Yadda kamfanonin China ke amfani da Mexico don kauce wa harajin Amurka

Mexican workers building sofas at Man Wah's factory in Monterrey
Bayanan hoto, Ƙera kaya a Mexico ya bai wa kamfanin Man Wah na China damar kauce wa harajin Amurka
    • Marubuci, By Will Grant
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Mexico correspondent, Monterrey

Kamfanin China na sarrafa kayan kujeru, Man Wah na samun karɓuwa ɗari bisa ɗari a Mexico.

Kamfanin ya samu damar kasancewa babban kamfanin da kamfanonin Amurka da dama irin su Costco da Walmart ke dillancin kayayyakinsa. Asalin kamfanin daga China ne, Kuma China ce ta gina reshen kamfanin a Mexico.

Wannan dangantakar kasuwancin tsakanin ƙasashen Amurka da China da kuma Mexico shi ya haifar da wata kalma da 'yan kasuwar Mexico ke amfani da ita, na cewa kasuwanci tsakanin ƙasashe.

Man Wah ya kasance ɗaya daga cikin kamfanonin China da suka yi ƙaura zuwa arewacin Mexico a shekarun baya-bayan nan, domin kai kayansu kusa da kasuwannin Amurka, da kuma kauce wa biyan kuɗin fito.

Ana ɗaukar kayan da kamfanin ke sarrafawa a matsayin wanda aka ƙera a Mexico, hakan na nufin kamfanonin China za su kauce wa harje-harajen Amurka, da takunkuman da Amurkan ke sanya wa kayayyakin China, saboda rikicin kasuwanci da ke tsakanin ƙasashen biyu.

A yayin da babban manajan kamfanin Yu Ken Wei, ya zagaya da ni harabar kamfanin, ya ce mayar da kamfanin zuwa Mexico ya taimaka wa dabarun kasuwancin ƙasar.

"Muna fatan ninka abain da muke ƙera wa da kashi uku ko huɗu a nan,'' lokacin da yake min bayani cikin harshen Sifaniyanci.

''Manufar hakan a nan Mexico shi ne ƙara yawan abubuwan da muke ƙera wa kamar yadda muke yi a Vietnam." in ji shi.

General manager Yu Ken Wei
Bayanan hoto, Babban manajan kamfanin, Yu Ken Wei ya ce, suna shirin ninka abin da kamfanin ke ƙerawa da ninki uku a Mexico
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A 2022 ne aka kai kamfanin birni Monterrey, inda ya ɗauki ma'aikata 'yan asalin Mexico kimanin 450.

Yu Ken Wei ya ce suna fatan, kamfanin zai ɗauki fiye da ma'aikata 1,200, da za su riƙa yin aiki a sauran rassansa nan da shekaru masu zuwa.

"Mutane a nan Mexico na aiki tuƙuru, kuma suna da saurin koyon abubuwa,'' in ji Mista Yu.

"Mun samu ma'aiakata masu hazaƙa, kuma suna ƙara abubuwa masu yawa. Don haka a ɓangaren ma'aikata, ina tunanin Mexico na da kyawun yanayin kasuwanci.''

Kamfanin Man Wah da ke ƙera kujeru da sauran kayan ofis na yankin Hofusan, wato yanzkin da kamfanonin China da ke Mexico suke.

Kuma ana samun ƙaruwar buƙatar kayayyakinsa, duk abin da aka ƙera na samun shiga a kasuwa.

Haka ma, ƙungiyar kamfanonin Mexico ta ce duk wani kamfani da ake shirin ginawa a ƙasar daga shekarar 2027 an riga an saye shi.

Abin mamakin shi ne mafi yawan masana tattalin arzikin Mexico na cewa muradin China a ƙasar ba haka nan kawai yake ba.

"Akwai dalilin da ya sa China ke kawo jarinsu Mexico,'' in ji Juan Carlos Baker Pineda, tsohon mataimakin ministan harkokin kasuwancin ƙetare na Mexico ya bayyana.

