Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mojtaba Khamenei: Daga shekaru a bayan fage zuwa zama jagoran addinin Iran
- Marubuci, Amir Azimi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
- Lokacin karatu: Minti 4
Ana tsaka da shirye-shirye ne a tashar talabijin ta gwamnatin Iran sai aka dakata, inda aka ce akwai sanarwa mai matuƙar muhimmanci.
A lokacin ne mai gabatar da shirye-shiryen ya tabbatar da naɗa Mojtaba Khamenei, ɗan tsohon jagoran addinin Iran Ali Khamenei a matsayin sabon Ayatollahi na ƙasar.
An fitar da sabon jagoran addinin ne kimanin kwana takwas bayan an kashe Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila a Iran, wanda aka fara a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Kisan tsohon jagoran addinin ya matuƙar girgiza ƙasar Iran, wadda ta koma Jamhuriyar Musulunci bayan juyin-juya-halin shekarar 1979.
An gudanar da zaɓen sabon jagora addinin ne a cikin sirri, matakin da majalisar shura mai mutum 88 ta ɗauka.
Daga aiki a bayan fage zuwa shugabanci
Ba a san Mojtaba ba sosai, amma yanzu shekarunsa 56, kuma bai taɓa riƙe muƙamin gwamnati ba a hukumance a ƙasar.
Ya yi karatun nazarin addini ne a Qom, wanda birni ne mai muhimmanci a wajen masu aƙidar Shi'a. Ya daɗe yana karantar da addini, wanda hakan na cikin kama hanyar zama jagoran addini a ƙasar.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa a bara ya rufe ajujuwan da ake karatun addinin ba tare da cikakken bayani ba, lamarin da wasu ke cewa ba ya rasa nasaba da umarnin mahaifinsa wanda ba ya so a ga tamkar yana ƙoƙarin gadonsa ne.
Ali Khamenei bai cika so yana shigar da ƴaƴansa cikin harkokin gwamnati da na addini ba, saboda bai cika so ana alaƙanta gwamnati da gado ba, musamman bayan sun jagoranci kifar da gwamnatin sarauta ta Pahlavi a juyin-juya-halin 1979.
Sai dai ana ganin Mojtaba na shiga ana damawa da shi a harkokin mulkin ƙasar ta bayan fage. Wasu masana suna ganin yana taka rawa wajen rawar gani kuma yana da ƙarfin faɗa a ji a siyasar Iran.
Yadda yake shiga harkokin siyasar ƙasar ya ƙara fitowa fili ne a babban zaɓen ƙasar na 2005, wanda Mahmoud Ahmadinejad ya samu nasara. Ƴan ƙasar da dama suna tunani goyon bayan Mojtaba ya taka rawa wajen samun nasarar Ahmadinejad a zaɓen.
An aiwatar da zanga-zanga a ƙasar bayan Ahmadinejad ya samu nasara a karo na biyu a zaɓen 2009, inda ƴan hamayya ciki har da Mir-Hossein Mousavi suka ƙalubalanci sakamakon zaɓen, lamarin da ya sa aka yi masa ɗaurin talala na kusan shekara 16 har zuwa yanzu.
Jagorancin Iran
Iran tana yaƙi ne da Amurka da Isra'ila a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin cikin gida.
Bayan kisan Ali Khamenei, an ga muhimmancin jagoran addinin, inda aka riƙa samun tsaiko wajen ɗaukar matakai masu muhimmanci saboda rashin jagora ɗaya da zai bayar da umarni.
Ta hanyar zaɓen Mojtaba ba tare da ɓata lokaci ba, Iran ta nuna cewa a shirye take ta cigaba daga inda marigayin ya tsaya.
Sai dai duk da haka, amincewa da sabon shugaban daban da sanar da shi a matsayin shugaba.
Mubaya'a
Tun bayan sanarwar, sai aka fara batun mubaya'a a tsakanin jagororin siyasa da na soji ga sabon jagoran.
Dakarun juyin-juya-halin ƙasar ne suka shige gaba, inda manyan kwamandojin rundunar suka bayyana shi a matsayin "Mataimakin Imam Mahadi,"
Haka kuma a wani gefen, ƙasar ta gargaɗi masu yunƙurin zaga-zanga, inda suka ce jami'an tsaron ƙasar a shirye suke su murƙushe duk wata zanga-zangar adawa da shugabancin Mojtaba.
Wannan na cikin matakan da ƙasar ke ɗauka domin nuna haɗin kai, sannan suna yunƙurin nuna wa duniya cewa babu ƙofar saɓani, wadda za ta iya bayar da damar samun matsala da rikicin siyasa.
Samun ƙarbuwa
Sai dai duk da irin goyon bayan da sabon jagoran addinin ke samu, yana fuskantar ƙalubale.
Ana dai ganin Mojtaba ba ya cikin manyan malaman ƙasar, waɗanda ake wa laƙabi da Ayatollahi. Sai dai tuni waɗanda suka masa mubaya'a suka fara kiransa da sunan Ayatollah Mojtaba Khamenei.
Mahaifinsa ma ya fuskanci ƙalubale irin wannan lokacin da ya zama jagoran addinin ƙasar a shekarar 1989, saboda ba ya cikin manyan malaman ƙasar.
Ali Khamenei ya yi aiki da shugabanni da dama, kuma yana da abokai a cikin ƴan siyasar ƙasar. Mojtaba kuwa, yawancin rayuwarsa a bayan fage ya yi.
Sannan yawancin waɗanda suka kasance ko dai na kusa da mahaifinsa, ko waɗanda suka yi aiki da shi, musamman kwamandojin soji da jagororin tattara bayanan sirri an kashe su ko dai a yaƙin kwana 12 na 2025, ko kuma a hare-haren yazu.
A hare-haren wannan karon ne aka kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa da matarsa baki ɗaya.
Shi kansa an kwanaki ana fargabar an kashe shi, kafin daga bisani aka tabbatar yana raye.
Ƙalubale a gaba
Kafin fara gyara tsare-tsaren tafiyar da Iran, babban aikin da ke gaban sabon jagoran addini na farko-farko shi ne kafa kansa.
Wannan na nufin fito da kansa a ga abubuwan da zai iya, musamman daɗewa da ya yi yana gudanar da harkokinsa ta bayan fage.
Haka kuma shi ne zai ɗauki mataki kan yaƙin da ƙasar ke gwabzawa da manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin soji guda biyu, waɗanda suka bayyana cewa za su yi farautar sabonda jagoran.
Yawancin mutanen da suka yi zanga-zanga a baya sun yi tunanin cewa rasuwar Ali Khamenei za ta buɗe sabuwar yanayin gudanar da siyasa da mulki a ƙasar.
Amma sai yanzu suka faɗa hannun sabo Khamenei, wanda matashi da wataƙila ma ya fi kuzari.