Matar da ta tsira daga harin nukiliya na Hiroshima da ke fafutikar neman zaman lafiya

Asalin hoton, Setsuko Thurlow
Setsuko Thurlow na da shekara 13 a lokacin da ta tsira daga harin bam na nukiliya da aka kai wa jamaa da dama, wanda hakan ya sa ta kasance mai tsayin daka wajen yaƙin kawar da duk wani irin makami na nukiliya a sama da shekaru 60.
Tana ɗaya daga cikin mutane ƙalilan da suka tsira daga harin bam ɗin nukiliya a birnin Hiroshima na ƙasar Japan.
Yanzu tana da shekaru 92, kuma tana cigaba da jajircewa wajen yaƙar kawar da makaman nukiliya musamman yadda kudaden da ake kashewa a duniya kan makaman ke karuwa sosai.
Har yanzu tana tuna lokacin da harin bam ɗin ya tashi da mutane.
“Na ga hasken tashin bam ɗin, amma kafin na ankara na fahimci wane irin haske ne, kawai jin kai na nayi a iska ina yawo, bam din ya tashi da ni, nan take na sume” Setsuko ta shaida wa BBC.

Asalin hoton, History / Getty Images
A ranar 6 ga watan Agustan 1945 da misalin ƙarfe 8 na safe ne Amurka ta harba bam ɗin nukiliya a birnin Hiroshima. Wannan shi ne bam ɗin nukiliya na farko da aka yi amfani da shi a yaƙi.
“A lokacin da na farfaɗo, ganin kai na na yi a cikin duhu, kuma ko'ina shiru.” Setsuk ta ƙara da cewa.
Ƙaruwar makamai
Setsk ta shafe mafi yawan shekarunta tana yaƙin a kawar da makaman nukiliya.
Ita ce jagora a yaƙin duniya na kawar da makaman nukiliya da ake yi wa laƙabi da can.
Alkaluman Ican sun nuna cewa a cikin shekaru biyar da wallafa rahotonta, kudin da ake kashewa a duk shekara kan makaman nukiliya ya karu da kashi 34 ko kuma dala biliyan 23.2
Rahoton ya kara da cewa a yanzu akwai kasashe tara da suka mallaki makaman nukiliya. Su ne:Rasha, Amurka, China, Faransa, Birtaniya, Pakistan, Indiya, Isra'ila, Koriya ta Arewa.
Ana kyautata zaton Isra'ila na da makamin nukiliya amma gwamnatinta na cigaba da musantawa.
Ican ta ruwaito a shekarar 2023 cewa kasashen da suka mallaki makaman nukiliya na kashe kusan dala 2,898 a duk dakika kan makaman nukiliya. - kaso 13.4 sama da shekarar da ta gabata.
Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Duniya ta Stockholm (Sipri) ta ce dukkan kasashen 9 da suka mallaki makaman nukiliya na ci gaba da sauna makaman a shekarar 2023.
Kashe mutane da dama
Sojojin Amurka sun jefa bam na nukiliya da ya kashe mutane da dama ta hanyar saukar lema, inda ya fashe mita 600 daga kasa.
Babu wani takamaiman alkaluman da ke nuna adadin mutanen da suka mutu a harin bam din, amma an kiyasta harin ya kashe mutane tsakanin 60,000 da 80,000 nan take.
"Na yi kokarin motsa jikina, amma na kasa, kawai sai na ji hannu a kan bayana da muryar namiji yana ce min kada na karaya, na ci gaba da jajircewa" a cewar Setsuk.
Ta kasa ganin mutumin da ya mata magana amma kuma ta bi shawararsa.
Ta ce ta ji kukan abokananta sun cewa "Ya Allah ya taimake mu, mama ki taimaka mana"
"Nan take sai ginin ya kama da wuta, mutanen da ke cikin dakin duk sun kone har suka mutu"

