Hotunan yadda kungiyar NLC ke gudanar da zanga-zanga a Najeriya
Kungiyar kwadago ta Najeriya ta soma gudanar da zanga-zanga a fadin kasar domin tilasta wa gwamnatin kasar biyan bukatun kungiyar Malaman Jami'o'i ta ASUU.
Hakan na faruwa ne a yayin da aka shiga wata na shida da soma yajin aikin Malaman Jami'o'in sakamakon abin da suka kira kin da Gwamnatin Tarayya ta yi na mutunta yarjejeniyar da suka kulla game da inganta tsarin karatunsu - da suka hada da samar da karin kayan aiki da inganta albashi da alawus-alwasu na Malaman Jami'ar.
Ga wasu hotunan yadda kungiyar ta NLC take gudanar da zanga-zanga:












