'Na ɗauki ciki duk da ƙwayar tsarin iyali da nake sha'

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da Susan Wamaitha ta fara jin rashin lafiya shekara ɗaya da ta wuce, ta zaci matsaloli ne da ƙwayoyin hana ɗaukar ciki suke haifarwa waɗanda ta sha wata ɗaya kafin haka – amma sai aka gano tana ɗauke da ciki har sati takwas.
Matar mai shekara 32 yanzu tana da ‘ya’ya uku. Abin da ba ta sani ba shi ne, an haramta amfani da ƙwayar da ta fara sha a watan Yunin 2021 a Kenya.
Sunan da aka fi sanin ƙwayar da shi a Kenya shi ne “Sofia” amma a China ake yin ta, sannan kuma an rubuta dukkan bayanan da ke jikin kwalin maganin da
Sunan da aka fi sanin ƙwayar da shi a Kenya shi ne “Sofia” amma a China ake yin ta, sannan kuma an rubuta dukkan bayanan da ke jikin kwalin maganin da Chinanci.
Fassarar layin farko na cewa tana ɗauke da “Levonorgestrel Fast Tablets". Ƙwayar “tana daɗewa tana aiki a jikin mutum don hana ɗaukar ciki”, a cewar layi na biyu.
Tun shekara 10 da suka wuce aka hana sayar da ƙwayar a Kenya saboda yawan sinadarin levonorgestrel da take da shi – fiye da ninki 40 na abin da aka yarda a sha ke nan.
Levonorgestrel nau’i ne na magani da ake amfani da shi wajen hana ɗaukar ciki. A cewar ma’aikatar lafiya ta Kenya, an taɓa samun lokacin da aka ɗauki ciki a baya bayan ƙwayar ta gaza yin aiki.
Ciwon kai da tasowar amai
“Ban san an haramta amfani da ita ba. Ƙawayena da yawa na amfani da ita ba tare da wata matsala ba,” kamar yadda Wamaitha ta faɗa wa BBC.
Kamar sauran mata a Kenya, ta fara amfani da ƙwayar ce saboda sauƙin kuɗi da kuma sauƙin amfani saboda ana shan ta ne sau ɗaya a wata.

Asalin hoton, PPB
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mata kan sayi ƙwayar Sofia duk wata – akasarin dillalanta ba sa sayarwa da yawa. Duk ɗaya na kaiwa 300 zuwa 400 na kuɗin Kenya (dala 2.50).
Sauran hanyoyin hana ɗaukar ciki da ake amfani da su a ƙasar sun ƙunshi na’urar da ake sakawa a cikin jiki, wadda ke aiki na wata uku kuma akan ba da ita asibitin gwamnati kan dala biyar. Sauran na’urorin da kan yi aiki na tsawon lokaci na kaiwa har dala tara.
Akan ba da kwaroron-roba kyauta a ofisoshi da banɗaki, amma sukan ƙare, duk da cewa ana iya saya a kantuna.
“Saboda ina fama da ciwon baya sakamakon ragar da aka saka min a ƙofar mahaifa, sai na cire ta na koma amfani da ƙwaya,” a cewar Wamaitha.
Haka nan ta samu ƙwarin gwiwa saboda ƙawayenta da suka ba ta shawarar amfani da ita ba su fuskanci wata matsala ba.
Sai dai kuma tun daga farkon amfani da ita ba ta ji da daɗi ba – duk da cewa tana tunanin sai daga baya jikinta zai saba da ƙwayar.
“Na fara fuskantar ciwon kai da yunƙurin amai. Ban ga jinin al’ada ba a watan farko,” in ji ta. Amma ba ta ji wata damuwa ba saboda ta ga jinin a wata na gaba – har sai da ya sake ƙin zuwa a wata na uku sannan ta fara fargaba.
Daga nan sai mijinta ya fara bincike game da ƙwayar kuma a lokacin ne ya gano cewa an haramta amfani da ita.
“Sai muka shiga firgici game da amfani da haramtacciyar ƙwaya kuma da na fahimci cewa ina da ciki na damu ƙwarai game da abin da za ta iya haifar wa jaririna.”
Yanzu sun haifi ‘yarsu mai wata uku, amma ma’auratan na cke da ɓacin rai game da ƙarancin bayanai kan abin da ka iya shafar ‘yarsu idan ta girma.
Abubuwan da ake ƙyama a shirin tsarin iyali
Kashi 50 cikin 100 ne kawai na matan da ke son amfani da hanyoyin zamani na hana ɗaukar ciki ke samun su a yankin kudu da hamadar Sahara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
A Kenya, ba a fiya magana kan tsarin iyali ba, akasari saboda al'adu da kuma ɗabi'u na addinai.
Wasu mazan ba sa barin matansu su yi amfani da hanyoyin tsarin iyali, yayin da wasu ƙungiyoyin addinin ke adawa da su. Misali, ƙungiyar Kavonokya na adawa da dukkan magungunan zamani saboda ta yi imanin cewa littafi mai tsarki na Bible cewa ya yi a yi addu'a kawai don neman magani.
A wajen ƙwararre kan ci gaban al'umma Dr Josephine Kibaru, zai fi kyau a fara wayar da kan mutane tun daga tushe kafin mutane su karɓi magungunan zamani na tsarin iyali.
"Muna buƙatar ma'aikatan lafiya 'yan sa-kai su samu horo kan tsarin iyali saboda mace za ta fi yarda da maƙocinta ko ƙawarta fiye da ma'aikacin lafiya da za ta gani a asibiti," in ji Dr Kibaru.
Kwastomomin da aka amince da su kawai ake sayarwa
Masana harkokin magani sun san cewa an haramta ta, yayin da a watan da ya gabata ma'aikatar lafiya ta sake fitar da gargaɗi, amma har yanzu ana sayar da ƙwayar saboda buƙatar da mutane ke nunawa.
Ba a nuna ta, amma ana sayarwa a ɓoye ga kwastomomin da aka yarda da su da ke zuwa saya duk wata.
BBC ta kai ziyara shagunan sayar da magani da yawa a Nairobi, babban birnin Kenya don bin diddigin ƙwayar ta Sofia - da yawa kan ce ba a sayar da ita.
Wani mai sayarwa - da ya nemi a sakaya sunansa - ya ce akwai ta amma a ɓoye, kuma masu shaguna na shiga da ita ne daga maƙwabtan ƙasashe.
Hasali ma, a farkon watan nan wani jami'in hukumar kula da magunguna ya faɗa wa jaridar Standard cewa sun kama wani ƙunshin ƙwayar a kan iyakar Uganda. Wamaitha ta ce ta sayo ƙwayar sau uku a wajen wata ƙawarta da ke samowa da yawa a wajen ɗaya daga cikin masu kawowa.
Ta ce ƙawar tata na sane da cewa an haramta ƙwayar lokacin da ta ba ta shawara.











