Yadda Trump ya samar da zaman lafiyar da ya gagari Biden a Gaza

Trump da Netenyahu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump da fraiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
    • Marubuci, Tom Bateman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, State Department correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 7

A lokacin da Isra'ila ta kai hari ta sama kan tawagar masu tattaunawa ta Hamas a ƙasar Qatar, mutane da dama sun ɗauka cewa hakan wani sabon tashin hankali ne da ya kara nisantar da yiwuwar samun zaman lafiya a Gaza.

Harin da aka kai a ranar 9 ga Satumba ya keta ikon ƙasar Qatar wadda take abokiyar Amurka, kuma ya haifar da haɗarin yaɗuwar rikicin zuwa yankin gaba ɗaya.

A lokacin, al'amuran diflomasiyya sun yi kama da waɗanda suka rushe.

Sai dai abin mamakin shi ne, wannan harin ne ya zama muhimmin lamari da ya kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda shugaban Amurka Donald Trump ya sanar ta sako duk sauran fursunonin.

Wannan buri ne da tsohon shugaban Amurka Joe Biden suka dade suna ƙoƙarin cimma tsawon kusan shekaru biyu.

Duk da cewa wannan mataki ne na farko zuwa ga zaman lafiya mai dorewa, har yanzu akwai batutuwan da za a tattauna, kamar yadda Hamas za ta ajiye makamai da yadda za a tafiyar da Gaza, da kuma cikakken janyewar Isra'ila.

Amma idan wannan yarjejeniyar ta tabbata, za ta zama babbar nasarar Trump a wa'adinsa na biyu, nasarar da Biden da tawagarsa ta diflomasiyya suka kasa cimma.

Salon mulkin Trump da kyakkyawar dangantakarsa da Isra'ila da ƙasashen Larabawa sun taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan cigaba.

Sai dai kamar yawancin nasarorin diflomasiyya, akwai wasu dalilai da suka fi karfin ikon kowannensu.

Dangantakar kusanci da Biden bai taɓa samu ba

Trump yawanci yana cewa Isra'ila ba ta da aboki mafi kyau a duniya fiye da shi, yayin da Netanyahu kuma ya bayyana Trump a matsayin "babban abokin Isra'ila da ta taɓa samu a Fadar White House.".

A wa'adinsa na farko a matsayin shugaban kasa, Trump ya mayar da ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Urushalima, kuma ya janye matsayar da Amurka ta daɗe tana riƙe da ita cewa gine-ginen Isra'ila a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan na Falasdinu ba bisa doka ba ne matsayar da dokokin kasa da kasa ke tabbatarwa.

Lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-haren sama kan Iran a watan Yuni, Trump ya umarci rundunar jiragen yaƙin Amurka da ta kai hari kan wuraren da Iran ke sarrafa makaman nukiliyarta da manyan bama-bamai mafi karfi da ake da su.

...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Isra'ilawa sun ɗaga tutocin Amurka da Isra'ila bayan jin labarin yarjejeniyar.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wadannan irin goyon bayan da ake gani a fili na iya bai wa Trump damar matsa wa Isra'ila lamba a bayan fage.

Rahotanni sun nuna cewa mai shiga tsakani na Trump, Steve Witkoff, ya matsa wa Netanyahu a ƙarshen shekarar 2024 har sai da ya amince da tsagaita wuta na ɗan lokaci yayin da za a a saki wasu daga cikin fursunonin Isra'ila da Hamas ke riƙe da su.

Lokacin da Isra'ila ta kai hare-hare kan dakarun Siriya a watan Yuli ciki har da bama-baman da suka lalata coci, Trump ya matsa wa Netanyahu ya canza matsayinsa.

Aaron David Miller daga cibiyar Carnegie Endowment for International Peace ya ce, "Trump ya nuna irin ƙarfin hali da matsin lamba ga Firaministan Isra'ila da ba a taɓa ganin irinsa ba.

Babu wani misali da wani shugaban Amurka ya taɓa faɗa wa firaministan Isra'ila kai tsaye cewa 'dole ne ka bi umarnina, in ba haka ba, ka fuskanci abin da zai biyo baya."

