'Duk da cin hancin da muka biya wajen rijistar zaɓe ba mu samu katin ba'

Wannan labari yana cikin jerin labaran da BBC Hausa za ta gabatar bayan neman jin ra'ayoyin ƴan Najeriya a manyan fannonin da suka fi shafi 'yan kasar.

Wannan shiri ne na musamman da BBC ta tsara dangane shirin manyan zaɓukan da ƙasar za ta gudanar daga watan Fabrairun 2023.

Fannonin da za a yi duba a kai din su ne na tsaro da ilimi da tattalin arziki da lafiya da kuma cin hanci.

Daruruwan mutane ne suka aiko da labaransu, kuma za mu dinga wallafa 25, ɗaya a kowace rana daga 10 ga Oktoban 2022.

Cin hanci da rashawa na cikin manyan matsalolin da suka fi addabar ƙasashen duniya, musamman a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya.

Rahoton haɗin gwiwa da ƙungiyoyin CISLAC da Transparency International suka fitar kan cin hanci da rashawa na 2021 ya nuna Najeriya a matsayi na 154 daga cikin ƙasa 180 da suka fi fama da matsalar.

Wane irin hali kuke zaton za ku shiga idan aka ce ka biya kuɗi a inda ya kamata a yi muku abu kyauta kuma ba ku samu abin ba daga ƙarshe?

'Raina ya yi matuƙar ɓaci'

Matashi Abdulrahman Adam, mai shekara 25 a yanzu ya ƙagu ya kai shekara 18 da haihuwa don ya samu damar fara jefa ƙuri'a a zaɓuka a Najeriya. Sai dai ya gamu da ɓacin rai da karayar zuciya lokacin da ya je yin rajistarsa ta farko a 2015.

"Saboda garinmu ba yana lungu ne, sai dai wani ɗan siyasa ya kawo muku masu yin rajista su zo su yi muku, muna zuwa aka ce sai mun biya kuɗi," in ji matashin haifaffen garin Tella na Ƙaramar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba.

Abdulrahman ya ce shi da abokansa biyu suka je yin rajistar kuma aka ce sai sun biya N500 kowannensu.

"Mu biyu ne muka biya amma shi ɗayan ba shi da kuɗi, bai yi rajistar ba.

"Lokacin da muka je heedikwatar ƙaramar hukuma sai don mu karɓi katin zaɓen namu sai aka ce mana wai ya ƙone saboda ba a nan muka yi ba."

Wannan lamari ya sa Abdulrahman da abokansa biyu ba su zaɓi wanda suke so ba a 2015 - shekarar da ya kamata su fara jefa ƙuri'a.

"Lokacin da na biya kuɗin ban ji komai ba saboda ina murna zan samu damar zaɓen wanda nake so. Raina ya yi matuƙar ɓaci gaskiya lokacin da aka ce ba za mu samu katin ba.

"Sai a 2019 na samu dama na yi katin zaɓen. Ɗaya daga cikin abokan nawa ma ya samu ya yi, amma ban sani ba ko ɗayan ya yi."

Yanzu haka Abdulrahman na zaune a birnin Benin na Jihar Edo da ke kudancin Najeriya.