Vinicius Junior ya zama gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na FIFA, 2024

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil da Real Madrid, Vinicius Junior, ya lashe kyautar ɗan ƙwallon ƙafa mafi ƙwazo na Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) na shekara ta 2024.

Haka nan kuma Aitana Bonmati ta Barcelona ita ce ta lashe irin wannan kyautar a ɓangaren mata, karo na biyu a jere.

Vinicius ya zura ƙwallo a wasan ƙarshe na gasar zakarun nahiyar Turai na wannan shekara, sai dai bai samu nasarar lashe kyautar ɗan wasa mafi ƙwazo ba a kyautar Ballon d'Or mai matuƙar farin jini.

An soki ƙungiyar Real Madrid saboda ƙaurace wa bikin bayar da kyautar ta Ballon d'Or.

Wannan ne karon farko da Vinicius ya lashe kyautar.

Ballon d'Or da kuma Fifa Best Awards suna kyaututtuka mafiya kwarjini a harkar ƙwallon ƙafa ta duniya.

Lionel Messi ne ya lashe kyautar karo biyu a baya, sai kuma Lewandowski, wanda ya lashe guda biyu gabanin Messi.

Bonmati ta taimaka wa ƙungiyarta wajen lashe kofuna uku na cikin gida da kuma kofin zakarun nahiyar Turai na mata a kakar wasanni da ta gabata.

Haka nan ta zura ƙwallo a wasan kusa da na ƙarshe da kuma na ƙarshe lokacin da ƙasarta Sifaniya ta lashe gasar Nations League a watan Fabarairu.

Haka nan kuma kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ne ya lashe kyautar mai horas da ƴan wasa mafi ƙwazo na hukumar ta Fifa na wannan shekara.

Ancelotti ya yi zarra ne bayan doke Pep Guardiola na Man City, da Xabi Alonso na Bayer Leverkusen, da Lionel Scaloni na Argentina da kuma Luis de la Fuente na Sifaniya.