Tsohon shugaban Angola José Eduardo dos Santos ya mutu

José Eduardo dos Santos ya sauka daga mulki a 2017 bayan ya kwashe shekara 38 yana shugabancin Angola

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, José Eduardo dos Santos ya sauka daga mulki a 2017 bayan ya kwashe shekara 38 yana shugabancin Angola

Tsohon Shugaban Angola José Eduardo dos Santos ya rasu, bayan ya yi wata doguwar jinya.

Ya mutu ne a kasar Sifaniya inda yake jinyar bugun zuciya.

Shafin Facebook na fadar gwamnatin kasar ne ya bayar da sanarwar rasuwar tasa da safiyar yau Juma'a.

Shugaba Dos Santos, mai shekara 79, ya shafe shekara 38 yana jagorantar kasar, wacce ke da tarin arzikin mai da ma'adinai.

Ya sauka daga mulki a 2017.

Za a tuna da shi a matsayin wanda ya kawo karshen yakin-basara a shekarun 2000 wanda aka kwashe lokaci mai tsawo ana yinsa- magoya bayansa suna kiransa da suna mutumin da ya "wanzar da zaman lafiya".

Sai dai ana zarginsa da cin hanci da take hakkin dan adam lokacin da yake kan mulki.

Dos Santos ya zama shugaban Angola ne yana da shekara 37 sakamakon mutuwar Shugaba António Agostinho Neto bayan ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin Injiniyan Fetur daga tsohuwar Tarayyar Sobiyet a shekarar 1969.