Wane ne ya yi nasara kuma wa ya faɗi a harin da Iran ta kai wa Isra'ila?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, By Mahmoud Elnaggar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
"Wata dama ce da ta haskaka Iran". Haka mafi yawan masu sharhi suke bayyana harin da Iran ta kai wa Isra'ila daga cikin ƙasarta.
A daren ranar Asabar ne, Tenhran ta kai hare-hare sama da 300 na jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan Isra'ila, kamar yadda sojojin Isra'ilan suka bayyana.
Sojojin Iran sun ce harin na ramuwar gayya ne kan wanda Isra'ia ta kai wa ofishinta da ke Damascus, kuma ta cimma duka burinta."
A baya Iran ta riƙa barazanar kai mummunan hari na ramuwa saboda harin da Isra'ila ta kai mata na sama ranar 1 ga watan Afrilu a wani gininta da ke Damascus babban birnin Syria.
Harin ya kashe mambobin tawagar juyin juya halin Iran su bakwai, sannan ya kashe wasu 'yan Syria su shida.
Isra'ila ba ta yi iƙirarin kai harin kan ofishin jakadancin Iran ɗin ba, amma kusan kowa ya yi imanin ita ta kitsa harin.

Asalin hoton, Atef Safadi / EPA
Riba da faɗuwa
Iran ta ce nasara ce kai wa Isra'ila garin.
Amma, a cewar wani mai bincike kuma darankata a cibiyar nazari darashin larabcin Iraniyawa Ali Nouri Zadeh, babu wani dalilin harin ramuwar gayyar da Iran ta kai.
Maimakon nasara raunin shugabancin Iran harin ya fito da shi, domin kuwa bai samu inda aka nufa da shi ba cikin Isra'ila.
Wannan wani abin dariya ya zama tsakanin wasu mutane a Iran.
Zaden ya yi amannar cewa da Iran ta ci gaba da yaƙin da ya kira na "sunƙuru", da ta fi samun nasarori.

Asalin hoton, Reuters
A gefe guda kuma, Dr Eric Rundtski, mai bincike kan nazarin Gabas ta Tsakiya a cibiyar Moshe Dayan da ke Jami'ar Tel Aviv, Isra'ila ce ta yi rashin nasara saboda tsoratar da ta yi ta ayyana ƙasar ta zama cikin shirin ko ta kwana. Ya ce hakan ya harzuƙa Isra'ilawa, kuma da yawansu na cikin firgicin za a iya sake kai musu irin waɗan nan hare-hare.
Zadeh ya ce yanzu Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na jin ya ƙara samun karfi. Harin ya taimaka wajen ƙarfafa alƙarsa tsakaninsa da Amurka da kuma wasu ƙasashen Yamma, bayan mummunar sukar da ya fuskanta gabanin harin na ranar Asabar.
Mai binciken ya ce wataƙila a kwai wata ribar da Isra'ila za ta ci a game da harin amma dai ta yi asara ta wasu fuskokin.

Asalin hoton, Getty Images
Komawa teburin sulhu da sauran ƙasashe
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani mai binciken Isra'ila Eric Rundtski ya yi amannar harin ya fi zama nasara ga Isra'ila. Ya ce zai iya zama wani sabon babi na siyasa, saboda yanzu Isra'ila na samun goyon bayan Yamma karon farko cikin watanni.
Yanzu Isra'ila za ta iya komawa kan teburin sulhu da waɗannan ƙasashe, musamman Amurka bayan wata doguwar sa toka sa katsi da ta faru tsakaninsu.
Idan koma bangaren Iran, mai binciken ya yi amannar Tehran ta yi rashin nasara ta fuskar siyasa, a cikin gida da waje. Ya ce Iran ta rasa goyon bayan ƙasshen da ke makwabtaka kuma babu sabon goyon baya daga kowacce kasashe yanzu.
Ya kuma ce akwai yunkuri daga wasu ɓangarori na yunkurin jefa Iran cikin yaƙin kai tsaye da Amurka.
Duka masu binciken sun amince da cewa ƙasashen biyu na da matsalar cikin gida kan wannan sha'ani.
Rundtski ya nuna cewa akwai babbar damuwa a cikin gida a Isra'ila. Ya ce akwai bacin rai ta fuskar siaysa da yake ƙaruwa a lokacin da ake fama da wannan yaƙi, saboda rashin ci gaba da ake fuskanta game da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Zadeh shi kuma ya ce jagoran addini a Iran Ali Khamenei na fuskantar matsin lamba a cikin gida shi ma, ba kawai ga mutanen gari ba, amma tsakanin manyan masu muƙamai na gwamnatinsa.
"Akwai damuwa da ake nunawa daga Dakarun Juyin Juya Hali kan mutum bakwansu da aka kashe wadanda jagorori ne, yanzu haka dakarun suna so a ɗaukar musu fansa.

