Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dortmund da Juve da Milan na son Rashford, City kuwa Marmoush
Borussia Dortmund da Juventus sun bi sahun AC Milan wajen duba yuwuwar sayen Marcus Rashford, wanda Manchester United ke son rabuwa da shi. (Sky Sports)
Ita kuwa Manchester City tana son sayen dan wasan gaba na Masar ne Omar Marmoush, mai shekara 25, wanda kungiyarsa, Eintracht Frankfurt ta Jamus ta yi masa kudi fam miliyan 50. (Espn)
To amma har yanzu City ba ta gabatar wa da Eintracht wani tayi a kan Marmoush ba. (Sky Germany)
Chelsea na kan gaba a masu son sayen Kobbie Mainoo, dan wasan tsakiya dan Ingila mai shekara 19, wanda tattaunawarsa da Manchester United kan kwantiragi ta ci tura. (Mail)
Mainoo, wanda sai a 2027 kwantiraginsa zai kare da Manchester United bai amince da tayin da kungiyar ta yi masa da farko ba. (Manchester Evening News)
A shirye United take ta saurari tayin da ya dace a kan 'yanwasanta da suka hada da
Mainoo, da Alejandro Garnacho dan Argentina mai shekara 20 da ke wasan gaba a gefe da dan gabanta Rasmus Hojlund, dan Denmark mai shekara 21. (Guardian)
Nottingham Forest na tattaunawa domin tsawaita kwantiragin dan bayanta na Brazil Murillo, mai shekara 22, wanda kwantiraginsa na yanzu zai kare a 2028. (Athletic)
Palmeiras na son sayen dan wasan tsakiya Andreas Pereira, dan Brazil mai shekara 29, amma har yanzu ba su cimma yarjejeniya da Fulham ba. (Fabrizio Romano)
Manchester United na son sayen dan bayan Hungary Milos Kerkez to amma farashin fam miliyan 40 da Bournemouth ta yi masa ka iya hana United cinikin dan wasan mai shekara 22. (Teamtalk)
Borussia Dortmund na sa ido a kan dan wasan tsakiya na Chelsea, Carney Chukwuemeka, dan Austria da Ingila mai shekara 21. (Sky Germany)
Arsenal na son dan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22, to amma ba za ta iya cinikin dan Sifaniyan ba a wannan watan saboda matsalar kudi. (Talksport)
Southampton na sa ran samun tayin da bai kai farashin da ta yi wa dan bayanta, Kyle Walker-Peters dan Ingila mai shekara 27, wanda kwantiraginsa zai kare a wannan bazarar, ba a wannan watan. (Football Insider)