Champions League: Wasannin da za a yi ranar Laraba

Asalin hoton, Getty Images
Za a ci gaba da wasannin cikin rkuni a wasa na biyu a Champions League ranar Laraba.
Wasa tara za a buga a babbar Gasar tamaula ta Turai a rukuni hudu har da kwantai tsakanin Rangers da Napoli.
Za a barje gumi a rukuni na biyar da na shida da na bakwai da kuma na takwas.
Mohammed Abdu ya hada rahoto kan wasannin da za a yi.
Rukuni na biyar

Asalin hoton, Getty Images
- GNK Dinamo Zagreb
- Red Bull Salzburg
- AC Milan
- Chelsea
Wasannin da za a buga:
- AC Milan da Dinamo Zagreb
- Chelsea da Red Bull Salzburg
Wannan shi ne wasa na uku da Milan da Dinamo Zagreb za su fuskanci juna a Champions League, inda Milan ta lashe dukkan karawa biyun.
Wasannin da suka buga a tsakaninssu
2000/2001
Champions League Talata 22 ga watan Agustan 2000
- Dyn Zagreb 0 - 3 Milan
Champions League Laraba 9 ga watan Agustan 2000
- Milan 3 - 1 Dyn Zagreb
Daya karawar ita ce tsakanin Chelsea da Red Bull Salzburg, wannan shi ne karon farko da za su fuskanci juna.
Chelsea za ta buga wasan da sabon koci, Graham Potter, wanda ya maye gurbin Thomas Tuchel.
Chelsea ta sallami Tuchel a makon jiya, bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a 1-0 a gidan Dinamo Zagareb a wasan farko a rukunin farko
Sakamakon wasannin da aka buga:
- Dinamo Zagreb 1 : 0 Chelsea
- Red Bull Salzburg 1 : 1 AC Milan
Rukuni na shida

Asalin hoton, Getty Images
- Shakhtar Donetsk
- Real Madrid CF
- RB Leipzig
- Celtic Glasgow
Wasannin da za a buga:
- Shakhtar Donetsk da Celtic Glasgow
- Real Madrid da RB Leipzig
Shakhtar za ta karbi bakuncin Celtic, kuma karo na biyar da za su kece raini a tsakaninsu, kowacce ta ci wasa bibiyu.
Jerin wasannin da suka fafata a tsakaninsu:
2007/2008
Champions League Laraba 28 ga watan Nuwambar 2007
- Celtic 2 - 1 Shakhtar
Champions League Talata 18 ga watan Satumbar 2007
- Shakhtar 2 - 0 Celtic
2004/2005
Champions League Talata 2 ga watan Nuwambar 2004
- Celtic 1 - 0 Shakhtar
Champions League Laraba 20 ga watan Oktoban 2004
- Shakhtar 3 - 0 Celtic
Daya karawar kuwa RB Leipzig za ta ziyarci Real Madrid, kuma wannan shi ne karon farko da za su buga Gasar Zakarun Turai a tsakaninsu.
Sakamakon wasannin da aka buga:
- RB Leipzig 1 : 4 Shakhtar Donetsk
- Celtic Glasgow 0 : 3 Real Madrid
Rukuni na bakwai
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Asalin hoton, Getty Images
Wasu labaran da suka shafi City da Dortmund
Mai tsaron bayan Manchester City, John Stones ya murmure zai iya buga wasan da City za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund ranar Laraba.
Sai dai har yanzu Aymeric Laporte na jinyar rauni a gwiwar kafa tare da Kyle Walker da bai warke ba.
Erling Haaland da Sergio Gomez da kuma Manuel Akanji za su fuskanci tsohuwar kungiyarsu Borussia Dortmund ranar Laraba.
Dan kwallon tawagar Ingila, Jude Bellingham ya shirya buga wa Dortmund tamaula, wadda ke fatan Thorgan Hazard zai kasance kan ganiya.
An sauya dan wasan tawagar Belgium a karawar da Dortmund ta ci Copenhagen 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a Champions League.
Kociyan Dortmund, Edin Terzic na fatan Karim Adeyemi da Donyell Malen za su murmure daga raunin da suka yi jinya, domin su buga masa wasan da za a yi a Etihad.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
- Manchester City
- Borussia Dortmund
- FC Kobenhavn
- Sevilla
Wasannin da za a buga:
- Manchester City da Borussia Dortmund
- FC Kobenhavn da Sevilla
City da Dortmund sun kara sau hudu a Champions League, inda City ta ci biyu, Dortmund ta yi nasara a daya da canjaras daya.
Jerin wasannin da suka buga
2020/2021
Champions League Laraba 14 ga watan Afirilun 2021
- B Dortmund 1 - 2 Man City
Champions League Talata 6 ga watan Afirilun 2021
- Man City 2 - 1 B Dortmund
2012/2013
Champions League Talata 4 ga watan Disambar 2012
- B Dortmund 1 - 0 Man City
Champions League Laraba 3 ga watan Oktoban 2012
- Man City 1 - 1 B Dortmund
Daya wasan shi ne na FC Copenhagen da Sevilla ba su taba karawa a tsakaninsu ba.
Sakamakon wasannin da aka buga:
- Borussia Dortmund 3 : 0 FC Kobenhavn
- Sevilla 0 : 4 Manchester City
Rukuni na takwas

Asalin hoton, Getty Images
- Benfica
- Paris Saint-Germain
- Juventus FC
- Maccabi Haifa
Wasannin da za a buga:
- Juventus da Benfica
- Maccabi Haifa da Paris Saint-Germain
Wannan shi ne wasa na biyar da za a kece raini tsakanin Juventus da Benfica, inda Benfica ta yi nasara a uku da canjaras daya.
Wasannin da suka fafata a tsakaninsu:
2013/2014
Europa League Alhamiss 1 ga watan Mayun 2014
- Juventus 0 - 0 Benfica
Europa League Alhamis 24 ga watan Afirilun 2014
- Benfica 2 - 1 Juventus
1967/1968
European Cup Laraba 15 ga watan Mayun 1968
- Juventus 0 - 1 Benfica
European Cup Alhamis 9 ga wwatan Mayun 1968
- Benfica 2 - 0 Juventus
Daya karawar ita ce tsakanin Maccabi Haifa da Paris Saint-Germain, karon farko da za su fuskanci juna a wasan Zakarun Turai.
Sakamakon wasannin da aka buga:
- Paris Saint-Germain 2 : 1 Juventus
- Benfica 2 : 0 Maccabi Haifa
Idan anjima za a yi gumurzu tsakanin Rangers da Napoli.
Wannan shi ne karon farko da Glasgow Rangers da Napoli za su fuskanci juna a Gasar Zakarun Turai.
Ranar Talata ya kamata a buga wannan wasan, amma hukumar kwallon kafar Turai Uefa ta dage karawar zuwa Laraba.
Hakan ya biyo bayan zaman makokin rasuwar Sarauniya Elizabeth II, wanda ba za a samu jami'an tsaron da za su kula da fafatawar ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3










