Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Putin ya fusata Trump da hare-haren Ukraine
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai ji dadin abin da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ke aikatawa ba, bayan manyan hare-haren da Rasha ke kai wa Ukraine har yanzu.
Cikin jawabin da ya yi da bacin rai ya ce abin da Putin ke aikatawa sam ba dai-dai ba ne kuma rashin hankali ne.
Tun da farko shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce shirun da Amurka ta yi a kan hare haren baya-bayanann da Rasha ta kai wa kamar karfafawa Putin gwiwa ta ke yi.
Zelensky ya bukaci da a kara matsawa Rasha lamba kan ta daina abin da take yi tare da sanya mata takunkumai ma su zafi.
Akalla mutum 12 aka kashe, yayin da aka jikkata wasu gwammai a Ukraine a wasu hare-hare da Rashan ta kai da jirage marassa matuka da makamai masu linzami cikin dare.
Wadannan na cikin hare-hare mafi muni da Rashan ta kai a cikin dare guda.
A safiyar Litinnin ma anji karar gargadi a kan hare-haren da ke tafe a yawancin yankunan Ukraine.
Akalla mutum uku aka raunata ciki har da wani yaro a arewa maso gabashin birnin Kharkiv a cewar magajin yankin.
Da ya ke Magana da manema labarai a New Jersey a daren jiya Lahadi, shugaba Trump ya ce;
"Ya na kashe mutane da dama, ban san irin abin da ke faruwa ba da Putin, yana aikata hari da makaman roka a birane da dama sanann yana kashe mutane, gaskiya ba na jin dadin abin da yake yi sam-sam."
Koda aka tambayeshi ko yana duba yiwuwar karawa Rasha takunkumai, sai Trump ya ce ko shakka babu.
Dama shugaban ya sha nanata daukar matakin hakan to amma bai yi ba.
Shugaban na Amurka ya kuma soki shugaban Ukraine, inda ya ce ba ya yi wa kasarsa adalci, bisa la'akari da abin ke faruwa a Ukrane.
Ya ce "duk wani abu da zai fito daga bakinka na janyo wa kasar matsala bana son haka gaskiya kuma gara ka daina".
Duk da cewa kawayen Ukraine na shirn kara kakabawa Rasha takunkumai, Amurka ta ce ko ta ci gaba da kokarin ganin an tattauna domin samun zaman lafiya a Ukraine ko kuma ta yi gaba abin da idan har babu wani ci gaba da ya biyo baya.