Mene ne Diwani kuma daga ina ya samo asali?

Asalin hoton, Sheikh Halliru Maraya
Littafin Diwani na cikin litattafan da ake yawan karantawa, musamman a tsakanin mabiya ɗarikar Tijjaniya a faɗin duniya.
Sai dai akwai littafan na Diwani da yawa kuma akwai marubuta da yawa da suka rubuta diwaninsu, waɗanda yawanci baitoci ne na waƙoƙin yabon Annabi Muhammad.
Domin jin tarihin littafin da na'ukansa da ma abin da ya sa littafin yake da muhimmanci, mun tuntuɓi Sheikh Halliru Abdullahi Maraya, wanda fitaccen malamin addinin musulunci ne a jihar Kaduna, inda ya ce littafin na da muhimmanci.
Halliru Maraya ya ce irin yawan da Musulmi suke da shi a duniya na da alaƙa da karɓuwa da littafin ya yi, "saboda Musulmi suna matuƙar son Annabi Muhammmad," kamar yadda malamin ya bayyana.
Ma'anar Diwani

Asalin hoton, Sheikh Halliru Maraya
A game da ma'anar Diwani, Sheikh Halliru Maraya ya ce gundarin kalmar Diwani daga Faransanci ta samo asali, amma yanzu ta narke a cikin Larabci kuma ake amfani da ita a duniya.
"Diwana asali kalma ce ta Farasanci, amma yanzu ta koma Larabci. Abin da take nufi shi ne rajista kamar dai rajistar makaranta ta ɗalibai ko ta sojoji. A Larabci kuma kalmar tana nufin wurin zaman ma'aikata wato sakatariya ko hedikwata," in ji Maraya.
Ya ƙara da cewa a yanzu abin da mutane suka fi tunani da zarar an ce Diwani shi ne littafin waƙe.
"A nan kuma ana nufin wani littafi na musamman da ya tattara ƙasidu na wani mawaƙi ko mawaƙa. Ita kuma ƙasida na nufin tsararriyar waƙa da ta kai baitoci aƙalla bakwai zuwa sama. Idan aka samu littafi mai ƙasidu aƙalla dubu ne ake kira da suna Diwani."
Ya ƙara da cewa duk da cewa akwai littattafan Diwani da dama, "amma yanzu da an yi maganar Diwani, an fi mayar da hankali kan littafin Diwanin Shehu Ibrahim Kaulaha," in ji Maraya.
Ya ce littafi ne da ya tattara waƙoƙin yabon Annabi (SAW) kusan dubu 6, amma ya ce akwai Diwani kusan guda tara.
Ya ce Shehu Ibrahim, wanda aka haifa ranar 8 ga watan Nuwamban 1900 kuma ya rasu a ranar Asabar 26 ga Yulin 1975, shi ne ya rubuta su a lokacin da yake raye domin yabon Annabi.
Zuwan Diwani Najeriya

Asalin hoton, Sheikh Halliru Maraya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A game da hanyar da Diwani ta shigo Najeriya, Sheikh Maraya ya ce wani babban malami, Sheikh Balarabe Jega ne ya kai littafin Najeriya.
"Akwai wani mashahurin malami mai suna Sheikh Balarabe Jega, wanda ɗan garin Jega ne ya fara zuwa da littafan guda shida Kano wajen Shehu Aliyu Sanka. Shi kuma da ya karanta, sai ya yi musu ƙarin bayani, sai ya ba wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Ɗanjinjiri ya buga aka ci gaba da sayarwa."
Malamin ya ce daga bisani ne aka samu Diwani na bakwai mai suna 'Nurul Haq' "wanda Shehu Sani Kafinga ya yi ƙarin bayani wato ta'aliƙi, sannan ya yi wa sauran guda shidan ta'aliƙi sai ya ba wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Abdulyassar ya ci gaba da sayarwa."
Babban malamin ya ce an kai wani Diwanin na takwas mai suna 'Sairul Ƙalb' zuwa ƙasar ta hannun wani malami mai suna Shehu Balarabe Gusau.
"Shi kuma wannan littafin Shehu Ibrahim yana cikin rubutawa ya tafi gidan rahama, shi ya sa bai ƙarasa waƙe haruffan Larabcin ba. Daga baya kuma aka samu "Kanzul Arifina."
Saƙon da ke ciki
Ganin yadda littafin ke da muhimmanci, BBC ta tambayi Sheikh Maraya game da saƙon da littafin ke ɗauke da shi, inda ya ce waƙoƙi ne na yabon Annabi (SAW)shi ya sa yake da karɓuwa sosai.
"Babban saƙon da littafin ke isarwa shi ne koya wa mutane muhimmancin soyayyar Annabi (SAW) da bin umarninsa da girmama sahabbai da girmama iyalan gidan Annabi," in ji shi.
Ya ce littafin na da muhimmanci ne saboda yanayin yawa da Musulmin duniya ke da shi. "Ka ga yanzu a cikin mutum kusan biliyan 8 da ke duniya, akwai kusan Musulmi biliyan biyu. Kuma duk wani Musulmi yana son Annabi. Don haka dole littafin ya samu karɓuwa sosai."
A game da alaƙar Shehu Ibrahim da Najeriya, malamin ya ce shi kansa Shehu Ibrahim Kaulaha ya fara zuwa Najeriya bayan sun haɗu da Sarkin Kano Abdullahi Bayero a Hajji na 1937. Bayan watanni kaɗan daga Hajjin ne Shehu Ibrahim ya ziyarci Kano.
A game da bambancin littafin da sauran littattafan yabo, Sheikh Maraya ya ce ƙa'idar ita ce duk littafin yabo da yake ɗauke da ƙasidu aƙalla 1000, to za a iya kiransa da Diwani.
Ya ce shi ma littafin Ishiriniya ana kiransa da Diwanin Alfazazi, "amma a ƙa'idar ma'auni littafin bai cika sharuɗɗa ba domin ƙasidun ba su kai 1,000 ba," in ji shi.










