Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan majalisar Najeriya na son komawa tsarin mulki na wa'adin shekara shida
Majalisar wakilan Najeriya ta fara muhawara kan wasu kudurori da ke neman komawa ga tsarin yin wa'adin mulki guda na tsawon shekara shida ga shugaban kasa da gwamnoni da kuma shawawar samar da mataimakan shugaban kasa guda biyu daga bangaren arewaci da kudancin kasar
Tuni wadannan kudirorin suka tsallake karatu na daya a Majalisar wakilai, inda ake sa ran za a ci gaba da tafka muhawa har sai an musu karatu uku, kafin aikawa majalisar dattawa ita ma ta yi na ta aikin.
Wasu 'yan majalisar wakilai 35 ne suka taso da batun, inda suke ganin cewa zai taimaka wajen ceto kasar daga halin da take ciki.
Me Yan Majalisar ke cewa?
Wasu daga cikin ƴan majalisar wakilan da ke goyan bayan kudurin irin su Injiniya Sagir Ibrahim Koki daga Kano, ya ce idan aka amince da ƙudurin zai bai wa gwamna ko shugaba ƙasar damar tsayawa ya gudanar da aikinsa cikin tsanaki ba tare da harkokin zabe ko siyasa sun dauke masa hankali ba.
“Hikimar wannan wa’adi na shekara 6 shi ne muna ganin zai bai wa shugaban kasa ko gwamna ya yi abun da ya da ce, wanda kuma mu ba mu hango cewar lokacin ya yi musu kadan ba, a bisa dalilan da muke da su a ƙasa.
A hannu guda kuwa akwai wasu daga cikin ƴan majalisar wakilan da ke adawa da ƙudurin inda suka ce za su kalubalance shi da tabbatar da cewa bai yi nasara ba.
Kabiru Alhassan Rurum na daya daga ckinsu inda ya ce samar da tsarin mulkin na falle daya ba komai zai haifar ba illa ya sa mutum ya yi abin da ya ga dama saboda ba shi da damar da zai koma mutane su sake zabar sa ba.
“ Idan aka ce za ai zango daya ko shugabancin shekara 6, daga nan ka gama, wannan zai sa mutum ya yi abin da ya ga dama saboda bashi da damar da zai koma mutane su sake zabarsa, don haka za mu jira a gabatar da wannan kuduri a gaban majalisa”
“Akwai yan majalisa iri na da yawa da basu gamsu ba kuma ba su yarda da wannan kuduri ba, domin kuduri ne da ya ke rushashshe tun gabanin a gabatar da shi a gaban majalisa, ba zamu amince da shi ba” in ji Rurum
Haka kuma a ɓangaren majalisar dattawan ƙasar kuwa tuni wasu daga cikin su, suka fara bayyana aniyarsu ta goyon bayan wannan kuduri, indai har majalisar wakilan kasar ta mika musu kudurin gabansu, wanda kuma Sanata abdulrahman Kawu Sumaila na cikinsu, ya kuma ce tsarin shekru shidan ya fi kwanciyar hankali.
“Magana ta gaskiya, idan har ya zo majalisar dattawa zan goyi baya wannan kuduri ina ganin ba karamin nasara ba ce za a samu a dimokaradiyar nan domin ba na zaton wannan tsarin na shekara 4 sau biyu na shekara 8 zai kai mu wani waje'' in ji shi
Sauran abubuwan da kudurin ya ƙunsa
Baya ga wa'adin mulki daya na shekara shida kudirin kuma ya kunshi samar da mataimakan shugaban kasa guda biyu daga arewaci da kudanci, akwai kuma Kudurin bukatar neman an gudanar dukkanin zabuka a rana daya tun daga na shugaban kasa da na yan majalisar tarayya da gwamnoni da kuma na yan majalisar jiha.
A daya kudurin kuma na ƙunshe ne da bukatar kammala dukkanin shari'un zabe kafin rantsar da wa'adanda aka zaba.
Za a dai saurari ra'ayoyin jama'ar kasa bayan karatu na biyu, sannan ya kai ga majalisar dattawa idan kudurorin sun yi nasara har ya kai ga amincewar shugaban kasa.