Ya kamata a sauya salon yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya - Ƴan majalisa

'Yan majalisar wakilan Najeriya da suka fito daga arewa maso yammacin ƙasar, sun bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaron kasar su sauya salon yadda suke tunkarar matsalar tsaro a yankin.

'Yan majalisar sun ce duk da cewar bangarorin da ke yaki da matsalar tsaron na aiki tare, amma akwai bukatar samun fahimtar juna musamman a bangaren gwamnoni da tarayya don ganin an ci nasara a yaki da ‘yan bindigar da suka addabi yankin.

Hon. Aminu Sani Jaji, na daga cikin ‘yan majalisar yankin da suka gudanar da taro a kan wannan bukata a Abuja babban birnin tarayar kasar, kuma a tattaunawarsa da BBC ya ce, yankin arewa maso yamma shi ne ya fi yawan al’umma da kuma fuskantar matsalar tsaro a yanzu gashi kuma anan ne aka fi noma.

Ya ce,”Babban abin da ya damemu shi ne yadda matsalar tsaro ta rage yadda ake noma a wannan yanki namu, abin da ake nomawa ada kafin matsalar tsaro a yanzu ko kwatansa ba a nomawa saboda akwai wurare da dama da ba a nomanma kwata-kwata.”

Dan majalisar ya ce bisa la’akari da rashin bayar da gudunmuwar yankin ta fuskar abincin da ake nomawa ya sa ba sa jin dadin abin da ke faruwa, kuma ba komai ya janyo hakan ba illa rashin tsaro a yankin.

“A yanzu zamu yi kokari mu ga mun zauna tare da jami’an tsaro, da kuma idan mun samu dama da shi kansa shugaban kasa don mu tabbatar da cewa lallai an kawo karshen wannan matsala musamman tashe-tashen hankula da kashe-kashe da dai makamantansu.”

Hon. Aminu Sani Jaji, ya ce akwai matakan da ya kamata a dauka don kawo karshen matsalar tsaron, na farko shi ne matakin karfin soji da ya kamata ace an yi amfani da shi da kuma matakin zama da masu ruwa da tsaki a kalli mahangar da za a bi wajen magance matsalar.

Dan majalisar ya ce hadin kai a tsakanin jihohin yankin ma na da matukar amfani saboda ta hakan ne za a san yadda za a tunkari matsalar.

Ya ce,”Hadin kai tsakanin gwamnonin yankin da ma gwamnatin tarayya na da muhimmancin gaske domin idan babu hadin kai to gaskiya ba lallai a samu abin da ake so ba, kuma suma jami’an tsaro idan da hadin kan aikinsu zai zo da sauki.”

“Mu a matsayinmu na wakilai daga yankin arewa maso yamma, mun yi kokari mun tattauna da wasu gwamnonin yankin domin lalubo bakin zaren matsalar.” In ji shi.

Har yanzu dai matsalar tsaro na ciwa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya, kuma duk da kokarin da gwamnatin kasar ke cewa tana yi wajen shawo kan matsalar, har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin jihohi kamar su Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Neja, har yanzu ‘yan fashin daji na ci gaba cin karensu ba babbaka.