An kashe sojojin Nijar 45 a hare-haren 'yan bindiga tun bayan juyin mulki

Sojoji

Asalin hoton, getty

Sojojin Nijar 45 zuwa yanzu aka kashe a hare-haren masu iƙirarin jihadi, tun bayan juyin mulkin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka yi a ƙarshen watan Yuli.

Hari na baya-bayan nan shi ne wanda 'yan ta-da-ƙayar-baya suka yi wa wata zugar sojoji kwanton-ɓauna ranar Talatar nan, inda suka kashe soja 17 a kusa da garin Koutougou na jihar Tillaberi.

Lamarin, wata manuniya ce ta tsananin taɓarɓarewar tsaro da ƙasar ke fama da shi daidai lokacin da sojoji masu mulkin Nijar ke fuskantar rikici da ƙasashe maƙwabta, waɗanda suka dage sai sun kawar da juyin mulkin watan jiya.

Sojojin da suka hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed daga mulki sun kafa hujjar juyin mulki ne a kan taɓarɓarewar tsaron da suka ce Nijar na fama da shi, sai dai rahotanni na cewa ba a taɓa samun yawan ƙazancewar hare-hare kamar yanzu ba a lokacinsa.

Sanarwar da rundunar sojin Nijar ta fitar na cewa wata zugar sojoji ce ta gamu da kwanton ɓaunan 'yan ta'adda a wani yanki da ke kusa da ƙasar Burkina Faso.

Ta ƙara da cewa, yayin harin an kuma raunata soja 20, shida cikinsu sun ji munanan raunuka, amma tuni aka kwashe su zuwa asibiti a Niamey babban birnin ƙasar.

Rundunar ta kuma ce an kashe su ma maharan fiye da 100 da ke tafe a kan babura.

Rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi ya tagayyara yankin Sahel na Afirka tsawon sama da shekara goma, bayan ɓarkewarsa a arewacin Mali a 2012 kafin bazuwarsa zuwa maƙwabtan ƙasashen Nijar da Burkina Faso a 2015.

Yankin da ake kira "kan iyaka uku" da ke tsakanin ƙasashen uku, a kai a kai yana fama da hare-hare daga 'yan tawaye masu alaƙa da ƙungiyoyin IS da Al-Qaeda.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahotanni na nuna cewa harkokin tsaro sun ƙara taɓarɓarewa a Nijar, musamman a yankunan da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga masu iƙirarin jihadi, mako uku bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Shafin LSI-Africa, da ke birnin Paris na Faransa ya ruwaito cewa tun bayan da sojojin suka yi juyin mulki alamu sun nuna cewa an janye dakarun ƙasar da ke fagen daga a yankuna daban-daban.

Matakin dai, ƙila ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin da sojojin ke yi na tattara ƙarfinsu wajen kare babban birnin ƙasar Yamai, domin kawar da duk wata barazana ta ƙin amincewa da sauyin gwamnatin.

Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO ta yi barazanar ɗaukar matakin soji domin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar, idan har sojojin ba su mayar da shi cikin lumana ba.

Ana ganin wannan mataki na ƙungiyar ƙasashen maƙwabta, wanda ya haifar da zaman ɗar-ɗar, da kallon hadarin-kaji tsakanin sojin da suka karɓe mulki da ƙungiyar, ya sa sojojin janye dakarun daga fagen daga domin haɗa ƙarfinsu a babban birnin don kare mulkinsu.

Bayanai sun nuna cewa a dalilin rashin dakarun su kuma mayaƙa masu tayar da ƙayar baya suka samu damar kai ƙarin hare-hare a yankunan.

Tsawon shekara da shekaru dakarun Nijar na fama da mayaƙa masu tayar da ƙayar baya da ke iƙirarin jihadi a yankin Tafkin Chadi na kudu maso gabashin ƙasar da kuma yankin da ya ƙunshi iyakokin ƙasashen Mali da Burkina Faso da ke yamma.

Ba a ga yawan hare-hare irin na yanzu ba lokacin Bazoum

A yankin Tillabery da ke yammacin ƙasar ta Nijar, mayaƙa masu iƙirarin jihadi sun kai hare-hare aƙalla guda shida tun bayan juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli, inda rahotanni suka ce sun kashe sojoji 28.

Waɗannan hare-hare sun shafi garuruwn Goulbal da Wabila da Hondobon da Katanga da Samira, da kuma Sanam.

Sai dai rahoton ya ce babu cikakken bayani a kan harin Sanam, abin da ya sa ake ganin yawan sojin da masu iƙirarin jihadin suka kashe na iya ƙaruwa.

Shafin da ya ruwaito labarin ya ce tun bayan zaɓen Mohamed Bazoum, masu iƙirarin jihadi ba su taba kai wa Nijar hare-hare da yawa cikin taƙaitaccen lokaci irin wannan ba.

Alƙaluma sun nuna cewa hare-haren da aka kai a ƙasar a dan wannan tsakanin sun ninka waɗanda aka kai a lokacin mulkin Bazoum biyu.

Ƙungiyar IS ta lardin Sahel, ita ce ta fi karfi da tasiri a cikin masu tayar da kayar baya da sunan jihadi a yammacin Nijar.

Bayan wannan kungiyar akwai kuma Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda take da alaka da al-Qaeda, wadda ita ma ana ganin tana kai hare-hare a wannan yanki

Haka can ma a gabashin ƙasar ƙungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad, wadda ake wa laƙabi da Boko Haram, bayanai sun ce ta ƙara ƙarfi tun bayan juyin mulkin.

A sanadiyyar janye sojojin daga fagen daga domin su je su kare masu juyin mulkin, ‘yan ƙungiyar sun samu damar karƙar maƙudan kuɗae daga mazauna garuruwan da suke, in ji kafar yada labaran.

Shafin ya ruwaito cewa, bayanin da ya samu ya nuna cewa mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun karɓi kuɗin da ya kai dalar Amurka 13,320 a Turban, yayin da a ƙauyen Morey suka kari abin da ya kai dala 6,700, sai dala 10,000 a Madouri da kuma dala 8,300 a Kargamdi.

Can a garin Gagamari, mayaƙan na Boko Haram sun nemi a ba su kuɗin da ya kai dalar Amurka 83,000, yayin da hukumar wajen ta ce dala 10000 za ta bayar.

Mayaƙan sun ƙi amincewa da wannan ragi, kamar yadda suka ƙi yarda da dala 8300 da al’ummar garin Chetimari suka ce za su biya.”

Shafin labaran ya ce, masu tayar da ƙayar bayan sun yi amfani da wannan dama inda ko dai suka sace ko kwashe ko kuma lalata motoci da makamai da harsasai da yawa a waɗannan yankuna.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Birgediya Janar Abdourahmane Tchiani, ya ce sun hamɓarar da gwamnatin Bazoum ne saboda abin da ya kira taɓarɓarewar tsaro.

Sai dai shafin labaran na intanet na LSI-Africa, ya nuna wasu alƙaluma na hukumomin Nijar din game da hare-hare, waɗanda ke nuna cewa an samu raguwar yawan farar hula da hare-haren ke rutsawa da su da kashi 60 cikin ɗari a 2022 sannan an samu raguwar da kashi 69 cikin ɗari a 2023, idan aka kwatanta da shekarar 2021.