Arsenal na son Nkunku, Liverpool za ta yi sabon cefane

Christopher Nkunku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Christopher Nkunku
Lokacin karatu: Minti 3

Arsenal na son dauko Christopher Nkunku daga Chelsea wadanda ke shirin zawarcin Jamie Gittens, Everton na son sake siyan Richarlison, Paul Pogba na son komawa DC United, da sauran su.

Arsenal na tunanin zawarcin dan wasan gaban Chelsea da Faransa Christopher Nkunku, mai shekara 27, yayin da Mikel Arteta ke neman kara karfafa gabansa a wannan bazarar. (Teamtalk)

DC United ta shafe watanni tana tattaunawa da tsohon dan wasan Manchester United, Juventus da Faransa Paul Pogba, mai shekara 32, wanda bai buga wasa ba tsawon watanni 20. (Washington Post)

Zakarun gasar Premier Liverpool na shirin sanya hannun jari sosai a kungiyar a lokacin bazara, musamman don siyan dan wasan gaba da na baya da kuma na hagu. (Telegraph)

Chelsea na shirin zawarcin dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jamie Gittens, mai shekara 20, kuma akwai yiwuwar ta sayar da dan wasan gaban Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, ga kulob din na Jamus a wani bangare na yarjejeniyar. A halin yanzu Sancho yana zaman aro a Stamford Bridge daga Manchester United amma Blues din na da alhakin sanya yarjejeniyar ta dindindin. (Teamtalk)

Shugaban Real Sociedad Jokin Aperribay ya ce za a cimma matsaya kan makomar Martin Zubimendi da Arsenal ke nema a watan Yuni. Gunners din suna shirye don tunkarar dan wasan tsakiyar dan Spain mai shekara 26 a kan fam miliyan 51. (Radio Marca Donostia)

Everton ta don sayan dan wasan Tottenham da Brazil Richarlison, mai shekara 27 (Givemesport)

Leeds na fatan daukar dan wasan tsakiyar Newcastle na Ingila Sean Longstaff, mai shekara 27 (j Paper)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tottenham za ta sayar da wasu 'yan wasanta, don samun kudin siyasan wasu sabbin yan wasa a wannan bazara. (Telegraph)

Fulham na sha'awar sayen dan wasan bayan Ingila Kyle Walker-Peters, mai shekara 28 a kyauta lokacin da kwantiraginsa na Southampton zai kare a bazara. (Sky Sports)

A shirye Arsenal take ta fara tattaunawa da wakilin dan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, game da komawa kungiyar a bazara (Givemesport)

Real Betis na iya fuskantar kalubalae wajen wajen kudin da Manchester United ta sanya a matsayin farashin dan wasan Brazil Antony duk da cewa shugaban kulab din na La Liga ya nace cewa suna son daukar dan wasan mai shekara 25 dindindin (Mirror)

Har yanzu Manchester United na sha'awar siyan dan wasan gaba na Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 26, amma akwai kalubale a kan yarjejeniyar. (TBF Football)

Everton na tattaunawa da dan wasan tsakiyar Senegal Idrissa Gueye, mai shekara 35, kan sabon kwantaragi. (Football Insider)

Wrexham, da Bolton, da Charlton da Portsmouth suna sha'awar dan wasan gaba na Dungannon Swifts na Ireland Ta Arewa,Tomas Galvin, mai shekara 20. (Football League World)