Waɗanne ƙungiyoyin mayaƙa ne Isra'ila ke taimako domin yaƙi da Hamas a Gaza?

Hamas ta yi yunƙurin kwace iko da Gaza amma tana fuskantar ƙalubale.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hamas ta yi yunƙurin kwace iko da Gaza amma tana fuskantar ƙalubale
    • Marubuci, Monitoring section
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza ta buɗe wata sabuwar ƙofar rikicin cikin gida, inda ta sa aka gane ashe akwai wasu ƙungiyoyin ƙabilu masu riƙe da bindiga da suke samun goyo bayan Isra'ila wajen faɗa da Hamas.

A watan Yuni, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarar "tattaro wasu ƙabilu domin yaƙi da Hamas a Gaza."

Daga cikin mayaƙan akwai ƙabilar Daghmash, wadda aka alaƙanta da kashe fitaccen ɗanjaridan Falasɗinu, Saleh Jaafaravi.

Rahotanni na cewa yawancin mambobin ƙabilun tsofaffin ƴan ƙungiyar Fatah ne ko kuma jami'an gwamnatin Falasɗinu.

Ƙungiyoyin nan sun ƙara ƙarfi a cikin shekara biyu da aka yi ana gwabza yaƙi, kamar yadda masanin tsaro a yankin ya bayyana wa kafar Al-Mudoun ta Lebanon.

Amma wata jarida a London ta Asharq Al-Awsat ta kalato daga wasu majiyoyi na "kusa da Abu Shabab," cewa ƙungiyar na da ɗaruruwan mayaƙa, kuma suna biyan su albashi mai tsoka.

Waɗanne ƙungiyoyi ne aGaza?

A yanzu haka dai akwai ƙungiyoyi da suke Zirin Gaza, ɗaya daga ciki tana da alaƙa da da Yasser Abu Shabab kuma ta fi ƙarfi a kudancin birnin Rafah.

Akwai wata ta "Al-Qawat Al-Shaabiyyah" da ake kira 'The Popular Forces', da aka ce tana da alaƙa da Abu Shabab. Jagoranta shi ne Ashraf al-Mansi kuma ta fi ƙarfi a arewacin Gaza, ciki har da Beit Lahia da Jabalia.

Hamas ta taɓa kama Yasser Abu Shabab bisa zarginsa da aikata manyan laifuka da wasu laifuka.

Ana dai cewa Isra'ila ce take ba ƙungiyoyin makamai, kuma kafofin sadarwa da dama sun tabbatar da cewa lallai suna da alaƙa da Isra'ila.

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa Abu Shabab ce kan gaba wajen sace kayayyakin agaji. An ce suna da mayaƙa sama da 100, kuma rahotanni na cewa daga Isra'ila suke samun makamai.

Wuraren da suka fi ƙarfi

Kamar yadda kafar labarai ta Iram News ta ruwaito, akwai wata ƙungiyar a ƙarƙashin Rami Hales da ke da ƙarfi a Zirin Gaza, kuma tana da gomman mambobi ƙabilar Hales, waɗanda daga cikin su akwai ƴan ƙungiyar Fatah. Kafar Iram ta ruwaito cewa ita ce ƙungiyar da ta fi tsari a birnin.

Ta ukun da Aram News ta ruwaito ita ce wadda ke ƙarƙashin Hesam Astel da ke da ƙarfi a birnin Khan Younis.

Akwai wata ƙungiya kuma da ke ƙarƙashin Yasser Hanidaq da ke da gomman mambobi da suka fice daga ƙungiyar Fatah, sai kuma mayaƙan ƙabilar Dagmash da ke samun goyon bayan sojojin Isra'ila.

Su wane ne Hossam Estal da Rami Hales?

Hussam Astel tsohon babban hafsan tsaro ne na Falasɗinu da ke jagorantar ƙungiyar mayaƙa a Khan Younis a kudancin Zirin Gaza.

Rami Adnan Halas mai shekara 46 tsohon jami'in Falasɗinu ne kuma mamba a ƙungiyar Fatah. Ya ce yana jagorantar ƙungiyar da ake kira da "People's Defense Forces" ko kuma Qawyat al-Difa' al-Sha'bi a Gaza.

