Tudun Biri - 'Raina yana ɓaci idan na ga raunin ƴata'

Wata yarinya na zubar da hawaye

Asalin hoton, Gift Ufuoma / BBC

Lokacin karatu: Minti 7

Bayan shekara ɗaya da rasuwar 'yarsa mai shekara bakwai a harin jirgi maras matuƙi na sojojin Najeriya lokacin bikin Mauludi a ƙauyensu na Tudun Biri, har yanzu Mallam Mas'ud Abdulrasheed yana alhinin wannan rashi da irin bala'in da suka gani a lokacin.

A lokacin dai sojoji sun ce sun yi kuskure ne na tattara bayanan tsaro na sirri inda suka ɗauka cewa taron Maulidin da ake yi taro ne na 'yan ta'adda, masu iƙirarin jihadi.

Abin da ya faru ranar 3 ga watan Disamba na 2023, babban abin alhini ne wanda bai kamata ya faru ba," in ji kakakin sojin Najeriya Manjo-Janar Edward Buba a tattaunawarsa da BBC.

"Sojoji sun yi nadamar wannan lamari. Kuma idan da za mu iya dawo da rayukan da aka rasa da mun yi."

Gargaɗi: Wannan labarin yana ɗauke da wasu bayanai da za su iya tayar da hankali

Kusan mutum 85 aka kashe ciki har da 'yar Mallam Abdulrasheed Habiba, lokacin da jirage marassa matuƙa suka jefa bam-bamai biyu a ƙauyen na Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a arewacin jihar Kaduna.

Mallam Abdulrasheed ya ce: ''An jefa bam na farko ne da misalin ƙarfe 10 na dare, a kusa da wata bishiya inda mata da yara suke zaune. Daga nan muka kama gudu domin tsira, to amma bayan wani ɗan lokaci da muka taru domin taimaka wa waɗanda sua ji rauni da neman taimako, sai aka saki bam na biyu wanda ya kashe wasu ƙarin mutanen."

Mallam Abdulrasheed ya bayyana wannan 'ya tashi a matsayin wadda ta fi nuna masa so a duk cikin 'ya'yansa".

"Duk abin da aka ba ta sai ta ba ni, ko da ba na buƙata," ya gaya wa BBC.

Malamin mai shekara 36, yana daga cikin waɗanda suka shirya taron Maulidin na Annabi Muhammad (SAW), kuma ɗalibansa da dama na daga cikin waɗanda suka mutu a harin.

Mun ga gawawwaki warwatse a ko'ina sai ka ce bacci suke yi. Ga sassan jiki nan warwatse, a kan bishiyoyi ne da rufin gine-gine. Sai tattara su muka yi a buhuna muka binne su a babban kabari na bai-ɗaya.

''Ba abin da yake da tashin hankali kamar ka ga mutanen da ka gayyata taro su rasu a wajen. Na ji takaici tare da alhinin wannan abu,'' in ji malamin.

A lokacin da yake yi wa BBC wannan bayani 'yarsa ta biyu, Zahara'u na zaune kusa da shi a kan tabarma a ƙofar gidansu. Ya ɗaga rigarta ya nuna wani ciwo a cikinta.

Mallama Mas'ud Abdulrasheed zaune da 'yarsa Zaharau tana nuna rauninta

Asalin hoton, Gift Ufuoma / BBC

Bayanan hoto, Masud Abdulrasheed ya ce an daina kula da 'yar tasa kyauta a asibiti
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tarkacen bam ɗin da aka jefa ne ya ji wa yarinyar mai shekara huɗu rauni. An ɗauki aƙalla sa'a ɗaya kafin a kai yarinyar da sauran waɗanda suka ji rauni asibiti a Kaduna.

Duk da cewa an yi mata aiki a asibiti har yanzu ba ta warke ba gaba ɗaya.

''An kula da ita sosai da sauran waɗanda suka ji rauni a asibitin. Mun gode wa gwamnati a kan hakan.

To amma al'amura sun sauya bayan da aka sallame su daga asibitin, bayan watanni. Asibitin ya ƙi ci gaba da yi musu magani kyauta. Sai uzuri suke ba mu.'' In ji mahaifin yarinyar.