Asalin hoton, Getty Images
‘Waɗanda suka ƙone sun zama tamkar fatalwa’
Mata 30 da ke wa rundunar sojin Japanese aiki na cikin dakin da ya kone, dukan su yan aji daya ne da aka zama domin su dinga taimakawa da bayannan sirrin da ake samu.
Setsuko da wasu mutum biyu ne kadai suka rayu daga harin.
"Na ga mutane da dama sun kone kurmus sun koma tamkar fataluwa"
A cikin watanni da shekarun da suka gabata, mutane da dama sun mutu bayan dagon jinya daga hari.
Daga karshe,an lissafa adadin mutanen da suka mutu ya zama 135,000.
Nagasaki
A ranar 9 ga watan Agustan 1945, Amurka ta sake jefa bam na nukiliya ta biyu a birnin Nagasaki da ke Japan inda harin ya kashe kusan mutum 50,000 a yadda aka kiyasata.
Ƙuriciyarta
Babu abin da Setsuko za ta iya kwatantawa da shi kan abubuwan da ta fuskanta amma duk da haka ta ci gaba da gudanar da rayuwarta ta yadda ya kamata.
Ranar farko ta aiki
Bayan samun horarwa na Dan kankanin lokaci, matan sun fara aiki a ranar 6 ga watan Agusta.
Da karfe 8 na.safe suke tafiya wajen aikinsu, waje ne da sojoji ke amfani da shi a matsayin hedikwatarsu.
Setsuko da iyayenta ne kawao suka tsira daga harin amma sauran yanuwanta mata sun sami rauni sosai inda daga bisani suka rasu.
Japan ta mika wuya kwanaki 27 bayan hakan.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan yaƙi
Bayan yakin, Setsuko ta shiga kungiyoyi Kiristoci na duniya da dama domin aiki wajen kawo sauyi a Japan. Ta hanyar haka ne ta hadu da Jim Thurlow, Dan Canada, wanda daga baya ya zama mijinta.
A shekarar 1954, lokacin da take da shekara 20 zuwa 25, ta samu damar yin karatu a jami'ar Virginia na Amurka inda za ta karanci Sociology.
Amma kuma tattaunawarta da wata jaridar cikin gida ya canza mata ra'ayi.
Fara yaƙin kawar da makaman nukiliya
A shekarar 1952, Amurka ta gwada bam ɗin hydrogen na farko a duniya, wanda yake da ƙarfin yin ɓarna sau dubu fiye da bam ɗin nukiliyar da Setsuko ta fuskanta lokacin da aka jefa shi a Hiroshima.
“Waɗannan hare-hare da makaman nukiliya sun isa haka, Setsuko ta tsawatar yayion tattaunawarta da gidan jaridu, kar da abun da ya faru a Hioshima da Nagasaki ya sake faruwa.” - gargaɗi ga duniya da cewa irin waɗannan hare-haren za su sake faruwa.
Ta yi suka ga manufofin nukiliyar Amurka. Nan take aka yi mata martani kuma ta samu barazana da wasiƙun ƙiyayya wanda ya tsorata.

Asalin hoton, Getty Images
'Ba a banza ba'
Babu mai ƙarfafa min gwiwa kan wannan abin da muke son cimma na kawar da makaman nukiliya, amma mun ji a jikinmu cewa ya kamata mu jawo hankalin duniya kan wannan lamari, wannan shine babban burin mu.
Saboda hakane Setsuko ta yi tafiya zuwa ƙasashen duniya da dama ta sanar da labarinta da niyyar jawo hankalin mutane kan mummunar ɓarnar da makaman nukiliya ke haifarwa.
Tarin nukiliyar duniya ya kai kololuwar makamai sama da 70,000 a cikin shekarun 1980, bisa kididdigar da Tarayyar Masanan Amurka ta yi.
Tattaunawar rage makamai ta fara ne a ƙarshen 1980 kuma ta haifar da raguwar yawan makaman nukiliya da aka adana a duniya. Amma kuma yanzu ana samun ci baya kan wannan lamarin.

Asalin hoton, Anadolu / Getty Images
Kyautar Nobel ta zaman lafiya
Duk da haka, kamfen ɗin kawar da makaman nukiliya na cigaba da samun nasara.
A ranar 7 ga Yuli 2017, ƙasashe 122 sun kada kuri'a don amincewa da yarjejeniyar kasashen duniya kan haramta makaman nukiliya. Ƙasashen da ke da makaman nukiliya na cikin wadanda suka ki sanya hannu.
A ƙarshen shekara, Ican ta sami lambar yabo ta Nobel kan yaƙin neman zaman lafiya inda aka gayyaci Setsuko don karɓar kyautar a Oslo.
Setsuko ta yi imanin cewa ana buƙatar ƙarin ƙoƙari don samun amincewar duniya gaba ɗaya wajen kawar da makaman nukiliya.










