Wane yanayi ake ciki a Iran bayan kai wa Isra'ila hari?

    • Marubuci, Jiyar Gol
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian World Affairs Correspondent

A karon farko, Iran ta kai wa Isra'ila hare-hare kai tsaye kuma daga cikin ƙasar ta. Ana dai kallon matakin a matsayin wata hanya da rundunar juyin juya hali ta Iran za ta bi domin ƙarfafa martabar da take da ita a tsakanin ƙasashen yankin, kuma wani matakin na yin gwajin ƙarfin Iran a fannin makaman nukiliya da kuma jirage marasa matuki.

An kafa rundunar ta IRGC ne shekara 45 da suka wuce domin kare tsarin dokar addinin musulumci da ake amfanin da ita, da kuma rage yawan da kuma tallafawa duk wani aiki na rundunar sojin. Tuni dai ƙungiyar ta yi suna a matsayin rundunar soji, kuma ƙungiyar siyasa da tattalin arziki.

Bayan hare-haren na ranar Asabar, mabiya rundunar suka shiga tituna ɗauke da tutar kasar Iran da falasdinawwa.

"Na gamsu da abin da matakin kai wa Isra'ila hari shi ne abin da ya fi dacewa domin hana ci gaba da kisan kwamandojin Iran, da kuma sauran su a" inji wata ƴar shekara ashirin da ƴan kai kuma mai goyon bayan gwamnatin Iran, cikin wani saƙon murya da ta aikewa BBC Persian.

Sai dai kuma, ƴan Iran da dama, masu sukar jamhuriyar musulumci sun ce kai wa Isra'ila hari da kuma abubuwan da suka biyo baya ba su wakiltar ra'ayoyin su.

"Mu ba ƴan jamhuriyar musulumci bane. Mu ne jama'ar Iran na asali. Mutanen Irna ma suna cikin rikici ne da wannan gwamnati. Ba mu son ƙulla ƙiyayya tsakanin mu da wata ƙasa, ko da kuwa Isra'ila ce. '' Inji wani matashi ɗan shekara 40, a cikin sakon da ya aikewa BBC Persian.

Wata mata ƴar shekara 50 ta bayyana damuwa a kan yadda harin zai iya tunzura yaƙi a yankin, ya kuma kai ga yin fito na fito tsakanin Iran da Isra'ila da kuma ƙawayen ta na Yamma.

Irin wannan matsaya ta samu karɓuwa idan aka yi la'akari da yadda darajar kuɗin Iran ke ƙara durƙushewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Tsoron harin ramuwa-dogayen layin mai da fargabar jama'a

Fargaba ta ƙaru a ranar Asabar, yayin da jama'ar Iran suka shiga tsoro don gudun kada Isra'ila da mayar da ƙawayen ta su martani. jama'a sun razana sosai ta yadda ake ta rige rigen siyan kayan abinci da man fetir da kuma sauran abubuwan buƙata.

An samu dogayen layin man fetir a gidajen mai da ke birnin Tehran da ma sauran manyan birane, yayin da jama'a suka cika manyan kantuna domin siyan kayan buƙata,

Duk da cewa Isra'ila ta yi Iƙirarin cewa ta daƙile kashi 99 cikin dari na makamai masu linzami da Iran ta harba mata, jami'an gwamnatoin Iran suna murna ne a kan abin da suka kira nasarar yin abin da ba a taɓa yi a can baya ba.

Babban hafsan sojin Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri, ya bayyana cewa daga cikin wuraren da suka kai harin akwai harda wata barikin sojin sama, inda jirgin saman inda kuma daga can ne jirgin Isra'ila samfarin F35s ya tashi har ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun Iran 7, a birnin Damascu.

Ya bayyana yaqinin cewa Iran ta cimma nasarar abin da ya sa ta kai wannann hari. Kuma shugaban Iran Ebrahim Raisi ya yi gargadi cewa duk wani yunƙuri na kai mata hari zai tilasta masa sake ƙaddamar da wasu ƙarin hare-hare.

Da alama yanayi ya canza zuwa na haɗin kai da sasanci a Iran tun bayn kai harin dare a ranar Asabar. jami'an soji da na ƴan kasuwa duk suna nuna jin dadin su kan harin na jiya.,

Yadda Iran ta bari har Isra'ila ta kammala sanya abubuwan kariya daga bama bamai, manuniya ce cewa itama Iran ba ta so harin nata ya yi barna ba.

Fafutukar nuna isa

Jama'ar Iran suna adawa da tura dakarun IRG zuwa wani wajen domin bayar da talagi.

A wajen wata zanga-zanga da aka yi kwannan nan a Iran, an riƙa rera wake cewa ''babu Gaza, babu Lebanon. na sadaukar da rayuwa ta ga Iran.

Ƴan Iran da dama sun haƙiƙance cewa maƙudan kuɗin da ake kashewa wajen horaswa da kuma ɗaukar nauyin dakarun, zai fi dacewa idan aka yi amfani da kudin ta hanyar da ta fi dacewa.

Yanzu haka Iran ta janyo wa kanta takunkumai. tattalin arziki ya durƙushe. Har masu ɗan rufin asiri a tsakanin jama'ar ƙasar suna matuƙar shan wahanar a kan abin da za su ci.

Muryoyin da ke fitowa daga Iran na nuni da cewa mutane ba su goyon bayan shirin gwamnati, musamman a kan batun yaƙi.

Lamarin ya canza sosai, ba kamar yadda a 1980s, miliyoyin ƴan Iran suka fito domin kare martabar ƙasar su, lokacin tana yaƙi da Irai.

Wani da aka yi yaƙin Iran da Iraqi da shi na wancan lokaci, wanda kuma yanzu haka ke fama da shanyewar jiki ya ce 'ba zan ƙara yin fada don kare kasar mu ba.

Iran tana da ƙarfin ƙaddamar da harin makami mai linzami da jirgin sama maras matuki, kuma tana da goyon bayan ƙungiyoyin shia, a Lebanon da Syria da Iraq da kuma Yemen. Amma da alama da gangan aka tsara cewa makaman yadda ba zasu yii ɓarna ba sosai a wannan karo.

Idan aka shiga yaƙi, jamhuriyar musulumci ta Iran za ta fafata ne ba kawai a fagen nuna ƙarfin soji ba, harma da karfin iko a fannin siyasa da faɗa a ji a auniya, ɓangaren da, kuma a wannan ɓangare Amurka tana goyon bayan Is1sra'ila.

Zanga-zangar 2022 bayan mutuwar Mahsa Amini, a hannun ƴan sanda, wani ƙarin manuniya ne game da raunin wannan gwamati.

Da yawa cikin masu ƙarfin faɗa a ji, a jamhuriyar musulumci ta Iran suna fargabar cewa Isra'ila da Amurka suna iya sake tunzura masu fita zanga-zanga a ƙasar.