Asalin hoton, Getty Images
' Sako da wuta'
Wani janar mai ritaya na Lebanon, Hashin Jaber - kwararre wajen dabarun soji kuma darakta a cibiyar nazarin dabaru ta Gabas ta Tsakiya da ke Beirut - ya shaida wa BBC cewa "babu wani abin mamaki game da harin da aka kai".
Ya ce saboda mako biyun da aka yi ana cacar bakin ya kai ga harin da aka kai ta sama, abin da ya jefa Isra'ila cikin fargaba.
Jaber ya bayyana harin na Iran a matsayin "Sako da wuta" domin nuna ƙarfin da take da shi na kai hari har cikin Isra'ila da kuma nuna cewa a shirye take da kare kan da Isra;ila ke ikirarin yi.
Ya ce harin ya taimakawa Iran dawowa da ƙimarta ta fuskar siyasa a yan shekarun nan biyo bayan abin da ya kira "siyasar da bara da nuna hakuri", yayin da kuma take samun nasara ta fuskatsoji da kuma dabaru.
"Idan Isra'ila ta zaɓi ta mayar da ramuwam" in ji Jaber, "Zai iya isa har cikin ƙasar Isra'ila makaman nata masu linzami, amma ba zai wuce haka ba saboda mummunan ramuwar da za a yi tsammani daga Iran."
"Ya ƙara da cewa "jiragen Isra'ila za su iya bambin din Iran ba tare da kuskure ba, amma suna buƙatar bi ta samaniyar wasu ƙasashen larabawa - wadanda Iran ta yi wa gargadi - ko kuma su kai hari daga sansanin Amurka, wanda kuma Amurka ba za ta amince da hakan ba".

Asalin hoton, ABEDIN TAHERKENAREH / EPA
Sauyawar dalila da kuma ƙarfafa kwarin gwiwa
Fawaz Gerges, farfesa ne a sashen nazarin huldar diflomasiyya ta duniya a makarantar nazarin tattalin arziki ta Landan, ya ce Isra;ila ta fi samun riba a wannan harin sama da Iran.
Ya yi bayanin cewa harin Iran bai yi wata barna ba ga Isra'ila, yanzu duka kasashen Yamma suna goyon bayan Isra'ila.
A cewarsa Amurka na gangamin nuna goyon baya ga Isra'ila ta fuskar soji da leken asiri da kuma tattalin arziki.
Gerges ya ce Shugaban Amurka JOe Biden ya nuna an cutar da ƙasar, ta yadda ya yi kiran tattaunawar gaggawa ta mambobin G7 domin nuna goyon bayansu ga Isra'ila: "Netanyahu zai yi nasara ta fukar siyasa bayan raba hankula, ko da na wani ɗan lokaci ne, daga tashin hankalin da aka fuskanta a Gaza zuwa wani saƙo mai sauki,"

Asalin hoton, Amir Cohen / Reuters
'Dabarun rashin nasara ga Isra'ila'
Amma Gerges na ganin akwai faɗuwa ga Isra'ila, yana cewa dabarar faduwa ce, nuna ƙasar a matsayin maras kariya.
Ya ce a siyasance Iran ta yi nasara a idon mutanenta da ƙawayenta da kuma maƙiyanta, ta yadda ta nuna ta shirya tunkarar Isra'ila gaba da gaba.
Ya ƙara da cewa Isra'ila ba za ta iya kare kanta ba ita kaɗai dole sai da taimakon ƙawayenta na Yamma, saboda Amurka da Burataniya da Faransa da kuma Jordan ne suka taru suka kakkabo makaman da Iran ta harba mata.
"Yanzu yankin na ƙan wata irin gaba," in ji Gerges, kuma duka ƙasashen biyu sun ɗauki hanyar ci gaba da fafatawa.
Ya yi gargaɗin cewa yankin na cikin tashin hankali ta fuskar siyasa soji da kuma tattalin arziki.










