Jirgin da ya ɗauki gawar Sarauniya ya zama wanda aka fi bin diddiginsa a tarihi

.

Asalin hoton, Reuters

Shafin manhajar bin diddigin jiragen sama ta Flightradar24, ya ce jirgin da ya dauki gawar Sarauniya Elizabeth zuwa Landan, ya kasance jirgin da aka fi bin diddiginsa a tarihi.

Kusan mutum miliyan shida ne suka yi kokarin bin diddigin tafiyar jirgin daga Edinburgh zuwa RAF Northolt a ƙasa da minti daya da tashinsa, in ji shafin.

Yawan mutanen da suka bibiyi jirgin, ya sa an samu matsalolin da suka jawo manhajar ta cushe har ta daina aiki.

Sama da mutum miliyan 4.9 ne suka kalli tashin jirgin a shafi da kuma manhajar na Flightradar24, inda 296,000 kuma suka kalla ta shafin Youtube.

Jirgin da aka fi bibiya kafin yanzu, ya kasance jirgi ne wanda ya dauki ‘yar siyasar kasar Amurka Nancy Pelosi zuwa Taiwan a watan da ya gabata, inda mutum miliyan 2.2 suka bi diddigin jirgin a shafin na Flightradar24.

An dauki gawar Sarauniyar cikin jirgin RAF Globemaster C-17, bayan ajiye ta a Majami’ar St Giles da ke Edinburgh.

Jirgin ya yi amfani da wata alama da ake amfani da ita ga dukkan jiragen soji, wajen daukar gawar Sarauniya Elizabeth.

Gimbiya Anne da mijinta Sir Timothy Laurence ne suka yi wa gawar rakiya, inda Gimbiyar ta ce dama ce ta ganin cewa ta kasance da mahaifiyarta a lokacin ƙarshe na rayuwarta.

"Babbar dama ce ta kasancewa da gawarta daidai lokacin da ake shirin yi mata jana’iza," in ji Anne.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Firaiminista Liz Truss da sakataren tsaro, Bem Wallace na cikin wadanda suka jira isowar gawar a RAF Northolt, inda ta isa birnin Landan kafin 7:00 a yamma.

Shafin Flightradar24, ya ce, ya dauki matakan ƙara inganta shafin ta yadda za a iya bibiyar jirgi ba tare da matsala ba.

Abin da ya janyo aka bibiyi jirgin Ms Pelosi, kakakin majalisar wakilai ta Amurka a watan Agusta, shi ne saboda ita ce daya daga cikin manyan ‘yan siyasar Amurka da ta kai ziyara yankin Taiwan bayan shekara 25, wacce China ke gani a matsayin wani bangare nata.

Da yake bayyana yadda aka samu matsala a shafin a ranar Talata saboda dumbin mutanen da suka bibiyi jirgin da ya dauki Sarauniyar, shafin Flightradar24, ya ce ‘duba da abin da muka gani a watan da ya gabata, mun sa rai cewa za a samu dumbin mutane da za su ziyarci shafin, said ai, bamu yi sammanin ganin mutane da yawa ba irin na jiya.’’

Shafin ya ce mutum sama da 600,000 ne suka samu damar bin diddigin jirgin kafin a dan samu matsala da shafin.

"Duk da cewa dumbin mutane sun hau shafinmu a jiya, jirgin da ya dauki gawar Sarauniya Elizabeth na II daga Edinburgh zuwa RAF Northolt, ya kasance jirgin da aka fi bin digginsa a tarihi a shafin na Flightradar24, kuma zai kasance a sama har na tsawon lokaci,’’ a cewar shafin.