Ziyarar Tinubu da ta turnuƙe Katsina da ƙura

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, BOLA AHMED TINUBU/FACEBOOK

Lokacin karatu: Minti 5

Gwamna Umar Dikko Raɗɗa ya fitar da jawabi a kan ce-ce-ku-cen da ya kaure game da ziyarar kwana biyu ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Katsina, ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da suka fi fama da masifar rikicin 'yan fashin daji.

Ka-ce-na-ce ya ɓarke ne har a shafukan sada zumunta tun lokacin da aka fara ganin wasu manyan allunan da aka kakkafa ɗauke da saƙon 'Katsina Ba Ƙorafi', a yayin ziyarar.

Saƙon 'Katsina Ba Ƙorafi' ga alama ya jefa ɗumbin mutane cikin mamaki, inda suke neman sanin hikimar nuna wa Tinubu cewa jihar ba ta da wani ƙorafi, duk da a zahiri, ba gaskiya ba ne.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Najeriya ta fitar ranar Litinin, na cewa a wata ziyara da ba a saba gani ba, Shugaba Tinubu ya gana da dakarun Shirin Fansan Yamma da suke fagen daga, domin bin diddigin halin tsaro da ake ciki (a Katsina) kuma ya karɓi bayanai kai tsaye na yadda ayyukan dakarun ke tafiya ba tare da rakiyar gawurtacciyar kwamba ta manyan hafsoshin soji ba.

Mutane masu yawa ba kawai a Katsina ba, har ma a arewacin Najeriya na ganin ziyarar wata gagarumar dama ce ta yi wa Tinubu gamsasshen bayani kan matsalolin tsaro da na tattalin arziƙi da suka fi addabar jihar.

Da dama a yanzu na cike da wasu-wasi, gwiwoyi a sanyaye. Suna tunanin ko 'Katsina Ba Ƙorafi' ne ainihin saƙon da kawai manyan 'yan siyasar jihar suka yi ta faɗa wa Tinubu tsawon kwana biyu da ya kwashe a can.

Yayin da wasu ke kallon saƙon a matsayin tumasanci, ba-ni-na-iya da bambaɗancin 'yan siyasa da ke son burge Tinubu, a lokacin da al'ummominsu ke ci gaba da shan azabar tsananin talauci da yunwa da kuma hare-haren 'yan fashin daji.

Allunan da suka janyo ce-ce-ku-ce

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto, Allon 'Katsina Ba Ƙorafi' na ɗauke ne da hotunan Tinubu da Gwamna Raɗɗa da kuma Minista Ahmed Ɗangiwa

A martanin da ya mayar cikin wani saƙon murya da aka yaɗa ranar Talata, Gwamna Umar Raɗɗa ya kama sunayen wasu dattijan jihar da ya ce ya ji saƙonsu na nuna rashin jin daɗi a kan lamarin.

A cewarsa, "maganar billboard da wani ya buga... cewa 'Katsina Ba Ƙorafi' ni a matsayina ma na gwamna, ban ma san an buga shi ba, sai da na gani a soshiyal midiya".

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, BOLA AHMED TINUBU/FACEBOOK

'Cin fuska ne ga Katsinawan da ke fama da hare-hare'

Mutane da yawa sun yi ta bayyana ra'ayoyi mabambanta a shafukan sada zumunta game da batun.

Wani Abdullahi Mansir Gafai ya yi tambaya a shafinsa na Facebook cikin Ingilishi cike da kaɗuwa cewa 'Katsina Ba Ƙorafi?'.

Wane irin cin fuska ne wannan, in ji shi. Wannan wata zolayar ɗiban albarka ce ga mutanen da ke kwarma ihu a sarari da kuma masu yi a zuci yayin da suke dulmiya cikin tsoro da yunwa ga kuma ƙaƙa-ni-ka-yin rayuwa.

"Kowa ya sani, ban da masifar hare-haren 'yan fashin daji, Katsina na ɗaya daga cikin jihohi mafi talauci a Najeriya."

Ya ƙara da cewa: "Yayin da Shugaba Tinubu ke sharɓar liyafar ƙasaita a Katsina rahotannin 'yan fashi sun auka wa garuruwa a Faskari da Bakori da Dutsin Ma da Ƙanƙara da Ɗan Musa, tuni sun cika gari.

"Wani zai cika da murna kan irin wannan dama wadda ba a cika samu ba, da ta faɗo wa Gwamna Raɗɗa ta ya zayyana 'ƙorafe-ƙorafen' al'ummarsa, amma maimakon haka sai ya zaɓi nuna ƙwambo da wadaƙa.

