…Daga Bakin Mai Ita tare da Uzee Usman
Daga Bakin Mai Ita, wani shiri ne na BBC Hausa, da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan mako, muna kawo muku hira da Uzee Usman Adeyemi, wanda aka fi sani da suna Uzee Usman, jarumi a fina-finan Kannywood da Nollywood.
An haifi tauraron fina-finan ne a Kaduna, ya yi digirinsa na farko a Jami'ar Abuja a fannin kimiyyar siyasa kafin ya koma ya karanta Ingilishi a Jami'ar Jos.
Ɗaya daga cikin fina-finansa da suka fi tashe a Kannywood shi ne 'Muqabala'.
Ya ce ya fito a wani fim da ke tashe a Najeriya mai suna 'A Tribe Called Judah' wanda rahotanni ke cewa zuwa yanzu shi ne mafi kawo kuɗi a tarihin fina-finan Najeriya.








