Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƴan jam'iyyar APC 8 suka sauya sheƙa a jihar Zamfara
A Najeriya jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar wata sabuwar rigima bayan da wasu 'yan majalisar dokokin jihar har takwas suka sanar da canza sheka daga jam'iyyar.
Yan majalisar sun bayyana matakin nasu ne a zaman majalisar dokokin jihar da aka gudanar a birnin Gusau, inda aka karanta wasiƙun murabus ɗinsu a hukumance.
Waɗanda suka sanar da ficewar tasu sun fito ne daga mazaɓu daban-daban na jihar, ciki har da Bakura da Talata Mafara ta Kudu da Maradun ta Ɗaya da Gummi ta Ɗaya da Kaura Namoda da sauran su.
Matakin da jam'iyyar ta APC ta ce duk da ba ta ji dadinsa ba.
A cikin wasikun sauya sheka da suka aike, yan majalisar sun ce sun dauki wannan matsayi ne bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki a mazabunsu.
Sun danganta matakin da abinda suka kira rashin hadin kai tsakanin shugabannin jamiyyar a jihar da kuma zargin rashin adalci da yaudara a harkokin siyasa.
Sun kuma nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al'amuran tsaro a wasu yankunan da ke fama da hare haren 'yan bindiga.
Onarable Ibrahim Tukur, daya daga cikin yan majalisar dokokin jihar Zamfara da suka fice daga jam'iyyar ta APC ya shaidawa cewa sun yi laakari da wasu abubuwa kafin suka yanke wannan shekra
''Mun yi kusan wata talati da biyu ana wannan hobbassa da mu kan abinda da ya shafi alummarmu, ba ma tsaron kadai, hatta tallafi da mu ke zaton za'a ba mu.Ana kashe mata sannan yara suna gararramba kuma ba bu wani mataki wanda jiha ta dauka domin kare rayuwar wadannan alumma'' in ji shi.
Omarbale Tuku ya ce har yazu basu koma wata jam'iyya ba , amma ya ce kusan dukkanin 'jam'iyyun adawa na zawarcinsu
''Mu takwas muka fice, biyar sun fito daga yankin Zamfara ta yamma, sannan akwai wanda suka fito daga Zamfara ta tsakiya da kuma Bungudu'' in ji shi.
Sai dai Mustapha Jafaru Kaura mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara kuma bangaren jam'iyyar APC ta jihar Zamfara ya shaidawa BBC cewa dalilan da 'yan majalisar da suka sauya sheka suka bayar, cike su ke da kura-kurai:
''Ina son na fadawa jama'a cewa su wadannan yan majalisa , yan majalisar dokokin jihar Zamafara ne da aka dakatar kuma dalilan da suka zayyana na ba bu jagoranci na kwarai wannan labari ne na ga yawa sarki gaya suke yi saboda in ba bu jagoranci na kwarai da basu zamo yan majalisu a shekarar 2023 ba''
Masana dai na kallon wannan mataki a matsayin wani babban sauyi da zai iya yin tasiri ga siyasar jihar Zamfara a zaben shekarar 2026