''Bani da wata alama da ke nuna cewa rikicin kasuwanci tsakanin China da Amurka ka iya zama tarihi nan ba da jimawa ba.''

Mista Baker Pineda na cikin tawagar da ta tattauna hulɗar kasuwanci da yankin arewacin Amurka, USMCA.

"A yayin da jarin da China ke zuwa da shi Mexico ka iya samun cikas ga tsare-tsare ko manufofin wasu ƙasashe," in ji shi, "dokokin kasuwanci na duniya, wadannan kayayyaki na da dalilai,''.

Hakan ya bai wa Mexico damar kasancewa mai shiga tsakanin manyan ƙasashe mafiya ƙarfin kasuwanci a duniya. A baya-bayan nan Mexico ta maye gurbin Amurka a matsayin babbar ƙawar kasuwancin China.

Workers at the factory sewing the covers for the sofas
Bayanan hoto, Shugabannin kamfanin Man Wah sun yaba da ƙwarewar ma'aikatan Mexico

Ƙaruwar hulɗar kasuwanci tsakanin Mexico da Amurka na daga cikin abubuwan da ke ƙara danƙlon alaƙa tsakanin ƙasashen.

Kamfanonin Amurka na kafa rassa a Mexico a wasu lokatan bayan janye wa daga ƙasashen yankin Asiya.

Abu na baya-bayan nan shi ne lokacin da fitaccen attajirin nan na duniya Elon Musk ya bayyana a shekarar da ta gabata cewa zai kafa sabon reshen kamfanin Tesla mai ƙera motocin laturoni a wajen birnin Monterrey.

Sai dai har yanzu kamfanin ƙera motocin laturonin bai fara aikin da zai laƙume kimanin dala biliyan 10 ba.

A yayin da har yanzu kamfanin ke da burin aikin, tana jan ƙafa kan shirin, sakamakon matsalar tattalin arziki da duniya ke fuskanta da kuma ake samun raguwar ma'aikata a kasuwanni ƙananan motoci.

To amma dangane da zuba jari da China ke yi, wasu na nuna damuwa kan yadda Mexico ke jan hankalin duniya tsakanin rikicin Amurka da China.

A yayin da lokacin zaɓe ke ƙaratowa a Amurka, batun kan iyakar Mexico na daga cikin abubuwan da ka iya ɗaukar hankali a lokacin yaƙin neman zaɓen.

Kuma ko ma wane ne ya lashe zaɓen tsakanin Biden ta Trump, ƙalilan ne ke sa ran za a iya samun kyautatuwar alaƙa tsakanin Amurka da China.

A new unit being built at the Chinese-Mexican industrial park in Monterrey
Bayanan hoto, Kamfanonin China na kokawar sayen duk wani sabon kamfani da aka gina a rukunin masan'antun mexico

Wasu kuma na da kyautata zato game da hulɗar "A tunani na, abin tambayar shi ne shin wannan yanayin zai ci gaba ko a'a, ta yaya za mu amfana da wannan yanayin," in ji tsohon jami'in kasuwancin Mexico, Juan Carlos Baker Pineda.

"Na tabbata mutane na irin wannan tattaunawa a Colombia, da Vietnam, da Costa Rica. Don haka, muna buƙatar tabbatar da cewa a Mexico, waɗannan sharuɗɗan da suka dace da kansu suna tafiya kafada da kafada da yanke shawara na kamfanoni da na gwamnati, don kiyaye wannan yanayin a cikin dogon lokaci."

Can kuwa a Monterrey, kamfanin samar da kayan kujeru na Man Wah na aikewa da kayyakin da yake ƙerawa zuwa arewacin ƙasar.

Idan Amurkawa suka saye kayan a kantin Walmart da ke dilancin kayyakin da ke kusa da su, ba za su iya fahimtar matsalar siyasar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Ko ma dai wannan kasuwanci na bayan fage tsakanin China da Amurka ka iya haifar da ruruwar yaƙi tsakanin ƙasashen biyu, a nata ɓangare, Mexico na samun amfanuwa a wannan lokaci da kasuwancin duniya ke samun tangarɗa.