Jirgin farko na ɗaliban Najeriya daga Sudan zai sauka a Juma'ar nan - NEMA

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce daga safiyar Juma'a ne za a fara kwaso ɗaliban ƙasar da ke karatu a Sudan bayan sun isa Aswan a cikin ƙasar Masar.

Kuma jirgin saman Air Peace da zai yi aikin kwashe ɗaliban da sauran 'yan Najeriya, zai tashi da ƙarfe 6 na yamma zuwa Aswan, cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawar.

Mustapha Habib Ahmed ya ce tuni motoci guda biyu ɗauke da ɗaliban da aka kwaso daga Khartoum suka isa bakin iyaka.

Ya amsa cewa ba shakka sun samu matsala da wasu direbobi da suka zubar da ɗalibai a cikin Sahara kusa da Dongola, wani wuri mai nisan kilomita 411 daga Khartoum.

Mustapha Habib ya ce suna aikin shirya takardu tare da ofishin jakadancin Najeriya a Masar don ganin jirgin Air Peace ya samu damar jigilar 'yan Najeriyan daga birnin Aswan.

Ya ce tuni suka daidaita da kamfanin sufurin da ya zubar da ɗalibai a Sahara, har ma sun shiga motocinsu guda bakwai sun ci gaba da tafiya.

Shugaban na NEMA ya ce motocin bas 13 ne suka fara tashi a ranar Laraba, kuma tuni akwai jami'ansu da ke kan iyakar Sudan da Masar waɗanda ke karɓar 'yan Najeriyan da aka kwaso.

Tafiyar ɗalibai ta gamu da cikas a Sahara

Ɗaliban Najeriya da tun farko, suka tashi daga Sudan a motocin bas-bas zuwa ƙasar Masar, sun gamu da cikas a kan hanya.

Direbobin motoci guda bakwai da suka ɗauko ɗaliban daga birnin Khartoum ne, suka buƙaci cikon kuɗaɗensu, kafin su ci gaba da tafiya.

Ɗaliban sun ce akwai mata masu shayarwa cikinsu lokacin da motocin suka tsaya a wani wuri cikin Sahara da ke yankin Dongola.

Dongola, shi ne babban birnin jihar Arewacin Sudan wato Northern Sudan a gaɓar Kogin Nilu, tana kuma da nisan kilomita 411 daga Khartoum.

Da yammacin Laraba ne sahun farko na ɗaliban Najeriya ya fara tashi a kan hanyar zuwa Aswan, tsallaken iyakar ƙasar Masar daga Sudan.

An ji muryar wani ɗalibi, ga alama daga birnin Khartoum yana tabbatar da cewa sun samu saƙonni daga takwarorinsu da suka tashi da yammacin Laraba a motoci cewa tafiyarsu ta tsaya.

Muryar ta ci gaba da cewa bayanan da suka samu, su ne kamfanonin motocin ne suka buƙaci direbobin su dakata, har sai sun karɓi cikon kuɗaɗensu daga hannun mahukuntan Najeriya.

Ana kyautata zaton cewa akwai 'yan Najeriya fiye da 5,000 a Sudan da ke son a kwashe su zuwa gida, a ciki har da ɗalibai kimanin 3,500.

Za su yi tsawon sa'a 13 suna tafiya daga Khartoum kafin su sauka a Wadi Halfa mai ratar kilomita 30 daga kan iyakar Masar, daga nan kuma su ƙarasa Aswan a cikin Misira.

Dubban jama'a ne ke ci gaba da ficewa daga Sudan daidai lokacin da wata yarjejeniyar tsagaita ta tsawon sa'a 72 tangal-tangal, inda rahotanni ke cewa an ci gaba da jin rugugin bindigogi nan da can.

Hukumomin Masar sun ce aƙalla mutane fiye da dubu 10 ne suka tsallaka cikin ƙasar a tsawon kwana biyar tun bayan kaurewar faɗa tsakanin rundunar sojojin Sudan da mayaƙan rundunar masu kayan sarki ta RSF.

Wasu 'yan asalin Najeriya da suka shafe shaekaru da dama suna zaune a Sudan sun bi sahun ɗaliban ƙasar da suka je karatun jami'a a ƙoƙarinsu na kuɓuta daga faɗan da ake ci gaba da gwabzawa.

Wasu rahotanni na cewa nisan tafiyar 'yan Najeriyar zai iya ƙaruwa don kuwa da yiwuwar za su riƙa haɗuwa da sojoji da kuma jami'an tsaro masu bincike.

Abin da ya faru

Motocin bas-bas kimanin arba'in da shida ne hukumomin Najeriya suka ce sun tanada don kwashe ɗaliban, in ji Muhammad Nura Bello, shugaban ƙungiyar dalibai 'yan Najeriya a Sudan International University.

Babban Daraktan Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) da jami'an ofishin Jakadancin Najeriya a Masar da Ethiopia ne za su tarbi ƴan Najeriyar da suka baro Sudan ta titin mota.

Shugaban ɗalibai ya ce aikin kwashe ɗaliban ya zo a wani yanayi inda aka riƙa rige-rigen shiga motoci, wani lamari da ya yi yunƙurin haddasa kai ruwa rana.

A cewarsa, "ɗalibai kowa so yake ya tafi gida, a haka kuma akwai mazauna gari, waɗanda asalinsu ƴan Najeriya ne.

Kasancewar akwai ɓarkewar rigingimu da rashin tsaro, su ma suna son su wuce Najeriya", cewar shugaban ɗaliban.

"Samun labarin za a kwashe ƴan Najeriya zuwa gida, su ma kawai sai suka zo suka ce za su shiga, abin sai da ya kawo rigima tsakanin su da ɗalibai".

Faɗa ya ɓarke ne tsakanin dakarun manyan janar-janar biyu na Sudan.

Abdel Fattah al-Burhan, jagoran rundunar sojojin Sudan da kuma Mohammed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da suna Hemedti, shugaban dakarun kai ɗaukin gaggawa don tallafawa ayyukan tsaro wato RSF.

Da farko, mutanen biyu sun yi aiki tare. Sun yi wani juyin mulki - inda suka riƙa goyon bayan juna - amma yanzu an gan su a rana, faɗan wa ya fi ƙarfi iko tsakaninsu, na durƙusar da Sudan.

Dukkansu sun ba da gagarumar gudunmawa wajen murƙushe rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya a kan 'yan tawayen Darfur, wani yaƙin basasa a yankin yammacin Sudan da ya fara a shekara ta 2003.

Janar al-Burhan ya sau ɗaukaka da ƙarin girma har ya kai matsayin karɓar iko da rundunar sojojin Sudan a Darfur.

Hemedti ya taɓa zama kwamandan ɗaya daga cikin rundunonin sojojin sa-kai na Larabawa masu yawa da ake kira Janjaweed, waɗanda gwamnati ta ɗauko kuma ta hanyoyi masu cike da rashin imani suka murƙushe ƙungiyoyin 'yan tawayen Darfur waɗanda ba Larabawa ba.