Idan ka kewaya wannan gari da wuya da ka samu gida ɗaya da wannan lamari bai shafa ba.

A'isha Buhari, mai shekara ashirin ta rasa ƙannenta maza uku. Ta tsira daga wannan hari amma har yanzu raunin da ta ji a hannunta na hagu bai warke ba.

A lokacin da BBC ke tattaunawa da ita, tana zaune a kan kujera, tana kuka ta sanya hijabinta tana share hawaye, yayin da take tuna yadda ta rasa 'yan uwan nata uku.

Ta ce a wannan lokaci ta gama magana da su kenan aka jefa bam na farko, daga nan sai gawawwakinsu kawai ta gani.

''Lokacin da aka garzaya da ni asibiti ba abin da nake tunani sai su. Na yi kuka sosai.'' In ji ta.

Yayin da A'isha ke bayani takan tsaya ta share ruwan da ke fitowa a ciwon nata.

''Ba wani aiki na gida ko na gona da ba zan iya ba kafin wannan abu, to amma yanzu ba na iya komai sosai. Yanzu sai dai a yi min wasu abubuwan, kamar wanki,'' a cewarta.

Hoton Aisha Buhari

Asalin hoton, Gift Ufuoma / BBC

Bayanan hoto, Aisha Buhari ta rasa ƙannenta maza uku a harin bam ɗin

Gwamman jihar Kaduna, Uba Sani ya gaya wa BBC cewa zai duba halin da waɗannan mutanen ƙauyen na Tudun Biri suke ciki - irin su Aisha Buhari.

''Na gode muku BBC a kan wannan bayani. Ni da kaina zan koma Tundun Biri, kuma idan na samu mutanen da ke ɓukatar magani har yanzu, zan tabbatar da an yi musu magani,'' ya yi alƙawari.

Ya ƙara da cewa : ''Umarnin da na bayar shi ne duk wanda ya ji rauni za a yi masa magani kyauta har sai ya warke gaba ɗaya.''

Abin da ya faru a bara bai hana al'ummar wannan ƙauye na Tudun Biri sake taronsu na Maulidin ba a bana, sai dai a wannan karon sun yi taron ne wata biyu kafin zagayowar lokacin da aka kai musu harin.

Haka kuma an yi taron ne tare da buɗe sabon masallacin da hukumomi suka gina musu a daidai wajen da aka jefa musu bam ɗin a matsayin wata diyya.

Mallam Abdulrasheed shi ne limamin masallacin yanzu kasancewar, ainahin limamin ya mutu a wannan harin.

Ya gaya wa BBC cewa: ''Muna farin ciki da masallacin, amma fa ba za mu iya taɓa mantawa da abin da ya faru ba. A duk lokacin da na zo nan, sai na tuna wannan rana. Sai na ji jikina ya yi sanyi. Ko da muka yi taron Maulidi na bana sai da muka yi makokin waɗanda suka rasu.

Tsawon shekaru sojojin Najeriya na fama da yaƙi da masu iƙirarin jihadi da sauran miyagu, da ke addabar ƙauyuka su sace mutane domin karɓar kuɗin fansa a sassan arewacin ƙasar ta Najeriya.

Wannan ya sa aka samu ƙaruwar hare-hare ta sama da sojojin ke kaiwa da nufin hallaka miyagun.

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sayi sababbin jiragen sama, da suka haɗa da jiragen sama marassa matuƙa na yaƙi, kamar yadda editan jaridar intanet ta ma'aikatar tsaro ta Najeriya - Defence Web, wato Guy Martin, ya gaya wa BBC.

Jiragen saman marassa matuƙa masu araha yawanci an saye su ne dagaChina, kamar yadda yawancin ƙasashen Afirka ke sayensu daga China da Turkiyya.

Mista Martin ya ce, ''To an kai wannan harin ne da irin waɗannan jirage marassa matuƙa.''

Editan ya ce, kuskuren da ake samu a kan gazawar samun bayanan sirri na tsaro da rashin tsari na bai ɗaya da rashin samun cikakken horo kan amfani da jiragen, na daga cikin abubuwan da ke haddasa irin wannan kuskure.

