Yadda dogari maci-amana ya tona maɓoyar Saddam Hussein ga Amurka

.

Asalin hoton, Getty Images

'Mun kama shi. Wannan babbar rana ce a tarihin Iraƙi.'

A lokacin da Paul Bremer, babban jami'in diflomasiyyar Amurka a Iraƙi, ya sanar da kama tsohon shugaban Iraƙi Saddam Hussein, a wani taron manema labarai ranar 13 ga watan Disamban 2003, 'yan jarida da ke wurin sun yi masa tafi, yayin da wasu suka nuna ɓacin ransu ga batun.

Da aka ci gaba da matsa masa, sai ya miƙe tsaye yana furta wasu maganganu da ƙarfi.

Kama Saddam Hussein, ya nuna yadda aka samu bayanan sirri game da maɓoyarsa. Bayanan da suka yi wa dakarun Amurka jagora har zuwa inda yake ɓoye, wani wuri a ƙarƙashin ƙasa kusa da mahaifarsa, Tiktrit.

Kanal James Hickey, wani sojan Amurkan da ya jagoranci zugar da ta kai samamen kama Saddam Hussein, ya ce sojojin na shirin jefa gurneti cikin ramin da yake ɓoye, sai ya fito tare da miƙa kansa, a ranar wata Asabar.

Sojojin na Amurka sun samu bayanan sirri kan inda Saddam ke ɓoye ne daga wani mutum da aka kama a birnin Bagadaza, a ranar ta Asabar da misalin ƙarfe 11:15 na safe agogon ƙasar.

Wannan mutumin ba ɗan’uwa ne kawai ga Saddam ba, hasali ma yana cikin manyan makusantan Saddam.

Bayan samun bayanan sirrin da safe sai aka shirya yadda za a kama shi cikin dare.

A lokacin da dare ya fara kusantowa, wajen ƙarfe 6:00 na maraice, sai aka shirya rukunin sojoji kusan 600 na runduna ta huɗu ta sojin Amurka da ke ƙasar, domin yi wa ɓangarori biyu na yankin Al-Dawur da ke kusa da Tikrit, garin da aka haifi Saddam, ƙawanya.

Daga bayanan sirrin da aka samu, an yi ta yaɗa jita-jitar cewa Saddam Hussein yana laɓe ne a ɗaya daga cikin ɓangarori biyu na garin.

An shirya atisayen ne da nufin kamawa ko kashe Saddam Hussein, abin da ya sa aka shirya dakarun ɓangare biyu.

Waɗannan dakarun sun kai samame wuraren da ake zaton Saddam yana ɓoye da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

To amma ba su same shi a wuraren biyu ba. Daga nan ne suka rufe duka wuraren tare da tsayar da al'amura, kuma suka sake ƙaddamar da farautarsa a duka wuraren.

A lokacin ne, suka shiga wata ƙaramar gona da aka katange, da ƙarafa da yumɓu.

Maɓoyar ƙarƙashin ƙasa

..

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yayin da ake binciken wajen, sojojin sun gano wani ramin da ya yi kama da na 'sojin sari-ka-noƙe' a farkon wurin da aka rufe da bulo da kuma laka.

Haka kuma akwai wani kafet mai ƙura da aka yi amfani da shi wajen rufe ramin, ta yadda ma ba kowa ne zai fahimci ramin ba.

Kanal Hickey - wanda ya jagoranci samamen - ya ce sojojin sun yi duba na tsanaki kan ramin sai suka ga alamar inuwa a cikinsa. Daga nan sai hannayen wani mutum da ke cikin ramin suka bayyana da alamar miƙa wuya.

A lokacin da aka zaƙulo Saddam Hussein daga cikin ramin da misalin ƙarfe 10:36 na dare, an fito da shi a birkice, kamanninsa sun sauya, kamar yadda Manjo Janar Ray Odierno, kwamandan runduna da huɗu ya bayyana.

Duk da cewa akwai ƙaramar bindiga a wajensa lokacin da aka kama shi, amma bai nuna turjiya ba.

Manjo Brian Reed, jagoran runduna ta huɗun ya ce a lokacin da aka kama Saddam, ya yi magana da Turanci, inda ya shaida wa Sojoji cewa "Ni ne Saddam Hussein, ni ne shugaban ƙasar Iraƙi kuma ina son a daidaita.'

Daga nan ne dakarun Amurka na musamman suka mayar masa da martani da cewa "Shugaba Bush na yi maka fatan alkairi'', kamar yadda Manjo Bryan ya ce.