Daya daga cikin allunan da suka janye ce-ce-ku-ce

Asalin hoton, FACEBOOK

Shi ma wani ɗan Katsina mai suna MT Maƙera Baban Islam - ya wallafa a Facebook ranar Litinin - wani bidiyo da ke nuna ƙananan motoci, wasu ma ɗauke da laftun kaya ajiye a gefe da gefen wani titi, ga matafiya nan sun fito sun yi cirko-cirko cike da zulumi. Abin da ga alama yake nuna 'yan fashin daji sun tare hanya, inda ya ce:

"Da sanyin safiyar nan da idanuna na ga mutane (talakawa) suna ta gudun hijira, wasu ma ko kunu ba su samu damar sha ba...

"Da idona na ga ƙauyukan da sun zama kufai. Da idona na ga yadda hankulan ɗaliban FUDMA suka tashi. Ga tsananin talauci ga tsadar rayuwa ga rashin abin yi a tsakanin al'umma...."

Yayin da Aliyu Kankia Abubakar ya rubuta cewa: "Maganar 'Katsina Ba Ƙorafi' abin ya ɓata ma al'ummar jihar Katsina da sauran 'yan arewa rai... ya tada ƙura.

"Har a mumbarin malaman addini ana tattauna wannan maganar, har addu'o'i ana ta yi kan maganar."

A facebook post

Asalin hoton, facebook

Bayanan hoto, Mutane da dama kuma na danganta allon 'Katsina Ba Ƙorafi' da 'yan siyasan da ke cikin gwamnatin Tinubu

Nasir Dabo kuwa wallafa wani bidiyo ya yi, wanda a ciki ana iya ganin wasu ƙananan yara cikin wata siririyar kwata a gefen wani layi, sun shiga sun tsugunna suna tarar ruwan famfo a kofuna suna zubawa a robobinsu, ga alama daga wani fayaf da ya fashe.

Wata murya da aka ji cikin bidiyon ta yi iƙirarin cewa lamarin na faruwa ne a garin Funtua cikin jihar Katsina.

Haka zalika, wani mai suna Kabiru Garba ya wallafa cewa: "Amma fa wannan wulaƙanci ne na ƙarshe wallahi.

"Da a ce Jagaban (Shugaba Tinubu) yana jin Hausa, kuma ya ga wannan shirmen to tabbas sai ya ce mu wawaye ne ko da a ransa ne."

Za a kai mu a baro - Dattijan Katsina

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ita dai muryar dattijan da aka ce saboda tsokacinta ne Gwamna Raɗɗa ya mai da martani ta zargi dattijan Katsina da zuba ido kawai, ba tare da yunƙurin taka wa Dikko Raɗɗa burki ba.

Ɗaya daga cikin muryoyin ta nuna takaici kan yadda dattijan suka gaza haɗuwa su fito da matsalolin al'ummar jihar, don tunkarar Tinubu su yi masa jawabi.

"Mutane manya su sadu da shi, su yi masa magana. Ai zai je wajen sarki ko, sarki ma ya yi mishi magana.

"Ya ga cewa duk inda ya isa, ya ga gwamna ya yi mishi magana, elders (dattijai) sun mishi magana, dole ya samu abin da zai yi".

Ya ƙara da cewa: "Mu akwai abin da yake damun mu irin.... rashin tsaro (insecurity) da talauci mai kassara al'umma (crippling poverty)?"

Ya kuma ce kamata ya yi su iya ƙarfin hali da nuna dattakon da za su tunkari haƙiƙanin matsalolinsu na rayuwa.

Ɗaya muryar ta zargi Gwamna Raɗɗa da "sakarcin" shaida wa Tinubu cewa Katsina ba ta da ƙorafi, inda ya ce kamata ya yi dattijan jihar su kira taron manema labarai domin nisanta kansu da wannan iƙirari.

Ya ce da sun yi haka, gwamnan zai san idanun mutane na kansa, kuma zai shiga taitayinsa.

"Maganar gaskiya, wannan abin damuwa ne. In ba mu tashi ba tsaye, wallahi Katsina za a kai mu a baro mu".

Governor Radda

Asalin hoton, Dr Dikko Umar Radda/Facebook

Bayanan hoto, Gwamna Raɗɗa dai ya ce ba gaskiya ba ne zargin cewar: 'Katsina Ba Ƙorafi' daga gare shi ne

Gwamna Raɗɗa ya ce babu hannunsa a allon 'Katsina Ba Ƙorafi', hasali ma ya ce a shafukan sada zumunta shi ma ya gani.

Umar Dikko Raɗɗa ya kuma ce gwamnatinsa ta yi wa Tinubu ƙorafi kan matsalolin al'ummar jihar guda uku da suka tantance.

Ya ce cikin batutuwan da ya gabatar wa Tinubu har da matsalar tsaro da ke addabar al'ummarsa. Kuma ya ce ya gabatar da ƙorafi a kan aikin samar da lantarki daga iska na garin Rimi wanda aka yi watsi da shi tsawon shekaru.

Gwamnan ya kuma shawarci dattawan da su riƙa tantance sahihancin duk wani bayani kafin su yi tsokaci a kai.