Me ƙasashen Brics suke son cimma a taron ƙungiyar a Rasha?

Asalin hoton, Getty Images
Taron ƙasashen da tattalin arzikinsu ke bunƙasa wato Brics, wanda aka fara a ranar 22 ga Oktoba a birnin Kazan, shi ne babban taron ƙasa da ƙasa da aka yi a Rasha tun bayan da ƙasar ta fara yaƙi a Ukraine.
Shi ma sakatare-janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya halarci taron - lamarin da Ukraine ta nuna rashin jin daɗinta. Rasha na so ne ta bayyana wa Amurka da Turai cewa ta isa.
Amma kowace ƙasa da ta halarci taron, tana nata buƙatun da take burin samu, kuma ba dole ba ne ya zama sun yi dai-dai da na Rasha.
Wakilan BBC a yankunan sun yi nazari tare da yin cikakken bayanin abubuwan da manyan ƙasashen suke burin samu.
Nasara ga Putin
Grigor Atanesian, BBC Rasha
A wajen shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, wannan taro wata dama ce ta nuna wa ƙasashen yamma ƙwanji, sannan ya fahimtar da mutane ƙasarsa cewa ƙasashen duniya za su iya tsayawa ba tare da ƙasashen na yamma ba.
Shugabannin ƙasashe sama da ƙasashe 30 ne suka amince da shiga ƙungiyar.
Daga ciki akwai shugabannin China da India da Iran da Turkey da Afirka ta Kudu da Masar da Ethiopia da wasu ƙasashen.
Daga cikin ƙasashen, akwai waɗanda suke fama da takunkumi daga ƙasashen yamma kamar Rasha, sannan kuma akwai ƙawayen Amurka da ma NATO, kamar Turkiyya.
Har yanzu ba a fahimci wace fa'ida kowace ƙasa take so ta samu ba. Sai dai samar da wani kuɗin da zai yi gogayya da dala na cikin gaba-gaba a taron, inda shafin taron na yanar gizo ma ya tunatar da mahalarta su zo da tsabar da kuɗin da za su kashe, domin katin cire kuɗi na Mastercarda da Visa ba sa aiki a Rasha.
China tana ta yi amfani da Brics wajen sauya tsare-tsaren duniya

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Chen Yan, BBC China
Bayan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, Rasha za ta ƙara fahimtar cewa China - duk kusancin da ke tsakanin su - ba za ta so su zama ƙawaye ba, musamman a ɓangaren tsaro.
Misali, China ta taƙaita fitar da wasu kayayyakin da ake tunanain za a iya amfani da su wajen haɗa makamai zuwa Rasha saboda Amurka ta buƙaci hakan.
Amma Rasha da China suna da tunani iri ɗaya a game da ƙasashen yamma, musamman haɗuwarsu a Brics. Don haka shin me China take so?
Tun bayan Yaƙin Duniya na biyu, duniya ta amince da tsare-tsaren da za su taimaka wa ƙananan ƙasashe maso tasowa.
To wane irin tsarin tafiyar da duniya China ke so? a taƙaice dai Xi Jinping yana so a daina takura wa ƙasashen da ke da tsarin mulkin gado. China ba ta so wasu ƙasashe su zama kamar China, amma tana so a samu tsarin da za a rage yi wa wasu ƙasashe katsalandan a harkokinsu, musamman a game da dokokin haƙƙin dan'adam ɗinsu.
China tana so a ƙarfafa tsarin 'ƙarfin iko farko' kafin ƴancin ɗan'adam a mulki.
To ta yaya China za ta cimma wannan burin?
Ƙungiyar Brics ta zama wata matattara na ƙasashe masu adawa da Amurka, sannan muradun ƙungiyar na ƙara fitowa fili a yanzu da take ƙara samun mambobi.
India na so ta zama mai shiga tsakani