Manjo Janar Buba ya gaya wa BBC cewa sojojin Najeriya sun samu kansu a wani yanayi mai wuyar gaske. Amma ya ce a yanzu sun samu cigaba wajen sarrafa makamai da kuma tura ƙwararrun kwamandoji da dakaru aiki.

Wani kamfanin harkokin bayanan tsaro na sirri, SBM, ya ce rundunar sojin saman ƙasar ta kai hare-hare ta sama na kuskure 17, a tsakanin watan Janairu na 2017 da Satumba na 2024, inda suka kashe sama da mutum 500.

Masud Abdulrasheed ne yake zaune a wajen sabon masallacin da aka gina a ƙauyen

Asalin hoton, Gift Ufuoma / BBC

Bayanan hoto, Masud Abdulrasheed ne sabon limamin masallacin bayan kashe tsohon limamin a harin

Mai bincike na ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'Adam ta Human Rights Watch (HRW), a Najeriya, Anietie Ewang ya nuna cewa, wannan kuskure ne da sojin Najeriya ke ta yi.

Sai dai Manjo Janar Buba cewa ya yi kamata ya yi ƙungyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam su yaba musu kan yadda suke fito wa su faɗi gaskiya kan abu idan ya faru, kamar yadda ya ce sun yi game da na Tudun Biri.

Ya ce akwai sojoji biyu da yanzu aka gurfanar da su a gaban kotun soji kan harin na Tudun Buri.

Haka kuma gwamnatin tarayya da ta jihar suna yin wasu ayyukan raya ƙasa a garin domin rage wa al'ummar raɗaɗin wannan rashi na 'yan uwansu, inda gwamnan jihar ya gaya wa BBC cewa an kusa kammala ginin asibiti da cibiyar koyar da sana'o'i da ake yi musu.

To amma kuma wani abin takaici shi ne sama da mutum 20 na kokawa da cewa an ƙwace musu filayen da suka dogara da su na noma don waɗannan ayyuka kuma ba a ba su diyya ba.

Dangane da wannan gwamnan ya ce, hukuma za ta duba ta ga waɗanda suka mallaki filayen a ƙa'ida a mayar musu.

Shi ma mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya ziyarci ƙauyen sakamakon harin inda ya yi alƙawarin gwamnatin tarayya tare da gwamnatin jihar za su ba wa mutanen diyya ta kuɗi da kuma tabbatar musu da adalci.

An yi musu alƙawarin naira miliyan 2.5 a kan duk mutum ɗaya da aka kashe, yayin da masu rauni za a ba wa kowa naira 750,000.

A kan haka aka ba wa iyayen A'isha Buhari naira miliyan 7.5, ita kuma ta samu naira 750,00.

Aisha Buhari zaune da ciwonta na ruwa

Asalin hoton, Gift Ufuoma / BBC

Bayanan hoto, Aisha Buhari ba ta iya amfani da hannunta na hagu sosai tun bayan da ta ji rauni a harin

A'isha ta ce da wannan kuɗin ne take zuwa kemis tana sayen magani ana kuma sa mata bandeji a ciwon, saboda iya abin da za ta iya yi kenan.

Ta ce tana fatan gwamnati za ta sake waiwayo su ta san ahalin da suke ciki ta shiga lamarin saboda asibiti sun daina yi musu magana.

Shi kuwa Mallam Abdulrasheed ya ce ba a ba shi wani kuɗi ba a kan raunin da 'yarsa mai shekara huɗu ta ji ba - ''duk lokacin da na ganta sai na damu,'' in ji shi.

Amma ya ce an ba shi diyyar ɗaya 'yar tasa mai shekara bakwai da ta rasu, to amma fa ba wani kuɗi da zai iya maye gurbinta.

''Duk lokacin da na ziyarci kabarinta , sai na tuna waɗanda muke zama tare, waɗanda yanzu babu su. Na rasa su gaba ɗaya. Ina kewarsu. Ina kewar 'yata.''

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo