Yadda ake harƙallar satar littafai masu muhimmanci a duniya

BBC
    • Marubuci, Nina Nazarova
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
  • Lokacin karatu: Minti 5

A watan Afrilun 2022 ne wasu mutane guda biyu suka shiga ɗakin karatu na Jami'ar Tartu da ke Estonia, inda suka buƙaci ganin wasu littattafai guda takwas na wasu fitattun marubutan ƙarni na 19 guda biyu Alexander Pushkin da Nikolai Gogol.

Mutanen biyu sun iya magana da harshen Rasha ne, inda suka ce ɗaya daga cikin su yana wani bincike ne na musamman.

Bayan kimanin wata uku, sai ma'aikatan ɗakin karatu suka lura an sace takardu guda biyu, an musanya su da na bogi. Sai bayanan ɗakin karatun suka nuna cewa mutanen biyu ne ƙarshen waɗanda suka taɓa littattafan.

Nan ne ma'aikatan ɗakin karatun suka yi maza-maza suka je duba sauran littafan marubutan guda shida, inda suka lura dukkansu an musanya su.

Bayan makonni, sai aka sace wasu littattafai guda goma da suke da wahalar samu a ɗakin karatu na Jami'ar Tallinn da ƙasar ta Estonia.

Haka aka yi wata 18 ana sace wasu gomman littattafai masu muhimmanci a ɗakunan karatu na ƙasashen turai kamar su Finlanda da Switzerland da Faransa.

A wasu wuraren, an sace na asalin ne, aka musanya da na bogi. A wasu wuraren kuma an sace su ne baki ɗaya.

Hakan ya sa hukumar Europol tabbatar da bin doka da oda a ƙasashen turai ta ƙaddamar da bincike da ta kira da suna Operation Pushkin.

A binciken ne aka tura sama da ƴansanda 100 suka riƙa zirya a ƙasashen duniya domin neman littattafan da suka ɓace, inda a ƙarshe aka kama mutum 9 da ake zargi, kuma dukkansu ƴan ƙasar Girka.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya bayyana wa BBC cewa ji yake kamar wani 'maye' idan ya ga littafi
Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya bayyana wa BBC cewa ji yake kamar wani 'maye' idan ya ga littafi

'Mayen littafi'

Wanda aka fara kamawa shi ne Beqa Tsirekidze mai shekara 48. An gabatar da shi a kotu, inda aka same shi da aikata laifuka uku a ƙasashe biyu - Latvia da Estonia - ciki har da sace littattafai a ɗakunan karatu na jami'o'in Tartu da Tallinn.

Yanzu Tsirekidze yana ɗaure a gidan yari bayan an yanke masa hukuncin shekara uku da wata uku a Estonia, gidan yari ke ba fursunoni damar zanta wa da ƴanjarida.

Daga can ne Tsirekidze ya shaida wa BBC ya shiga harƙallar sace littafai ne, sai su sauya su da na bogi domin su sayar da na ainihin domin ciyar da iyalansa.

"Ni tamkar maye ne a batun littattafai. Da na riƙe littafi a hannuna zan iya faɗa maka farashinsa," in ji shi.

Tsofaffin littattafai masu daraja na ɓacewa a ɗakunan karatun jami'o'i
Bayanan hoto, Tsofaffin littattafai masu daraja na ɓacewa a ɗakunan karatun jami'o'i

'Sata mafi girma bayan yaƙin duniya na biyu'

A watan Oktoban 2023, wasu ma'aurata matasa suna zaune a ɗakin karatu na Jami'ai Warsaw suna ta shawagi suna duba littafai, har mijin yana sumbantar matarsa.

An kasance ana naɗar abubuwan da ke wakana ne ta na'urar sirri da ke ɗakin karatun.

Mijin mai suna Mate, ɗa ne a wajen Tsirekidze tare da matarsa Ana Gogoladze. Daga bisani an kama su da laifin sace littafan da darajarsu ta kai $100,000 daga ɗakin karatun.

Akwai ɗimbin littattafai a ɗakin karatun na tarihin ƙasashen Soviet, waɗanda aka daɗe ana mamakin yadda suka sha a rigimar Warsaw na 1944, inda har ginin aka ƙone shi.

Jimilla a cikin shekara, aƙalla littattafai masu daraja da suke wahalar samu guda 73 aka sace, waɗanda kuɗinsu ya kai $600,000 daga ɗakin karatun, kuma har yanzu akwai ɓarayin da ba a kama ba.

"Wannan sata ce mafi girma da aka yi tun bayan yaƙin duniya na biyu," in ji Farfesa Grala.

