Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Majalisar Dattawan Liberia ta amince da ƙudurin kafa kotun hukunta laifukan yaƙi
Majalisar dattawan Liberia ta amince da kafa kotun hukunta laifukan yaki da na tattalin arziki da aka dade ana neman a yi a kasar.
Ana ganin hakan a matsayin wani muhimmmina mataki na tabbatar da gaskiya, sama da shekara ashirin bayan an kawo karshen yakin basasa biyu da aka yi a kasar ta yammacin Afirka, da ya yi sanadiyyar hallaka mutum akalla dubu dari biyu da hamsin.
Bayan irin rashin imanin da aka tafka na jikkatawa da kisa da kuma barnatar da dukiya a yakin basasa biyu da aka tafka a kasar ta yammacin Afirka, daman an sha kiran da a kafa wannan kotu da za ta bi diddigin wadanda suka aikata laifi na yaki da kuma na barnatar da dukiyar kasa domin hukunta su don hakan ya zama ya kawo karshen ruwa ta sha ga masu aikata miyagun laifuka ga kasar.
Dan majalisar dattawa daya ne kawai bai sanya hannu na amincewa da kudurin kafa wannan kotu ba, kudurin da damn tun a watan da ya wuce majalisar wakilan kasar ta Liberia ta amince da shi.
Shugabar majalisar dattawan, Nyonblee Karnga-Lawrence ta bayyana matakin a matsayin sanya dan-ba na kawo karshen ta’adar aikata laifi ba tare da mutum ya gamu da hukunci ba, kamar yadda ta rubuta a wani sako ta intanet.
Yanzu dai an mayar da kudurin dokar ga majalisar wakilan kasar domin samun daidaito da shawarwarin ‘yan majalisar kan kudurin yadda zai zama bai-daya.
Da zarar an kammala hada wadannan bambance-bambance kudurin ya zama daya za a mika shi ga shugaban kasar, Joseph Boakai domin ya amince da shi ya zama doka, daga nan sai a kafa kotun.
Idan aka kafa kotun, Liberia a karon farko za ta iya gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata laifukan yaki, a munanan yakin basa biyu da aka tafka a tsakanin shekarar 1989 da kuma 2003.
An yi kiyasin hallaka mutum dubu 250, tare da aikata laifukan da suka hada da fyade da sanya kananan yara aikin soji.
A shekara ta 2009 kwamitin binciken gaskiya da sasanto na kasar ya bayar da shawarar kafa irin wannan kotu ta musamman amma ba a abin da gwamnatocin da suka biyo baya suka yi a kai.
A lokacin rantsar da shi Shugaba Boakai ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta duba yuwuwar kafa kotun, domin hukunta wadanda suka aikata laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil’Adama.
Ana ganin watsi da wannan batu wanda a can baya ya kasance kan gaba cikin abubuwan da yawancin al’ummar kasar ke fatan gani, wato na kafa wannan kotu, da kuma zargin rashawa da almundahana, ya janyo wa tsohon shugaban kasar George Weah faduwa a zaben neman wa’adinsa na biyu a karshen 2023.
A lokacin Mista Weah ya ki wannan batu fur a yayin kamfe, duk kuwa da cewa abin da jama’a da dama ke ta magana ne a kai.
A baya Mista Weah tsohon gwarzon dan kwallon kafa na duniya ya hau shugabancin kasar, da alkawarin samar da ayyuka da inganta rayuwar jama’a da kuma kafa kotu.
To amma bayan da ya dare kan mulki a 2018 sai ya sauya baki, inda ya ce waiwayar abubuwan da suka wuce na yaki ba hanya ce da ta dace wajen samar da cigaba ba, wannan masana da dama suka kalli hakan a matsayin ruguza kansa a siyasa.
Shugaba Joseph Boakai ya kayar da George Weah a zaben raba-gardama da aka yi a watan Nuwamba na 2023 bayan sakamakon zaben da aka yi a watan Oktoba na shekarar ya kasa samar da dan takara daya da ya samu yawan kuri'un da ya kamata ya zama zakara.