Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
De Bruyne zai ci gaba da zama a City, PSG na zawarcin Kvaratskhelia
Ana sa ran dan wasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne zai tsawaita kwantiraginsa da Manchester City, duk da cewa mashawartan ɗan wasan mai shekaru 32, sun tattauna da ƙungiyoyi a Saudiyya. (Mirror)
Paris St-Germain za ta yi tayin Yuro miliyan 100 ( Fam Miliyan 85) kan ɗan wasan gaba na Georgia Khvicha Kvaratskhelia, mai shekara 23 idan har ya kasa cimma matsaya kan sabunta kwantiraginsa da Napoli. (Gazzetta dello Sport)
PSG na fargabar cewa Liverpool da Manchester United da Real Madrid za su tsere mata a fafatukar neman ɗaukar dan wasan Lille ɗan ƙasar Faransa Leny Yoro, mai shekara 18, wanda kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar wasa mai zuwa. (L'Equipe)
Napoli na tattaunawa da Antonio Conte kan batun ɗaukar tsohon kocinna Tottenham da Chelsea a matsayin sabon kocinta. (Sky Sports Italia)
Sir Jim Ratcliffe na Manchester United ya ƙi amsa tambayar da aka yi masa kan ko kocinsa Erik ten Hag zai ci gaba da zama a ƙungiyar bayan da ta doke Manchester City a gasar FA Cup. (Mail)
Daraktan wasanni na Barcelona Deco yana sha'awar ɗan wasan gefe na Liverpool Luis Diaz kuma kulob din na Sifaniya zai iya siyar da ɗan wasan gaban Brazil Raphinha don samun kuɗin ɗaukar ɗan wasan mai shekara 27. (AS- in Spanish)
Barcelona ta tuntubi ɗan wasan tsakiyar ƙasar Sifaniya Thiago Alcantara, wanda zai bar Liverpool idan kwantiraginsa ya ƙare a ranar 30 ga watan Yuni, game da dan wasan mai shekaru 33, ya zama mataimakin Hansi Flick, wanda ake sa ran zai zama sabon kocinta. (AS)
Newcastle na neman kammala sayen ƴan wasan baya na Ingila guda biyu kyauta - Lloyd Kelly na Bournemouth, mai shekara 25,da kuma Tosin Adarabioyo na Fulham, mai shekara 26. (Insider Football).
Aston Villa ta sanya farashin Fam miliyan 6 zuwa 8 kan ɗan wasan tsakiya na Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 31, amma kuma za ta iya barinsa ya tafi a matsayin aro. (Rudy Galetti)
Dan wasan gefe na ƙasar Sifaniya Lucas Vazquez, mai shekara 32, yana dab da ƙulla yarjejeniya da Real Madrid inda zai ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa aƙalla watan Yunin 2025. (Marca)