An kuma kama wasu mutum biyu da aka yi amanna cewa suna tare da Saddam domin yi musu tambayoyi.

"Bayanai game da ramin"

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ainihin cikin ramin ƙarƙashin ƙasan da aka kama Saddam Hussein

Ramin da tsohon shugaban Iraƙin ya ɓoye kansa na da zurfin ƙafa shida zuwa takwas, wanda ke da faɗin da zai ishi mutum guda ya kwanta.

Akwai hanyar da ke bai wa iska damar shiga ciki, sannan akwai fankar da ke ba shi iska a lokacin da iska ta daina kaɗawa.

Manjo Odierno ya ce gonar da ramin yake 'yar ƙarama ce, kuma akwai ɗakuna biyu a cikinta.

Ya ce a ɗaya daga cikin ɗakunan wuri ne da ake rataya tufafi, Tufafin sun haɗa da ƙananan riguna da safa, da wajen girki da famfon ruwa.

Ya ƙara da cewa a duk lokacin da dakarun Amurka suka je wannan yanki, sai Saddam ya fice daga ɗakin, ya koma ramin da ke cikin ƙarƙashin ƙasar domin ɓuya.

Ramin na kusa da kogin Tikrit, kuma daga nan ana iya hango wasu fadojin Saddam ɗin da ke garin Tikrit.

Manjo Janar Odierno, ya ce a maimakon zama a ɗaya daga cikin fadojinsa, ya gwammace ya zauna cikin ramin ƙarƙashin ƙasa a kusa da kogin.

'Bayanan ƙarshe'

...

Asalin hoton, Getty Images

Duk da cewa sojojin Amurka sun sha binciken yankin, ba su taɓa gano Saddam Hussein a wajen ba, saboda an ce yana yawan sauya maɓoya, daga lokaci zuwa lokaci.

Amma a lokacin da ake tuhumar ɗaya daga cikin 'yan’uwansa a Bagadaza, bayan kama shi, sojojin Amurkar sun samu 'cikakkun bayanan sirri' kan maɓoyarsa.

Manjo Janar Odierno ya ƙara da cewa ba a samu wayar hannu ko wasu hanyoyin sadarwa a wajen da Saddam ɗin ke ɓuya ba.

Babban kwamandan sojin Amurka da ke aiki a Iraƙi, Laftanar Janar Ricardo Sanchez, ya ce bayan kama shi, ''Saddam ya bayar da haɗin kai'' ba a ji masa ciwo ba, kuma ya kasance cikin ƙoshin lafiya a lokacin da ka kama shin.

Matakin ƙarshe

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayan Saddam, sojojin sun kuma samu kuɗi, dala miliyan bakwai da rabi, da kuma wasu dala dubu 100 a cikin ramin da suka kama shin.

An kuma samu bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, da wata ƙaramar jakar ajiye takardu a wurin.

An kuma samu wasu motocin tasi guda biyu fara da ruwan lemo a ajiye kusa da wurin.

Janar Sanchez ya ce bayan kama Saddam an kai shi wani wuri da ba a bayyana ba.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sadam Hussein

Mutane da dama sun yi mamakin inda aka samu moɓoyar Saddam.

Da farko masu sharhi na ganin cewa Saddam Hussien zai iya ɓuya a kusa da garin da ka haife shi, Tikrit, suna tunanin cewa magoya bayansa a garin za su iya ba shi kariya daga dakarun ƙawancen da ke farautarsa.

Amma an yi ta yaɗa jita-jitar ladan dala miliyan 25 da Amurka ta saka ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Saddam, ka iya taimakawa wajen wargaza biyayyar da makusantansa suke yi masa.

A shekarar 2004, wasu bayanan da BBC ta kwarmata na Panorama, sun nuna cewa wani ɗan’uwa kuma makusancin Saddam mai suna Muhammad Ibrahim Omar da ke cikin masu tsaron lafiyar Saddam ne ya bayar da bayanan sirrin da suka kai ga kama shi.

An kuma kira shi da wanda ya yi 'ɓatan-ɓaka-tantan'. Saboda ya bayar da rahoton maɓoyar ubangidan nasa a lokacin da sojoji ke tuhumarsa, a maimakon ya bayar da bayanan don raɗin kansa don samun ladan dala miliyan 25 da aka saka wa wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama shi.

Ankararwa: Wannan rahoto kan kama Saddam an haɗa shi ne da taimakon bayanan da BBC ta wallafa a rahotonninta na shekarun 2003 da 2004.