Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gavi zai yi jinya ta tsawon lokaci
Dan wasan tsakiya na Barcelona Gavi ya ji rauni a ƙafarsa yayin da yake taka leda da tawagar Sifaniya kuma kulob dinsa ya tabbatar yana bukatar tiyata.
Gavi, mai shekara 19, ya bar filin wasa yana hawaye ranar Lahadi bayan ya yi mummunar fadowa a lokacin da ya yi tsalle don sarrafa ƙwallo.
Barca ta ce za a yi masa tiyata a ACL na ƙafarsa ta dama, tare da cewa za ta yi ƙarin bayani kan raunin da ya ji a cikin "kwanaki masu zuwa".
Gavi na iya rasa sauran kakar wasan nan kuma ana shakkun damarsa ta buga gasar Euro 2024 da kuma gasar Olympics ta Paris.
Barcelona ta tabbatar da raunin a ranar Litinin kuma lokacin murmurewarsa na iya kaiwa wata takwas zuwa 10.
Gavi ya buga wa kulob ɗin na Catalonia wasa 111, inda ya zira ƙwallaye bakwai ya kuma taimaka aka zira 12, yayin da ya buga wa Sifaniya wasanni 27 tare da cin ƙwallaye biyar.
Ya taimaka wa Barca ta lashe gasar La Liga da kuma Super Cup na Sifaniya a bara.