Abubuwan da suka kamata ku sani kan guguwar da za ta afka wa Tanzania

Asalin hoton, ZOOM EARTH
- Marubuci, Tell Hirsi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- Aiko rahoto daga, Nairobi
Yankin gaɓar ruwan Gabashin Afirka, musamman Tanzaniya, zai fuskanci guguwar da aka yi wa laƙabi da Hidaya, wadda za ta haddasa ruwan sama mai ƙarfi.
Tun a farkon makon nan ne hukumar nazarin yanayi ta Tanzaniya (TMA) ta sanar cewa akwai ƙaramar guguwa da ake sa ran za ta ci gaba da ƙaruwa kuma ta haddasa ruwan sama mai ƙarfi, da iska a yankuna biyar na ƙasar da suka haɗa da Mtwatra, da Dar es Salaam, da Lindi, da yankunan Tanga, da Morogoro, da Pemba, da Unguja, da Unguja islands.
Guguwar Hidaya ta fara tunkarowa ne a ranar Laraba a kudancin Tekun Indiya zuwa gabashin Tanzaniya da arewa maso yammacin Tsibirin Comoro.
A cewar TMA, zuwa yanzu alamu na nuna aukuwar guguwar ta Hidaya yayin da take ƙara matsawa kusa da gabar ruwan Tanzaniya, kuma za ta ci gaba da yin hakan har zuwa Litinin, 6 ga watan Mayu.
A cewar hukumomi, guguwar na ci gaba da girmama, har ma ƙarfinta ya kai gudun kilomita 110 duk awa ɗaya a daren Juma'a.
Wane gargaɗi TMA ta yi?
Gwamnati ta bai wa mutane shawarar su ci gaba da lura da kuma duba yanayi daga majiyoyin ba da bayanai don sanin yadda za su kare kansu.
TMA ta ce ƙaruwar gudun iskar da kuma ruwa mai ƙarfi za su haifar da igiyar ruwa a koguna kuma za ta watsu zuwa gabar ruwa a ranakun Asabar da Litinin (4 da 6 ga watan Mayu).
Sakamakon haka, TMA ta gargaɗi 'yan ƙasa su ci gaba da lura da kuma sa ido kan abin da ke faruwa.
Me Kenya ta ce?
Gwamnatin Kenya ta faɗa ranar Alhamis cewa ƙila nan da 'yan kwanaki guguwar ta Hidaya ta afka wa gabar ruwa saboda ƙaruwar ruwan sama mai ƙarfi da ake gani a ƙasar.
An yi gargaɗin ne bayan ganawa ta musamman da majalisar ministoci ta yi ranar Alhamis don tattauna ƙarin matakan kare aukuwar ambaliya, da zarftarewar laka da kuma ƙasa.
Mece ce guguwa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar ƙungiyar kula da yanayi ta duniya World Meteorological Organization (WMO), guguwa iska ce mai ƙarfin gaske da ke jujjuyawa a kan tekuna.
Cibiyar Meteo France La Reunion ce ta kira wannan da suna Hidaya, tare da yin hasashen bin sawunta zuwa arewa maso yammaci daga 2 zuwa 4 ga watan Mayun 2024.
Guguwa ta ƙarshe da ta taɓa afka wa Tanzaniya ita ce a 1952 (lokacin tana ƙarƙashin mulkin mallakar Tanganyika), kuma ta sauka a yankin Lindi da ke kudancin Tanzaniya.
A yankin Zanzibar kuma, ta faru ne a 1872 kuma an ji tasirinta a sassan ƙasar kamar Bagamoyo, da arewacin Dar Es Salaam.
Idan Guguwar Hidaya ta afko kan ƙasa, zai zama karo na farko kenan a tarihi da hakan ta faru a Dar Es Salaam.
A 'yan shekarun nan, Tanzaniya ta fuskanci guguwa biyu, inda aka yi hasashen ta 2019 mai suna Kenneth za ta afka wa Mtwara amma sai ta sauya hanya zuwa Mozambique.
A 2021, an zaci Guguwar Jobo za ta yi ɓarna amma sai ta ragu kuma ba ta haddasa wata ɓarna ba.











