Arsenal na son Kounde, Man United ta dage kan Cunha

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na son mai tsaron gidan Faransa da ke taka leda a Barcelona Jules Kounde mai shekara 26, kan kudi fam miliyan 55. (Sun - subscription required)
Watakil Nottingham Forest, ta sake zawarcin dan wasan Manchester City, James McAtee, mai shekara 22, ko da kuwa za su ci gaba da rike 'yan wasan gaba biyu, wato na Ingila Callum Hudson-Odoi mai shekara 24 da dan wasan Sweden Anthony Elanga mai shekara 22, wadanda kungiyoyi da dama ke zawarcinsu. (Sky Sports)
Dan wasan gaban Ingila Jamie Vardy, mai shekara 38, ka iya komawa taka leda Wrexham idan kwantiraginsa da Leicester City ya kare, idan kuma kulub din ya samu nasarar komawa gasar Championship daga League One. (Talksport)
Manchester United za ta karkata akalar zawarcinta kan dan wasan gaban Holland mai taka leda a RB Leipzig, Xavi Simons, mai shekara 22, idan suka gagara dauko dan wasan Brazil mai taka leda a Wolves, Matheus Cunha, mai shekara 25. (Teamtalk)
Real Betis na shirin tsawaita zaman aron da dan wasan Brazil mai taka leda a Manchester United, Antony, mai shekara 25 ke yi a kungiyar. (Telegraph)
Chelsea da wakilan dan wasan Borussia Dortmund, Jamie Gittens, mai shekara 20, sun gana domin tattauna kwantiragi da dan wasan. (Sky Germany)
Chelsea dai na da kwarin gwiwa kan dauko dan wasan gaban Ipswich Town, Liam Delap, mai shekara 22, da fatan shan gaban Manchester United da ita ma ke bibiyar dan wasan. (GiveMesport)
Strasbourg sun cimma yarjejeniya da koci, Liam Rosenior, mai shekara 40, don ci gaba da zama a kungiyar duk da nuna sha'awar daukarsa da kungiyoyi daban-daban na Premier League suka yi. (Athletic)











