Me ya sa zaɓen ƙananan hukumomin Legas ke da muhimmanci?

- Marubuci, Yusuf Akinpelu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 3
Masu zaɓe sama da miliyan bakwai ne ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen waɗanda za su shugabanci ƙananan hukumomi 20 da ƙananan yankunan mulki 37, haɗi da kansuloli a faɗin jihar Lagos, a ranar Asabar ɗin nan.
An tsara kaɗa ƙuri'a a cibiyoyin zaɓe 13,325 a mazaɓu 376 a jihar da ke zaman babbar cibiyar kasuwancin Najeriya.
Tun da farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (Lasiec), ta bayar da tabbacin cewa ta yi shirin da duk ya kamata domin zaɓen, kuma ta ce an inganta hanyoyin zuwa cibiyoyin zaɓen.
Kamar yadda aka gudanar da zaɓukan da aka yi na jihar da kuma na tarayya na bayan-bayan nan za a yi amfani da na'urar tantance mai kaɗa ƙuri'a ta hanyar tantance zanen yatsu ko kuma fuska, tare kuma da aikawa da sakamakon zaɓen kai tsaye daga cibiyoyin zaɓen.
Dangane da tsaro rundunar 'yansanda ta jihar ta sanar da taƙaita tafiye-tafiyen ababan hawa a duk faɗin jihar tun daga ƙarfe uku na dare zuwa ƙarfe uku na rana, a ranar Asabar ɗin.
Wa zai iya yin nasara a zaɓen?
Akwai jam'iyyu 19 a takardar zaɓen inda duk mutumin da yake da katin zaɓe na dindindin mai kyau zai zaɓi 'yantakara daga cikinsu.
Sakamakon zaɓukan baya tun daga shekara ta 2014 ya nuna cewa jam'iyya mai mulki a jihar ita ce take cinye kusan dukkanin kujerun da ake takara a kodayaushe na ƙananan hukumomin - kamar yadda wata ƙungiya mai rajin tabbatar da dimukuraɗiyya a Najeriya (EiE Nigeria), ta bayyana.
Tun daga shekarar 1999, jam'iyya ɗaya, ta siga daban-daban take gudanar da mulkin jihar Lagos kuma ita ke cinye dukkanin zaɓen ƙananan hukumomi da na jiha har ma da na tarayya a jihar
Jam'iyyar APC, ko kuma jam'iyyar da ta juye ta zama APC, bayan da ta riƙa canza sunanta (AD, AC, ACN kafin ta zama APC), kusan a kodayaushe ita ke mulkin jihar tun komawar ƙasar mulkin dimukuraɗiyya.
Jam'iyyar ta kawar da duk wata jam'iyyar hamayya a zaɓen jihar a shekara 20 da ta gabata.
Mutane sun fito zaɓen?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kusan a kodayaushe mutane ba sa fitowa zaɓe sosai a Najeriya. Kashi ɗaya bisa huɗu na yawan masu zaɓe ne kawai suka fita zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
Yawan ba ma ya kaiwa haka a zaɓukan ƙananan hukumomi da aka yi a baya a Najeriya.
Waɗanda suka fito kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi na ƙarshe a Lagos kusan kashi 11 ne kawai cikin ɗari, duk kuwa da cewa akwai sama da mutum miliyan 6.5 da suka cancanci zaɓe a cewar hukumomin jihar.
Yawanci ana danganta ƙin fita zaɓe da mutane ke yi da tsoron tashin hankali da akan samu a lokacin zaɓe da kuma bijirewa da jama'a kan yi saboda rashin cika alƙawarin 'yansiyasa a baya.
Wani dalilin kuma shi ne mutane ba sa ɗaukar zaɓen ƙananan hukumomi da muhimmanci idan aka kwatanta shi da zaɓen ƙasa - wanda hakan kan sa kafafen yaɗa labarai ma ba sa ba shi muhimmanci da kuma wayar da kan jama'a.
Shugaban hukumar zaɓen jihar Maisharia Bola Okikiolu-Ighile ritaya, ya ce za a sake zaɓe a duk inda aka samu matsalar satar akwati a lokacin zaɓen.
Mene ne muhimmancin zaɓen?
A matsayin ƙaramar hukuma na matakin gwamnati na uku, waɗanda suka ci zaɓen za su jagoranci shugabancin samar da abubuwan jin daɗin rayuwa ga jama'a a mataki mafi kusa da jama'a.
Gwamnatin ƙananan hukumomi ita ce ta fi kusanci da jama'ar da ake mulki a ƙasa.
Aikinsu ne su tabbatar da jin daɗi da walwalar jama'a a matakin farko ta hanyar samar da ilimin firamare da kula da lafiya a matakin farko da kula da kasuwanni da ƙananan tituna na cikin garuruwa ko karkara da tasoshin mota da tsaftar muhalli da gidaje da kuma kula da shara.
To amma a yanzu kusan gwamnatocin jihohi duk sun mayar da waɗannan ayyuka ƙarƙashinsu.
Hukumomin zaɓe na jihohi (Siecs), masu zaman kansu waɗanda jiha ke samawa kuɗi, su ke gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Najeriya, saɓanin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta tarayya (Inec) da ke gudanar da zaɓukan jihohi da na tarayya.
Wane iko ƙananan hukumomi suke da shi?
A shekarar da ta gabata Kotun Ƙoli ta zartar da hukuncin bai wa ƙananan hukumomi 'yancin cin gashin-kansu a ɓangaren kuɗi.
Wannan hukumcin ya dakatar da gwamnatocin jihohi daga karɓa da kuma riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi daga asusun tarayya.
Kotun ta umarci babban akanta na tarayya ya riƙa bai wa ƙananan hukumomi kuɗinsu kai tsaye.
To amma har yanzu bayan shekara ɗaya da wannan hukunci, gwamnonin jihohi na ci gaba da iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomin.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa tun bayan hukuncin kotun ƙolin a watan Yuli na bara - sama da naira tiriliyan 3.048 da aka ware wa ƙananan hukumomin na Najeriya 774 daga asusun tarayya an zuba kuɗin ne a asusun haɗin gwiwa na jiha da ƙananan hukumomi.
Katsalandan na siyasa da rashin samar da wadatattun kuɗi ga hukumomin zaɓe na jihohi (SIECs) da batun cin gashin-kai da rashin yin abu a bayyane da ƙauracewar masu zaɓe na daga cikin matsalolin da masu lura da al'maura suka gano na rage tasiri da gudanar da ayyukan ƙananan hukumomi yadda ya kamata.











