Abin da ya sa wasu kasashen da Faransa ta yi wa mulkin-mallaka ke shiga kungiyar kasashe renon Ingila

Wasu mata matasa

Asalin hoton, Getty Images

A yayin da kasashe biyu da Faransa ta taba yi wa mulkin-mallaka suke shirin shiga kungiyar kasashe renon Ingila, mai sharhi kan harkokin Afirka Paul Melly ya yi nazari kan tasirin shiga kungiyar da ke magana da turancin Ingilishi.

Gabon da Togo sun soma yaukaka dangantakarsu ta difilomasiyya a yayin da suke kokarin rage dogaro kan Faransa.

An shigar da su kungiyar da a baya kasasshe renon Ingila ne kawai suke shiga amma daga bisani aka rika fadada kasashen da za su iya shiga cikinta.

Wadannan kananan kasashen da Faransa ta yi wa mulkin-mallaka yanzu sun zama mambobin kungiyar kasashe renon Ingila na 55 da 56.

Rwanda ta shiga kungiyar a shekarar 2009 yayin da ita kuma Mozambique ta shiga a 1995. Dukkan wadannan kasashe ba su da wata dangataka da Birtaniya a baya.

Matakin da suka dauka na shiga kungiyar kasashe renon Ingila a yanzu na nufin suna kallonta a matsayin mai amfani a fannin difilomasiyya da al'adu, da kuma yin "tasiri" a kasashen duniya.

Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya je Rwanda inda ya kwashe kwana uku a can lokacin taron kungiyar kasashe renon Ingila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya je Rwanda, inda ya kwashe kwana uku a can lokacin taron kungiyar kasashe renon Ingila

Haka kuma ya nuna muhimmancin turancin Ingilishi wajen gudanar da kasuwanci da harkokin kimiyya da siyasar kasashen duniya da kuma hadin kai wajen tallafa wa cigaban tattalin arziki da isar da sakonnin difilomasiyya.

Rwanda ce ta bai wa Gabon da Togo kwarin gwiwar shiga kungiyar: shekara 13 kacal bayan da ta shiga kungiyar, ta samu damar karbar bakuncin taron, wanda shugabannin kasashen duniya suka halarta, ko da yake wasu fitattun shugabanni ba su halarce shi ba, ciki har da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.

Goyon baya daga wurin matasa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gabon da Togo sun shiga kungiyar kasashe renon Ingila ne a yayin da dangantaka tsakanin Afirka da Faransa ta yi tsami.

Ana ci gaba da samun karuwar matasa a birane da ke neman a daina amfani da kudin CFA wanda ake kwatanta shi da euro a karkashin wani tsari da gwamnatin Faransa take bai wa tabbaci. Kazalika jibge dakarun sojin Faransa a yankin Sahel ya jawo ce-ce-ku-ce.

Don haka matakin da Togo da Gabon suka dauka na shiga kungiyar kasashe renon Ingila ya yi matukar farin jini a tsakanin matasa.

Hakan zai taimaka wajen sanyawa a rika yi wa gwamnatocin kasashen biyu kallon wadanda suka dace da zamani kasancewar shekara da shekaru ana yi musu kallon masu ra'ayin rikau a dangantaka tsakanin kasashen Afirka da Faransa.

A baya irin wannan mataki yana iya fusata shugabannin Faransa wadanda ke tsoron raguwar tasirinsu a yankin kudancin Sahara.

Sai dai gwamnatin Faransa ta yanzu ba ta ganin hakan a matsayin wani abin damuwa sosai.

Kuma wannan dalilin na fadada hulda da alaka ta kasa da kasa ne ya zaburar da ita ma kungiyar kasashe renon Faransa wato the Organisation Internationale de la Francophonie (OIF) inda take kokarin fadada.

Marigayi tsohon shugaban Gabon da takwaransa na Faransa, Omar Bongo (Hagu) da Jacques Chirac (Dama)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marigayi tsohon shugaban Gabon da takwaransa na Faransa, Omar Bongo (Hagu) da Jacques Chirac (Dama)

Ta ma yi ikirarin cewa tana da kasashe mambobinta 88 - ciki har da Rwanda, wadda tsohon Ministan Harkokin Wajenta Louis Mushikiwabo shi ne sakatare janar dinta. Hasalima ofisoshinta na Yammaci da Tsakiyar Afirka a kasashen Togo da Gabon suke, kuma ita kanta tana bunkasa.