Dangantakar Biden da gwamnatin Netanyahu ba ta da ƙarfi sosai tun farko.

Manufar gwamnatinsa ta "bear hug" ta dogara ne da ra'ayin cewa dole Amurka ta nuna goyon baya ga Isra'ila a fili, domin samun damar lallaɓa ta ta rage tsanantar yaƙin a bayan fage.

A ƙarƙashin wannan dabarar akwai kusan shekaru hamsin na goyon bayan Biden ga Isra'ila, tare da rikice-rikicen ra'ayi a cikin jam'iyyarsa ta Democrat game da yaƙin Gaza.

Duk wani mataki da Biden ya ɗauka yana da haɗarin tarwatsa goyon bayan cikin gida, yayin da Trump kuwa yake da cikakken goyon bayan jam'iyyarsa ta Republican, wanda ya ba shi sarari don yin abubuwa yadda yake so.

A ƙarshe, siyasar cikin gida ko alaƙar mutum da mutum ba su da wani tasiri fiye da gaskiyar cewa, a lokacin mulkin Biden, Isra'ila ba ta shirya yin sulhu ba.

Tarihin kasuwanci ya taimaka wajen samun goyon bayan ƙasashen Gulf

Harin makamin roka da Isra'ila ta kai a birnin Doha, wanda ya hallaka ɗan ƙasar Qatar amma bai kashe wani jami'in Hamas ba, ya sa Trump ya aika wa Netanyahu da gargaɗi mai tsanani da ke cewa 'dole ne a kawo ƙarshen yaki.'

Trump ya ba Isra'ila cikakken 'yanci wajen kai hare-hare a Gaza, kuma ya tallafa mata da ƙarfin sojojin Amurka a yaƙinta da Iran.

Amma kai hari a ƙasar Qatar ya zama wata matsala daban gaba ɗaya, wadda ta sa Trump ya fara karkata zuwa ra'ayin ƙasashen Larabawa kan yadda ya kamata a kawo ƙarshen wannan yaki.

Wasu jami'an gwamnatin Trump sun shaida wa abokan aikin BBC a tashar CBS cewa wannan lamari wanda ya sa shugaban ya matsa ƙarfi sosai don ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Shugaban Siriya Ahmed al-Sharaa na tafiya a kan jan kafet bayan sauka daga jirgi a Doha kafin taron gaggawa na shugabannin Larabawa da Musulmai

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An gudanar da taron gaggawa na shugabannin Larabawa a Doha bayan harin Isra'ila a Qatar

An san cewa Donald Trump na da kusanci sosai da ƙasashen Gulf.

Yana da harkokin kasuwanci da ƙasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE kuma ya fara dukkan wa'adinsa na shugabanci da ziyarar aiki zuwa Saudiyya.

A bana ma, ya tsaya a Doha da Abu Dhabi yayin wata ziyararsa.

Yarjejeniyarsa ta 'Abraham Accords', wadda ta daidaita dangantaka tsakanin Isra'ila da wasu ƙasashen Musulmi, ciki har da UAE, ita ce babbar nasarar diflomasiyya a wa'adinsa na farko.

Ed Husain daga majalisar dangantakar ƙasashe ya ce lokacin da shugaban ya shafe a biranen yankin Tekun Larabawa a farkon wannan shekara ya taimaka wajen canza yadda yake tunani.

A ziyararsa zuwa Gabas ta Tsakiya, Trump bai ziyarci Isra'ila ba, amma ya je UAE da Saudiyya da Qatar inda ya ji kira sau da dama daga shugabannin ƙasashen nan suna roƙon a kawo ƙarshen yaƙin.

....

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yaran Falasɗinu na murna bayan Isra'ila da Hamas sun amince da mataki na farko na tsagaita wuta

Ƙasa da wata guda bayan harin Isra'ila a Doha, Trump ya zauna kusa da firaministan Isra'ila lokacin da ya kira ƙasar Qatar da kansa domin bada haƙuri.

A ranar nan ma, Netanyahu ya rattaɓa hannu kan shirin zaman lafiya mai matakai 20 na Trump don Gaza wanda kuma ya samu goyon bayan muhimman ƙasashen Musulmi na yankin.

