare-haren sunƙuru a wuraren soji, da cibiyoyin gwamnati, da kuma ofisoshin diflomasiyyar Turkiyya a ƙasashen waje. Sama da mutane 40,000 ne aka kashe a rikicin.

Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana ta a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda.

Shugabanta Abdullah Ocalan, mai shekaru 75 a duniya, ya kasance mai faɗa a ji a fagen siyasar Ƙurdawa, kuma ya na da baƙin jini tsakanin al'ummar Tuurkawa, kuma gwamnatin Turkiyya na kallonsa a matsayin maƙiyin ƙasar, amma mafi yawan masu kishin Ƙurdawa na girmama shi.

A Turkish gendarme stands guard next to PKK leader Abdullah Ocalan in a bullet-proof glass cage dock on the first day of his treason trial at a state security court in Imrali island

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yanke wa Ocalan hukuncin kisa bisa laifin cin amanar ƙasa a shekarar 1999, amma sakamakon soke hukuncin kisa a shekara ta 2002 an sauya hukuncin nasa zuwa ɗaurin rai da rai.

Dakarun sojin Turkiyya ne suka kama shi a 1999 a Kenya, kuma tun wannnan lokacin aka yanke masa hukunci ɗaurin rai-da-rai a wani gidan yari da ke kan wani tsibiri da ke yankin kudancin Istanbul.

Ƙurdawa su ne karamar ƙabila mafi yawan al'umma a Turkiyya. Su ne kusan kashi ɗaya cikin biyar na al'ummar ƙasar da yawansu ya kai miliyan 85.

Makwabtan Turkiyya Iraki, da Iran da Siriya suma suna da tsirarun Kurdawa a cikin al'ummarsu .

Wata dama ta samu

Kwana guda bayan Bahceli ya bayar da shawarar da ba a taɓa yin irin ta ba, an bayar da izinin a ziyarci Ocalan a gidan yari bayan ya kwashe watanni 43 ya na keɓe gaba ɗaya ba tare da samun damar tattaunawa da lauyoyinsa ko danginsa ba, kuma ya fito da martaninsa na farko. Ya ce zai iya "sauya tsarin daga tashin hankali zuwa siyasa".

President Recep Tayyip Erdogan speaks to the Nationalist Movement Party leader Devlet Bahceli

Asalin hoton, Turkish Presidency / Murat Kula

Bayanan hoto, Shugaba Erdogan ya ba da cikakken goyon baya ga shawarar "jarumta" da abokin tarayyarsa ya bayar, yana mai cewa hakan ya buɗe "kafar wata dama" kuma ya yaba masa a matsayin shugaba mai hangen nesa.

Sai dai a wannan rana ƴan ta'addar PKK biyu sun kai hari a wani kamfanin jiragen sama mallakar gwamnati a kusa da Ankara babban birnin ƙasar Turkiyya, inda suka kashe mutane biyar tare da jikkata 22.

Ƙungiyar ta PKK ta ce harin ba shi da alaƙa da wannan sabuwar goron gayyatar, kuma an daɗe ana shirin kai harin.

Har ila yau, Turkiyya ta mayar da martani da kai hare-hare kan matattarar PKK a makwabtanta Siriya da kuma Iraki.

Waɗannan lamuran da suka afku za su iya kashe yiwuwar tsarin zaman lafiya da ake niyyar ƙyanƙyashewa amma ba su yi wannan tasirin ba.

Relatives and friends grieve near the coffin of Cengiz Coskun one of the victims of the PKK attack in Ankara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harin da ƴan ta'addar PKK suka kai a wani kamfanin jiragen saman Turkiyya da ke Ankara ya kashe mutane 5, kwana guda bayan da gwamnati ta miƙawa Abdullah Ocalan goron gayyata.

Shugaba Erdogan ya ba da cikakken goyon baya ga shawarar "jarumta" da abokin tarayyarsa ya bayar, yana mai cewa hakan ya buɗe "kafar wata dama" kuma ya yaba masa a matsayin shugaba mai hangen nesa.

Duk da haka batun yiwuwar tattaunawar sulhun ya fuskanci barazana ƴan kwananki kaɗan bayan haka a lokacin da gwamnatin Turkiyya ta kori magadan garin wasu garuruwa guda uku da ke yankin kudu maso gabashin ƙasar inda a ke da yawan al'ummar ƙurdawa.

An zargi maggadan garin jam'iyyar DEM mai goyon bayan Kurdawa a garuruwan Mardin da Batman da Halfeti da alaƙa da ƙungiyar ta PKK, an kuma koresu daga mukamansu, aka maye gurbinsu da wasu masu gudanar da mulki da gwamnati ta naɗa, lamarin da ya haifar da zanga-zanga da dama a al'ummar Ƙurdawa.

A banner is seen in front of a group of protesters in Diyarbakir during a demonstration against the dismissal of three pro-Kurdish mayors

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kurdawa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da korar da aka yi na baya-bayan nan da aka yi wa magadan gari masu goyon bayan Kurdawa a garuruwan Kudu maso Gabashin ƙasar inda suka yi rubuce-rubucen da ke cewa: "Ba za a iya karya nufin jama'a ba."

Jam'iyyar DEM wadda ita ce jam'iyya ta uku mafi girma a majalisar dokokin Turkiyya ta yi tir da korar da aka yi.

A cikin wata sanarwa da DEM ta fitar ta ce "Yayin da muke sa ran za a miƙa hannu don samun mafita da zaman lafiya, an keta muradun jama'a."

A baya dai an kori wasu gomman magadan gari masu goyon bayan Kurdawa daga mukamansu bisa irin waɗannan tuhume-tuhume.