A watan Maris Ministar Harkokin Wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchwey ta sanar cewa kasarta, kasar da Ingila ta yi mulkin-mallaka kuma take da alaka da kungiyar kasashe renon Faransa, OIF, tun shekarar 2006, za ta kammala zama mamba a kungiyar.

Ghana, wadda ke da kwararan cibiyoyin mulkin dimokuradiyya da tattalin arziki mai yalawa, na daya daga cikin kasashen da cikin kungiyoyin kasashen renon Ingila da Faransa - bisa dalilai na difilomasiyya da kuma na kashin kai.

Akasarin makwabtanta da ke Yammacin Afirka kasashe renon Faransa ne kuma gwamnatin kasar ta dauki matakai daban-daban wajen karfafa gwiwar matasa wajen bunkasa tattalin arziki, da al'adu da siyasa - alal misali, yanzu haka tana da makarantu 50 da ke koyar da harsuna biyu.

Ba za a manta da muhimmancin karamar kungiyar kasashen da ke magana da harshen Portugal (CPLP) ba - akasarin mambobinta a nahiyar Afirka suke.

Kalubale na mulkin dimokuradiyya

Dukkan kungiyoyin uku - ta kasashe da ke magana da harshen Portugal da ta kasashe renon Faransa da kuma ta kasashe renon Ingila - suna fuskantar kalubale kan yadda za su samar da mulki na gari, da dimokuradiyya da 'yancin dan adam - wani batu da Kungiyar Tarayyar Afirka da wasu daga cikin kungiyoyin nahiyar, musamman kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (Ecowas), suke ta fafutikar ganin an kyautata.

Kungiyar kasashe renon Faransa da ta kasashe renon Ingila sun aika da masana domin taimaka mambobinsu wajen inganta tsarin zabukansu, sai dai ba sa tsaurara game da batun zama mambobinsu.

A baya Togo ta yi fama da zanga-zanga domin neman yin garanbawul ga harkokin siyasar kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A baya Togo ta yi fama da zanga-zanga domin neman yin garanbawul ga harkokin siyasar kasar.

Mai mulkin kama-karya Gnassingbé Eyadéma ya shugabanci Togo daga shekarar 1967 zuwa 2005, kuma tuni dansa, Faure Gnassingbé, ya gaje shi.

Shugaban Gabon, Ali Ben Bongo Ondimba, ɗa ne ga Omar Bongo, shugaban kasar daga shekarar 1967 zuwa 2009, wanda ya amince da kiraye-kirayen kafa jam'iyyun siyasa fiye da daya a shekarun 1990 amma ya mayar da hankali wajen ganin jam'iyya mai mulki ta ci gaba da lashe zabe da kuma ganin iyalansa sun yi dumu-dumu a harkokin gwamnati.

Kafin ya zama shugaban kasa, Ali Bongo ya rike mukamin ministan tsaro.

Sanarwar da kungiyar kasashe renon Ingila ta fitar game da shigar Togo da Gabon cikinta ta ce: "Wasu daga cikin sharuddan shiga kungiyar kasashe renon Ingila sun hada da cewa: dole kasar da ke son shiga kungiyar ta jaddada muradunta na kare tsare-tsaren dimokuradiyya, da suka hada da gudanar da sahihin zabe da wakilci na gari a majalisun dokoki."

Amma duk da haka shugaban Rwanda Paul Kagame, wanda ake jinjina wa bisa kawo sauye-sauye a fannin tattalin arziki da walwala, ana kuma zarginsa da yin mulkin kama-karya. Masu sukarsa na cewa ya hana 'yan hamayya sakat.

Mr Kagame ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa tana kare hakkin dan adam, kuma babu wani "dan kasar Rwanda da ke tsare a gidan-yari da aka kai shi ba tare da ya yi laifi ba".

Paul Melly jami'i ne a shirin Africa Programme a Cibiyar Chatham House da ke London.