Truong My Lan: Attajirar Vietnam da ake zargi da almundahanar biliyoyin daloli

.

Asalin hoton, Getty image

Bayanan hoto, Ana zargin Truong My Lan da sace makudan kudade a daya daga cikin manyan bankunan Vietnam, cikin shekaru 11

Shari'a ce da ba a taba ganin irinta a kasar Vietnam ba, da ta hada da almundahana mafi girma a daya daga cikjin gawurtattun bakuna da duniya ta shaida.

An gurfanar da matar mai arzikin gaske da ta yi shura wajen harkar gine-gine, ana shari'ar ne a daya daga cikin tsofaffin kotunan kasar tun zamanin mulkin mallaka da ke Ho Chi Minh.

Matar mai shekaru 67 ta wawure dukiyar kasa ta biliyoyin daloli a tsahon shekaru 11a bankuna daban-daban na kasar.

Adadin kudin da aka fada masu tada hankali ne. Ana zargin Truong My Lan da karbar bashin dala biliyan 35 daga bankin kasuwanci na Saigon Commercial Bank. Amma ma su shigar da kara sun ce, ba za a taba gano inda dala biliyan 27 su ke ba.

Gwamnatin Kwamunusanci ta kasar ta fara kokarin kunbiya-kunbiya kan batun, amma daga bisani dolke suka bara.

Sun fara bayyanawa manema labarai duk wani abu da ya shafi shari'ar, sun kuma tabbatar da an gayyaci sama da mutane 2,700 domin ba da shaida kan wannan badakala.

Tawagar masu shigar da kara daga jihohi 10 da lauyoyi 200 ne ke jagoranta da wakiltar gwamnati a shari'ar.

A zaman farko na shari'ar, an kawo manyan akwatuna da suke dauke da takardu da bayanan shaidu da aka auna nauyinsu sun kai tan 6. A bangare guda kuma wasu mutane 85 an gurfanar da su duk dai kan wannan badakala da Truong My Lon, wadda ta musanta dukkan tuhumar da ake yi mata.

Ita da wasu mutane 13 ka iya fuskantar hukuncin kisa idan aka same su da laifi.