Idan dangantakar Trump da Netanyahu ta ba shi damar matsa wa Isra'ila lamba don cimma yarjejeniya, to tarihi da alaƙarsa da shugabannin Musulmi ne suka taimaka wajen samun goyon bayansu da kuma shawo kan Hamas ta amince da yarjejeniyar.

Jon Alterman daga cibiyar nazarin dabarun siyasa da huldar ƙasashen waje (CSIS) ya ce, "Shugaba Trump ya samu damar yin tasiri a kan Isra'ilawa kai tsaye da kuma a kan Hamas a ba kai tsaye ba.

Wannan ya bambanta da sauran shugabanni da suka gabata, domin ya iya yin abubuwa bisa jadawalin da ya tsara, ba tare da ya bi son ran ɓangarorin da ke yaki ba."

Yanzu Isra'ila ta amince da sakin fiye da fursunoni 1,000 na Falasɗinu da take tsare da su, tare da janye wani ɓangare na dakarunta daga Gaza.

Hamas kuma za ta saki duk sauran fursunonin da ta kama raye ko a macce a harin da ta kai ranar 7 ga Oktoba, wanda ya hallaka Isra'ilawa sama da 1,200.

Turawa na amfani da tasirinsu

Sukar da ta biyo bayan ayyukan Isra'ila a Gaza daga sassan duniya sun kuma shafi tunanin Trump.

Halin da ake ciki a Gaza an daɗe ba a ga irinta ba ta fuskar lalacewa da bala'in jin kai da Falasɗinawa ke fuskanta.

A cikin watannin da suka gabata, sauran ƙasashen duniya sun ware gwamnatin Netanyahu.

Lokacin da Isra'ila ta karɓi ikon rarraba abinci ga Falasɗinawa sannan ta sanar da shirin kai hari kan birnin Gaza, wasu manyan ƙasashen Turai ƙarkashin jagorancin shugaban Faransa Emmanuel Macron suka yanke shawarar cewa ba za su iya ci gaba da goyon baya ga Isra'ila ba kamar yadda Amurka take yi.

...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Falasɗinawa na kallo daga taga bayan sanarwar tsagaita wuta a Gaza.

An samu rarrabuwar kai a tsakanin Amurka da abokan Tarayyar Turai kan muhimman batutuwa na diflomasiyya da makomar rikicin Isra'ila da Falasɗinu.

Gwamnatin Trump ta soki Faransa lokacin da ta ce za ta amince da ƙasar Falasɗinu, abin da Birtaniya ma ta bi.

Manufarsu ita ce tabbatar da mafitar ƙafa ƙasashen biyu da rage ƙarfin masu tsattsauran ra'ayi a bangarorin biyu.

Amma Macron ya samu nasarar samun goyon bayan Saudiyya kan shirin zaman lafiyarsa.

A ƙarshe, Trump ya tsinci kansa a tsakiyar haɗin Turai da Larabawa da masu kishin Isra'ila da 'yan adawa, sai ya zaɓi abokansa na ƙasashen Gulf.

A ƙarƙashin shirin Faransa da Saudiyya da kasashen Larabawa sun soki hare-haren Hamas na 7 ga Oktoba kuma sun buƙaci ƙungiyar ta kawo ƙarshen mulkinta a Gaza tare da miƙa makamai ga Hukumar Falasɗinu.

Wannan nasara ce ta diflomasiyya ga Larabawa da Turawa.

Salon Trump na musamman ne ya samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Gaza

Salon Trump na musamman na cikin abin da ya samar da cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Gaza

Trump ya fara wa'adinsa na biyu da shawarar ban mamaki cewa Falasɗinu su bar Gaza domin a mayar da shi wurin shakatawa na duniya a bakin teku.

Wannan ya fusata shugabannin Musulmi, kuma masu diflomasiyya na Gabas ta Tsakiya sun yi mamaki sosai.

Sai dai shirin zaman lafiya na matakai 20 na Trump ba shi da bambanci sosai da abin da Biden zai iya cimmawa, kuma abin da abokan Amurka suka jima suna goyon baya.

Trump ya bi hanya mai ban sha'awa don cimma sakamakon da aka saba samu.