Yadda ‘yan kasar Ghana suka kalli jana'izar Sarauniya, 'Suna maci, muna rawa'

Asalin hoton, EPA
A jerin wasikun da ake aiko mana daga ‘yan jaridar Afrika, a wannan karon Elizabeth Ohene ta kwatanta yadda aka yi jana’izar Sarauniya Elizabeth ta II da yadda suke yi tasu a kasar Ghana.
Ba mu da wani mutum mai kimar da za mu kwatanta jana’izarsa da ta Sarauniya Elizabeth II, don haka ba zai zama adalci ba a kwatanta yadda aka yi ta Sarauniya da ta wani a Ghana.
Amma tunda muna kiran kanmu a matsayin jagorori a fagen jana’iza ta duniya, ba zai bayar da mamaki ba idan muka kalli yadda aka yi ta Sarauniya cikin shauki.
Babban abin da ya soma bambanta jana’izar da muke yi da wadda aka yi wa Sarauniya shi ne yadda aka binne ta cikin kwanaki 10 da mutuwarta.
A Ghana, daraja da girman mutum su ake la’akari da su domin tantance tsayin kwanakin da za a dauka gabanin a rufe shi. A tunaninmu binne mutumin da ya mutu da wuri rashin girmamawa ne.
Bari na bayar da misali da abin da ya faru a kaina, ni da ‘yan uwana har yanzu ana yi mana wani irin kallo a kauyenmu kan cewa mun binne mahaifiyarmu makonni uku bayan mutuwarta. Ana cin fuskarmu cewa mun binne mahaifiyarmu tamkar wata kaza!
Don haka cike da mamaki wani zai rika tunanin ya za a yi Sarauniya ta mutu ranar 8 ga watan Satumba kuma a binne ta ranar 19 ga watan na Satumba.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai tambaya kan yadda aka yi shiru na wani dogon lokaci lokacin jana’izarta. A nan ana yin bikin jana’iza ne cikin hayaniya - a makabarta da kuma coci.
Da gangan ake daga murya a wajen bikin. Idan kida muka sa to sai mun kure shi. Idan ganga ake bugawa haka ake kure ta.
Muna yin kuka. Muna kuka domin nuna bakin ciki. Ana so mu nuna bakin cikin wanda muka rabu da shi da radadin haka a cikin kukan da za mu rika yi ba kakkautawa.
Kai har hayar kwararrun masu kuka muke yi domin su samar da irin ihun da ya kamata a wajen bikin jana’izar, ta yadda ba za a rika yi wa mutum gorin cewa ba a yi kuka yadda ya kamata ba a wajen jana’izar mahaifiyarsa ba. Abin kunya ne a wajen mutum.
A jana’izar Sarauniya, da hawaye ya zuba a idon wani hakan zai zama abin magana. Mu kuwa da a ce wata daga cikin surukanta ta share hawayen kuka da ya yi lamarin zai ja hankalin jaridu.
Mutane a yayin taron sun ruka neman ahuwa na rashin nuna “damuwa”, wanda hakan na nufin zubar hawaye ko kuma nuna damuwa karara.

Asalin hoton, Getty Images
Kowa da ke wajen yadda aka tsara taron jana’izar ya burge shi.
Sun jeru a layi guda. Tabbas ba wanda zai yi mamaki idan sojoji sun yi hakan tare da shirun da suka yi a dandamalin bikin. Ihun da ake yi a jana’izarmu ya fi tsaruwa a kan tasu.
Abu ne da muka sani ga mutanen Birtaniya cewa suna yin abubuwa a kan lokaci, babu bata lokaci ko kadan.
Akwatin gawar Sarauniya ya bar Fadar Buckingham a daidai karfe 14:22 kamar yadda aka sanar.
Jana’izar da aka yi ta kasar an yi ta ne cikin awa daya. Wannan ya sha bamban da yadda muke yi a Ghana – da mu ne sai ta fi haka tsayi – tun da duka duniya na gani, shi kansa Archbishop na Canterbury an ba shi kasa da minti shida don ya yi addu’a.
Da wannan na gama gano cewa babban bambancin da yake tsakanin jana’izarmu da ta Sarauniya shi ne: su suna yin maci ne mu kuma muna rawa.
Macin da kungiya ke yi dubban mutane kuma su kalla. Macin da ake yi a tsare. Wanda ke bukatar a yi ta gwaji ta yadda wani ba zai yi kuskure ba ko da daga kafa daya ne. Ba za ka iya shiga ba idan ba layinka ba ne.
Rawar wata kungiya ce ke yinta a tsare mutane da dama su kalla. Amma mu kowa zai iya shiga ya taka. A bude ake yin ta don haka akan iya kuskure ciki, sannan muna binta da ihu.
Ina ganin akwai darasin da ya kamata mu dauka a wannan macin domin mu sanya shi cikin jana’izarmu da za mu rika yi nan gaba. Ba ni da tabbas idan mutanen Birtaniya na da wani darasi da za su iya dauka daga namu salon jana’izar.