Mate Tsirekidze da matarsa Ana Gogoladze
Bayanan hoto, Mate Tsirekidze da matarsa Ana Gogoladze

Ma'aikatun ɗakin karatun yawanci ba sa gane an musanya littafan, "akwai tambarin littafin, kuma ana musanyawa da littafai daidai girman wanda aka sace, babu wani giɓi da ake ragewa," in ji Farfesa Grala.

"Akwai alamu ɓarayin sun ƙware, kuma a shirye suka zo," in ji Grala.

'Wata ƴar alama'

A ƙa'ida, dukkan littafai ana saka musu tambari, amma yanayin girmansu na bambanta. Misali a Rasha an saka manyan tambari, in ji Pyotr Druzhnin mai tattara littafan da suka da wahalar gani tare da adana su.

Wasu lokutan ɗakunan karatu sukan sayar da littafai ta hanyar gurza su wasu lokutan saboda ƙarancin fili, kamar yadda aka yi a ƙasar Soviet.

Haka kuma yana da wahala a gane ko tambarin na ƙarni 18 ne ko na ƙarni na 19, kamar yadda Druzhinin ya bayyana.

Wasu lokutan tambarin kan iya ɓacewa ko kuma a cire shafukan tambarin a musanya su, wanda da wahala a gane idan ba masani ba.

Yawanci tsofaffin littafai babu tambari saboda lokacin da aka kawo su ba a fara amfani da tambarin ba.

Wasu lokutan, ɓarayin sukan sace littafan ba tare da musanya su ba
Bayanan hoto, Wasu lokutan, ɓarayin sukan sace littafan ba tare da musanya su ba

Dubban daloli

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Za ka ga ana sanya masu gadi sama da 22 domin kula da rabin kilo na zinare da ya kai darajar dala 600,000. Amma littafai biyu da suka kai darajar 60,000 sai dai ka tsince su a ɗakunan karatu a turai babu wani mai gadi sai wataƙila wata dattijuwa, kuma ba tare da na'urar naɗar bidiyo ta sirri ba," in ji Tsirekidze a zantawarsa da BBC daga gidan yarin Estonia.

Druzhinin ya ce littafai masu daraja da suke da wahalar samu na Rasha sun fara tsada ne a tsakanin 2022 da 2024.

Misali, an kama wani ɗan ƙasar Girka mai suna Mikhail Zamtaradze da laifin sace wasu littafai masu daraja daga Jami'ar Vilnius da ke ƙasar Lithuana a watan Yuni.

Zamtaradze ya yi rajista ne a ɗakin karatun da takardun bogi, inda ya karɓi littafai masu daraja da suke wahalar samu guda 17, sai ya musanya guda 12 daga ciki da na bogi, sannan ya sace guda biyar.

Jimilla kuɗin takardun da ya sace ta kai dala $700,000.

Zamtaradze ya bayyana a kotu cewa ta taɓa sace littafai daga Moscow ya tura ta motar bas zuwa Belarus, inda aka tura masa cryptocurrency da darajarsu ta kai dala $30,000.

Zamtaradze ya yi iƙirarin cewa yana sayar da littafan ne zuwa ga wasu cibiyon gwanjon kayayyaki.

Wani tsohon littafi da aka musanya da na asalin da aka sace
Bayanan hoto, Wani tsohon littafi da aka musanya da na asalin da aka sace

Ba wannan ba ne karon farko da aka zargi cibiyoyin gwanjon kayayyki da hannu a harƙalallar.

An sayar da aƙalla littafai huɗu na Jami'ar Warsaw a cibiyar gwanjon kayayyaki na LitFund - a Moscow a ƙarshen 2022 da 2023, in ji Farfesa Grala.

BBC ta tattara wasu hotu daga shafin intanet game da littafan da ake magana a kai, daga ciki akwai The Tales of Ivan Belkin na Pushkin, wanda ke ɗauke da tambarin ƙarni na 19 a lokacin da ake gwanjonsa.

Daraktan LitFund, Sergei Burmistrov, ya ce suna aiki bisa doka da oda na gwamnatin Rasha, kuma ba sa gwanjon littafin da ke ɗauka da tambarin gwamnatin wata ƙasa.

Ya ƙara da cewa masu littafin suna saka hannu a takardar yarjejeniyar tabbatar da kasancewar littafinsu ne, sannan sai masana sun tsakace bayanan kafin su yi gwanjonsa.

Har yanzu dai ba a kammala aiki na musamman na Operation Pushkin saboda har yanzu akwai wanda ake zargi da ke fuskantar shari'a a Faransa bisa zarginsa da satar littafai a wasu ɗakunan karatu a can.