Yanayin siyasar yanki

Abin da ya haifar da gayyatar da Ankara ta yi wa Ocalan ya kasance babban abin tambaya a cikin ƴan makonnin da suka gabata.

Ana tunanin wani mahimmin abin da ya jawo hakan shi ne sauyin yanayin siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya, inda Iran da ƴan amshin shatanta ke shan wahala a hannun Isra’ila cikin ƴan kwanakin nan.

Wani masani ɗan kasar Turkiyya Mesut Yegen ya shaida wa BBC cewa "Turkiyya da Iran sun samarwa tsirarun ƙurdawan da ke Iraki da Siriya ta hanyar daidaita tsakaninsu."

A man walks past a mural painting of Iranian flags in a street in Tehran on October 26, 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wahalar da Iran da ƴan amshin shatanta ke sha a hannun Isra'ila na iya zama sanadiyyar wannan gayyata da Ankara ta yi wa shugaban na PKK.

"Yanzu wannan daidaiton yana fuskantar barazanar dagulewa, kuma ina ganin Turkiyya na ƙoƙarin sake daidaita kanta ta hanyar ɓullo da wani tsari na sulhu," in ji shi.

Yegen ya kuma ƙara da cewa raguwar tasirin Iran a Siriya da Iraki zai iya baiwa PKK da abokan tarayyarta a yankin, kuma mai yiwuwa Turkiyya na son ɗaukar matakin riga-kafi.

Har ila yau, PKK na iya kasancewa a shirye don cimma yarjejeniya da Ankara saboda "ba za su so su fuskanci Turkiyya a cikin wani yanayi na rashin iko" a Gabas ta Tsakiya ba, in ji shi.

Turkish President Recep Tayyip Erdogan addresses his supporters gathering to celebrate reelection victory in presidential runoff in Ankara on May 28, 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A bara ne aka sake zaɓen shugaba Erdogan a karo na uku kuma bisa ga kundin tsarin mulkin ƙasar bai cancanci tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara a shekarar 2028 ba.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana kuma tunanin siyasar cikin gida a Turkiyya ita ce babbar al'amari a cikin sabuwar shawarar da Ankara ta yi na sasanta batun Ƙurdawa.

Wasu na ganin cewa babban abin da gwamnatin ƙasar ta sanya gaba shi ne ta ci gaba da tabbatar da shugaba Erdogan na wani wa'adi na daban, kuma a dalilin haka suke neman goyon bayan Kurdawa.

Erdogan ya shafe sama da shekara ashirin yana kan karagar mulkin Turkiyya, da farko a matsayin firaminista, sannan daga baya ya zama shugaban ƙasa.

A shekarar da ta gabata ne aka sake zaɓen shi a karo na uku, kuma bisa ga kundin tsarin mulkin ƙasar, sai dai idan majalisar dokokin ƙasar ta kira zaɓen da wuri, ba zai iya tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a shekarar 2028 ba.

Domin sauya kundin tsarin mulki, kawancen gwamnati na buƙatar goyon bayan jam'iyyar DEM da ke goyon bayan Ƙurdawa.

Za a iya gudanar da ƙuri'ar raba gardama kan batun sauya kundin tsarin mulki idan ƴan majalisa 360 a majalisar mai kujeru 600 suka marawa hakan baya. Gamayyar gwamnatin na da kujeru 321 yayin da DEM ke da 57.

Tattaunawar sulhu da aka yi a baya

A baya gwamnatin Turkiyya ta fara tattaunawa da Abdullah Ocalan da PKK a shekarar 2012.

Wannan tsari da kuma tsagaita wutar da aka kwashe tsawon shekaru uku ana yi amma ya ruguje a watan Yulin shekarar 2015, wanda ya haifar da ƙazamin faɗa tsakanin PKK da dakarun gwamnati a kudu maso gabashin Turkiyya.

Dubban ƴan siyasa masu goyon bayan Kurdawa ne ake zargi da alaƙa da ta'addanci inda aka ɗaure su bayan wani samame da aka gudanar.

Turkish Kurdish women flash V-signs during a women's day event in Silopi in March 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu masana na ganin ya kamata taswirar zaman lafiya ta ƙarshe ta haifar da tsarin dimokraɗiyya baki ɗaya a Turkiyya

Karabekir Akkoyunlu, daga Makarantar nazarin Gabashin duniya da Afirka (SOAS) a Jami'ar London ya ce "An gudanar da tsarin da aka yi a baya ne ta hanyar yin watsi da majalisar dokoki ba tare da tabbatar da mafi ƙarancin amincewa tsakanin jam'iyyun ba."

"Ba za a iya magance batun Kurdawa daban da tsarin dimokuradiyyar Turkiyya ba," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Yayin da Ankara ke taka tsantsan kuma ta guji bayar da duk wata alamar taswirar zaman lafiya a wannan karon, ba a san ko za a iya cimma yarjejeniya ba.

Bugu da ƙari, harin na PKK a watan da ya gabata ya sanya ayar tambaya kan ikon da Abdullah Ocalan ya ke da shi kan ƙungiyar bayan shafe shekaru 25 a gidan yari.

Da alama dai ra'ayoyin al'ummar Turkiyya ba su goyi bayan yarjejeniyar da aka shirin kullawa da ƴan ta'addar PKK ba wanda zai kai ga sako shugabanta daga gidan yari.

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan da cibiyar nazarin zamantakewar al'umma ta Ankara ta gudanar ta gano kusan kashi 75% na waɗanda suka kaɗa ƙuri'ar suna adawa da batun cewa Abdullah Ocalan zai yi jawabi a gaban majalisar dokokin Turkiyya.