Asalin hoton, Reuters
Raghvendra Rao, BBC Hindi
A bana, taron Brics na da matuƙar muhimmanci ga India, domin ƙasar za ta samu damar ganawa da wasu manyan ƙasashen duniya : China da Rasha.
A karon farko a shekara biyar, Firaiminista Nerandra Modi zai gana da shugaban ƙasar China Xi Jinping.
Taron na zuwa ne bayan India ta sanar da cewa ta shiga yarjejeniya da China kan bayar da tsaro a hanyar nan mai tsaron mil 2,100 a yankin Himalayan da ke tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya daɗe yana jawo tankiya tun a shekarar 2020.
Ta hanyar ganawar Modi da Xi, India na tunanin za a samu maslaha kan saɓanin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Haka kuma India na so ta zama mai samar da maslaha da sulhu tsakanin Rasha da Ukraine.
Turkiya: Brics ɗoriya ce a kan EU, ba musaya ba
Emre Temel, Turkish BBC Service
Turkiya ta nuna sha'awarta ta shiga Brics ce a Satumba, kuma ta tura tawaga mai girma ƙarƙashin shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan.
Shugaba Erdogan ana tunanin zai ƙara nanata burin Turkiya na samun assasa kuɗin ƙasashen Brics, sannan ƙasar na so ta ƙulla alaƙa da samun haɗin kan ƙasashe waɗanda tattalin arzikinsu ke bunƙasa.
Sannan Turkiya ta nanata cewa shigarta Brics ba ya nufin za ta fice daga tarayyar turai ba, za ta haɗa ƙungiyoyin biyu ne.
Wata dama ga Iran
Kayvan Hosseini, BBC Persian
Ita Iran tana garin taron na Brics a matsayin wata dama ce, musamman batun nuna wa ƙasashen yamma ƙwanji, wanda ya yi daidai da ra'ayin shugaban addinin ƙasar.
Ayatollah Khamenei ya daɗe yana bayyana ƙiyayya ga yadda dalar Amurka take yadda ta ga gama, musamman wajen juya akalar tattalin arzikin duniya.
Sannan kuma Iran ta daɗe tana fama da takunkumi daga Amurka, da ma wasu ƙasashe da suke ƙawance da Amurka.
Yanayin ƙarfi da tasirin da dala ke da shi a tattalin arzikin duniya ne ya sa takunkumin da aka ƙaƙaba wa Iran ya yi tasiri sosai.
Brazil: Ƙoƙarin faɗaɗa ƙarfin iko
Julia Brown, BBC Brazilian Service
Brazil na cikin ƙasashen da suka fara assasa ƙungiyar Brics.
Akwai wasu abubuwa muhimmai da Brazil za ta amfana da su a ƙungiyar, ciki har da buƙatar yi wa majalisar tsaro na majalisar ɗinkin duniya garambawul.
Tun bayan da shugaban Lula ya lashe zaɓr a zango na uku, sai ya fara ɓullo da wasu tsare-tsare na faɗaɗa ƙarfin ikon ƙasar a duniya.
Samun ƙarfin iko a duniya na cikin muradun gwamnatin Lula. Brazil na so ta samu damar rage ƙarfin dogaro da dalar Amurka da batun sauyin yanayi.

Asalin hoton, Reuters
Taron Brics a wajen ƙasashen Afirka: Damar ƙulla alaƙa da manyan ƙasashen duniya
Bruno Garcez, editan kafofin sadarwa na BBC News Africa
Ƙasashen Afirka guda uku ne a Brics: Afirka ta Kudu, wadda ta shiga ƙungiyar a shekarar 2010, sai Masar da Ethiopia da suka shiga a bana.
Lokacin da Afirka ta Kudu ta shiga ƙungiyar a shekarar 2010, sai aka yi hasashen nahiyar baki ɗaya za ta ci riba.
Duk da cewa tattalin arzikin nahiyar ƙarami ne, amma tana da ɗimbin arziki da ƙasashen turai za su yi hanƙoro.
Sai dai wasu na ganin Najeriya, wadda ta fi girman tattalin arziki a nahiyar ce ya fi kamata ta fara shiga ƙungiyar.
Ga ƙananan ƙasashe waɗanda tattalin arzikinu ke bunƙasa, shiga ƙungiyar Brics wata dama ce domin haɓaka tattalin arzikin su, da shiga alaƙar kasuwanci da samun bashi mai sauƙi da sauran su.