A ranar 7 ga Oktoba, ya shaida wa kafar Arabic Network mai suna "Jasour News" cewa akwai kusan mutum 500 a yankin da yake da iko.

Ina ƙungiyoyin suke a lokacin yaƙi?

Bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila, sai aka fara raɗe-raɗin makomar Abu Shab.

Daga baya sai kafar Rai al-Youm ta Landan ta ruwaito cewa "sojojin Isra'ila sun saki wakilinsu na sirri Abu Shabab da mutanensa."

Kafar intanet ta The Al-Madin ta ruwaito a ranar 14 ga Oktoba daga wani masanin tsaro cewa akwai "wasu ƙungiyoyin mayaƙa a yankin da suke samun tallafi daga ƙsashen waje."

Ƙungiyoyin suna fafatawa?

Akwai rahotannin da ke cewa waɗannan ƙungiyoyin suna da alaƙa da juna a Gaza.

Akwai abubuwa biyu da suke tarayya da su: Samun goyon bayan Isra'ila da alaƙar wasu daga cikinsu da ƙungiyar Fatah movement.

Jaridar The Times of Israel ta ruwaito cewa akwai alaƙa tsakanin ƙungiyoyin Abu Shabab da Astel.

Me kafofin sadarwa na Isra'ila ke cewa kan ƙungiyoyin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jaridar The Israeli Kan ta ruwaito cewa a ƙarshen makon jiya ma an gwabza tsakanin Hamas da mayaƙan ƙungiyoyi a yankin Sabra, inda mayaƙan Dagmash suka kai farmakin da suka kira a "ramakon gayya"

Kafar Ynet ta ƙasar Isra'ila ta ruwaito a ranar 9 ga Oktoba cewa tun bayan kashe wasu jagororin Hamas, sai hare-haren ƙungiyoyin da suke samun goyon Isra'ila suka ƙara yawa.

Kafar ta intanet ta ruwaito daga Abu Shabaab a Rafah cewa, "muna murna da tsagaita wuta, yanzu kuma za mu fatattaki ta'addanci da yaƙi daga Gaza."

Ynet ta ƙara da cewa a yunƙurin Hamas na hana ƙungiyoyin nan ƙara ƙarfi, mayaƙanta sun yi yunƙurin kashe Yasser Abu Shabab, amma ba ta samu nasara ba.

Shi ma Abu Shabab ya bayyana a wata tattaunawarsa da kafar Ynet a ranar 12 ga Oktoba cewa, "yanzu Hamas ba ta da ƙarfi, kuma ta kusa karyewa."

A cikin ƴan kwanakin nan, an samu rahoton da ke nuna cewa akwai rigima tsakanin Hamas da ƙabilar Al-Majida da ke Khan Yunis.

Hussam Astel, shugaban ƙabilar Al-Majida ya shaida wa Ynet a ranar 12 ga Oktoba cewa "yana ganawa da wasu ƙasashen yamma, ciki har da Amurka da ma Isra'ila," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa burinsa "mutane su samu zaman lafiya kamar yadda suke kafin harin 7a ga Oktoba."

Kafar Ynet ta nanata cewa dukkan ƙabilun nan suna samun goyon bayan Isra'ila, kuma ƙasar ta sha yunƙurin amfani da su wajen rabon kayayyakin agajin gaggawa a zirin.

Ricikin cikin gida

Ynet ta ruwaito daga wata majiya cewa kawo ƙarshen yaƙi da Isra'ila a Gaza ba shi ba ne ƙarshen yaƙin cikin gida a zirin, inda ta ce za a ci gaba da fafata rigima tsakanin Hamas da sauran ƙungiyoyi.

Jaridar da ke rahoto kan harkokin soji Ma'ariv ta ruwaito a ranar 11 ga Oktoba cewa, "babban sirrin Isra'ila shi ne ƙara ƙrfi, kuma jami'an tsaronta na taimakon ƙabilun Gaza."

Jaridar ta ce Isra'ila na taimakon ƙungiyoyin domin su yi ƙarfin da za su iya yaƙi da Hamas, duk da cewa babu tabbacin irin tallafin da ƙasar take ba ƙungiyoyin har zuwa yanzu.

Fassarar Mariam Mjahid, sannan Ambia Hirsi ta tace.