Man Utd da Tottenham da Liverpool na rububin David, Chelsea na neman yi wa Arsenal fancale

Jonathan David

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Atletico Madrid na son Cristian Romero, Manchester City na zawarcin dan wasan baya na Juventus Andrea Cambiaso, Manchester United na zawarcin dan wasan Palace Mateta, da dai sauransu.

Atletico Madrid na son dan wasan bayan Tottenham dan kasar Argentina Cristian Romero, mai shekara 27 (Marca)

Ana sa ran Manchester City za ta dauko dan wasan bayan Italiya da Juventus Andrea Cambiaso, mai shekara 25, inda kulob din na Italiya ya karkata zuwa ga dan wasan bayan Arsenal na Portugal Nuno Tavares, mai shekara 25, wanda ke zaman aro a Lazio. (Sun)

Newcastle United, da Manchester United, da Tottenham, da West Ham, da Chelsea, da Liverpool duk suna sha'awar sayen dan wasan Canada Jonathan David, mai shekara 25, lokacin da kwantiraginsa na Lille ya kare a bazara, amma Marseille na fatan shawo kan dan wasan ya ci gaba da zama a Faransa. (RMC Sport)

Manchester United ta yiwa dan wasan gaban Wolves Matheus Cunha tayin kwantiragin shekaru biyar idan dan kasar Brazil din mai shekaru 25 ya zabi komawa Old Trafford. (Teamtalk).

Chelsea na matsa kaimi wajen ganin ta riga kulla yarjejeniya da dan wasan gaban Juventus Kenan Yildiz, mai shekara 19, wanda Arsenal, da Liverpool, da Manchester United da Manchester City ke nema. (Cought Offide)

Manchester United na ci gaba da sha'awar sayen dan wasan gaban Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, mai shekara 27, idan ba za su iya sayen dan wasan gaban Ipswich na Ingila Liam Delap, mai shekara 22 ba. (GiveMesport)

Newcastle United na kokarin daukar dan wasan bayan Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekara 28, daga Bayern Munich a bazara. (Football Insider)

Newcastle ta fitar da jerin sunayen wasy yan baya da take sha'awar dauka don karfafa bayanta, da suka hada da dan wasan Sporting dan kasar Ivory Coast Ousmane Diomande, mai shekara 21, da dan wasan baya na AC Milan Malick Thiaw, mai shekara 23, da dan kasar Holland Jan Paul van Hecke, mai shekara 24, daga Brighton. (GiveMeSport)