Barcelona na shirin sayen Rashford, Mainoo na daf da barin Man United

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona za ta sayi Marcus Rashford daga Manchester United kan yarjejeniya ta dindindin a ƙarshen zaman aronsa, amma sai ɗan wasan gaban na Ingila mai shekara 28 ya amince da tayin albashin ta. (Talksport)
Ficewar ɗan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo daga Manchester United a watan Janairu ya kusanto, yayin da Napoli ta ƙara ƙaimi wurin yunƙurin ɗaukar aron ɗan wasan mai shekara 20. (Team Talk)
Wakilin Niclas Fullkrug ya ce "zai yi kyau" idan ɗan wasan na Jamus mai shekara 32 ya bar West Ham. (TOMorrow Business Podcast).
Ɗan wasan bayan Arsenal da Faransa William Saliba, mai shekara 24, ya ce ya yi nazarin yiwuwar komawa Real Madrid kafin ya yanke shawarar ƙulla sabuwar yarjejeniya da Gunners a watan Satumba. (Sports Illustrated)
Newcastle United na nazari kan ɗan wasan tsakiyar Atalanta Ederson, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan ƙasar Brazil Joelinton, mai shekara 29. (The I)
Liverpool ta shiga jerin ƙungiyoyin da ke fafatukar daukar ɗan wasan River Plate ɗan ƙasar Argentina Ian Subiabre mai shekara 18 . (Fichajes)
Chelsea da Manchester United na sha'awar sayen ɗan wasan gaban Brazil Vitor Roque, mai shekara 20, daga Palmeiras. (Mundo Deportivo)
Tsohon kocin Manchester United Erik ten Hag yana cikin ƴan takarar da Wolves ke zawarci domin maye maye gurbin Vitor Pereira a matsayin kocinta. (Athletic)
Ɗan wasan tsakiya na ƙasar Sifaniya Oriol Romeu, mai shekara 34, zai koma tsohuwar ƙungiyarsa Southampton bayan ya soke kwantiraginsa da Barcelona. (Sport)
Ɗan wasan Canada Jonathan David, mai shekara 25, zai iya komawa Tottenham ko Bayern Munich a watan Janairu bayan ya yi fama da rashin tagomashi a Juventus tun lokacin da ya koma kulob ɗin na Serie A a bazarar da ta gabata. (Sky Sports)
A yanzu dai tsohon kocin Roma Daniele de Rossi ne ke kan gaba a jerin sunayen waɗanda za su iya karɓar ragamar horas da Genoa, bayan sallamar Patrick Vieira da aka yi a ƙarshen makon da ya gabata. (Football Italia)











