Da gaske ne al'ummar Igbo ba sa sayar da fili ga wasu ƙabilun?

Asalin hoton, BBC/Getty Images
An fara samun yaɗuwar labarai a shafukan sada zumunta bayan da wani ɗan jarida na gidan talabijin na Arise, Reuben Abati ya yi magana kan yadda 'yan ƙabilar igbo - da ke zaune a yankin kudu maso gabashin Najeriya - ke sayar da filaye.
Cikin wani shiri da ya gabatar a makon da ya gabata ya ce, ''al'ummar Igbo ba sa sayar wa wasu ƙabilun filaye''.
Wannan iƙirari ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu suka gaskata, wasu kuma suka ce kalaman nasa na nuna ƙiyayya ne.
Hakan ne ya sa BBC ta fara bincike domin gano gaskiyar iƙirarin na Mista Abati.
A yayin binciken, an tambayi ɗan wata ƙabilar da ya mallaki fili a yankin na kudu maso gabashin ƙasar.
Haka kuma an tambayi wani ɗan kasuwa sannan aka tambayi wani mutum masanin al'adun ƙabilar ta Igbo.
Ina da filaye masu yawa a jihar Enugu - Alhaji Nura

Wani ɗan kasuwa daga yankin Ugwu a jihar Enugu, Alhaji Nura ɗan asalin garin Dutse a jihar Jigawa, da aka fi sani da, Dan masanin Enugu', ya faɗa wa BBC cewa yana da filaye da gidaje da dama a jihar Enugu.
Nura ya ce an haife shi a Enugu kuma yana zaune a can fiye da shekara 60.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da aka tambaye shi hanyar da ya bi wajen sayen waɗannan filaye, sai ya ce ai idan kana da kudi babu abin da ba za ka saya ba.
"Magana ake yi ta kuɗi. Duk wanda yake da su to zai iya sayen fili, duk kuma wanda ba shi da su ba zai iya sayen fili ba''.
"Lokacin da kakana ya zo Enugu, ya sayi fili domin ya gina gida, kafin rasuwarsa sai da ya mallaki gidaje 30''.
"Bayan rasuwarsa ne wasu daga cikin 'ya'yansa suka sayar da gidaje da filayen da suka gada a wajensa, sannan suka koma yankin Ugwu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
"Ina da gidaje da dama a Enugu, ɗaya na kan titin Ogui, akwai wani a kan titin Owerre da kuma wani a layin Ogidi. Amma gidana da ke gaban Awusa shi ne na gada daga kakana."
Nura ya ce ba gaskiya ba ne iƙirarin da ke cewa al'ummar Igbo ba sa sayar da fili ga wata ƙabilar, yana mai cewa maganar mallakar fili ta ta'allaƙa ne kan kuɗi.
"Idan ɗan ƙabilar Igbo ya tashi sayar da gidansa, kuma ina da kuɗi, zai iya sayar mini. Idan zai sayar da gidan kan kuɗi naira miliyan 100, idan ina da su ba abin da zai hana ya sayar min''.
Ya ci gaba da cewa, idan gona ce a ƙauye, hanyar da ake samunta ita ce, bi ta hannun sarakunan gargajiya.
Dillalai na nuna wa masu sayen gida wariya?

Onyebuchi Igboke, wani dillalin gidaje da filaye a jihar Enugu ya faɗa wa BBC cewa ya ji mamakin jin cewa wai ya kai wani mutum ɗan wata ƙabilar domin ya sayi fili, sai aka ce wai ba za a sayar masa ba saboda shi ba ɗan ƙabilar Igbo ba ne.
"Idan kana da wani mutum ba ɗan ƙabilar Igbo ba da ke son sayen fili, ka kawo min su, za su samu''.
"A matsayinmu na dillalai da ke sayar da filaye ga masu buƙatar gina gidaje, ba mu taɓa cewa ba za mu sayar wa kowa ba''.
"Amma akwai al'umomin da ke yin tambayoyi kafin su sayar da fili, domin su san haƙiƙanin mutumin da zai sayi filin nasu''.
"Irin waɗannan mutane kan tambaye mu, "Shin za su sayi filin ne sannan su sayar da shi ga mutanen da za su iya kawo mana fitina?
Igboke ya ce idan akwai wannan fargaba to nan ne masu filaye suke shiga ɗar-ɗar, tare da bayar da umarnin tantance waɗanda za su sayi filayen nasu.
Amma indai ba wannan fargabar aka shiga ba, kowa zai iya sayen fili ba tare da nuna wariya ko bambanci ba.
Me al'adun Igbo suka ce kan sayar da fili

Wani mutum da ya shahara wajen sanin al'adun ƙabilar Igbo, Mista Olueze Ukaejuoha daga ƙauyen Duruagwu na garin Okpurutongi a ƙaramar hukumar Ikeduru a jihar Imo ya ce maganar gaskiya al'adar Igbo ba ta amince da sayar da fili ba.
Olueze ya ce, ''Turawa ne suka kawo ɗabi'ar sayar da fili, al'ummar Igbo ba sa sayar da fili, sai dai su bayar da shi kyauta, ko su yi amfani da shi wajen biyan bashi, ko sayen wani abu''.
Ya ƙara da cewa saboda yadda ya yi kamanceceniya da kuɗi ne ta fuskar ciniki, ya sa ake sayar da shi.
“Al'adar Igbo ba ta amince da sayar da fili ba, duk wanda ya sayar da fili, zai fuskanci matsala, domin ƙasa ba dukiya ba ce da za a sayar''.
"Hakan na nufin rayuwa da soyayyar ƙasa. Abin da kawai ake sayarwa shi ne abin da aka samu. Amma ita ƙasa gadarta ake yi daga magabata''.
A taƙaice, ba a sayar da ƙasa a al'adar Igbo tun shekaru aru-aru, ba tare da la'akari da ƙabilanci ba.
Amma a yanzu, mutane da dama kan sayar da fili domin samun kuɗi, sukan sayar da fili ga kowa ba tare da la'akari da ƙabilanci ba.











